Sashe 42
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai ya saka hannu a cikin aljihun shi a hanzarce ya dunƙulo sabbin ƴan dubu-dubu ya miƙa ma Yaseer.
Kallon yawan kuɗin yayi yana girgiza kai da hannu alamun ba zai karɓa ba.
Ƙwaƙwalwar shi ta tuna mishi skekaru tara baya, idanun shi ya hasko mishi mahaifin shi ya durƙushe baya a gaban shi lokacin suna tare da Alhaji Salisu mahaifin Jamal a lokacin da shi kuma yake shirin shiga Jss1, Ranar da aka haifi ita sarauniyar tashi.
Yana kallo ya ƙirgo kuɗi a aljihun shi wanda bai taka kara ya karya ba ya miƙa ma mahaifin shi amma bai kai ga karɓa ba Alhaji Salisu ya amshe ya mayar cikin nashi aljihun.
Sai murmushin takaici ya suɓuce mishi "Allah ka barshi Alhaji" yace cikin sautin dariya-dariya.
Tunanin kunya da fulako yake yi don haka Alhaji Tahir ya mayar da kuɗin yana faɗin "toh ba haka za'a yi ba" sai ya ciro katin shi ya miƙa masa.
"Gashi, kayi min text ɗin account number ɗin ka"
Sa hannu yayi ya karɓa, sannan Alhaji Tahir ya durƙusa ya sumbaci goshin Reina ya miƙa mata farin envelope ɗin hannun shi.
Da sauri ta buɗe don ganin menene, ta ciro bundle ɗin 500 guda huɗu ta dube shi da alamun tambaya.
"Ban ce kuma ki koyi kashe kuɗi haka kawai ba. Ki bawa umman Jamal ta ajiye idan buƙatar wani abu ya tashi sai ayi amfani da shi, Idan kuma wani abun kike so a siyo miki kawai ki faɗa ma driver zai siyo ya kawo miki"
"Daddy har da su cake ɗin toh?"
"Komai ma idan kina buƙata kiyi magana kawai."
"Toh yaushe Aunty zata dawo?"
Ƙaramin murmushi yayi ya shafa fuskar ta "zata dawo soon idan kina karatu"
Ta gyaɗa kai cike da jin daɗi "thank you Daddy, zanyi da yawa kaji?sai ta dawo da wuri"
Ya lura yanzu ta rage tsalle-tsalle da garaje, girma ya fara kama Reina.
Ya so ta raka shi mota amma kaman tana tsoron hakan sai ya ɗaga mata hannu kawai itama ta ɗaga mishi, suna kallo har driver ɗin shi yaja suka bar gidan ba tare da ya shiga ciki ba.
......
Har kwana biyu Yaseer bai nemi Alhaji Tahir ba, hasali ma katin da ya bashi neman wuri yayi ya ajiye bai sake bi ta kan shi ba ya ci gaba da hidiman gaban shi. Ga shi yau sakamakon zagayen ƙarshe na aji biyu zai fito su fara shirye-shiryen registration ɗin fara aji 3, kuma dake bai so zama haka nan ba a sauran ranakun mako yana zuwa haddan su koyarwa shima ya ɗauki karatu don haka yanzu basu biyan shi.
Sakamakon shi na bana yayi kyau sosai, har Jama'are Saudat ta tura shi yaje ya gwada ma su goggo in yaso bayan kwana biyu sai ya dawo.
Ranan Juma'a da hantsi ya sauƙa a tasha, mamaki ya kusan daskarar da shi ganin Meesha a tasha wai tazo ɗaukan shi.
Itama bata wuce kwana biyu da dawowa ƙasar ba baki ɗaya wai sun je graduation ɗin Uncle ɗin su da ya kammala karatun likitanci daga nan suka wuce yawon buɗe ido.
Tana yawan damun shi da kira don haka ya san da dawowar ta a cikin satin nan sai kuma yau da ya sanar da ita shima zai dawo cikin gari shine fa dake hankali bai isheta ba ta tattaro mota tazo.
Haɗe gabas da yamma yayi kafin ya ƙarasa wurin ta, ta karɓi jakar shi tana mishi sannu da dawowa da murmushi a kan fuskar ta gashi hutu ya karɓe ta sosai ta ƙara haske da kyau.
Saboda kar ya disga ta ga idanun jama'a a kanta ganin haɗuwar motar da tazo da shi da itama kanta ya saka kawai ya shiga ta ja suka ɗau hanya. Amma a hanya tasha faɗa saida ta kusan zubda hawaye, har dai suka isa bakin layin su Lafiya.
Yau ma yana fitowa suka yi ido huɗu da Saudat ta fito da shirin zuwa kasuwa don ta ɗauka sai can maraice kafin ya dawo.
"Umma"
Ya kira ta cikin rasa abin cewa.
Sai Meesha ma tayi saurin fitowa daga motar ta durƙusa har ƙasa a kunyace ta gaida ta.
Babu yabo babu fallasa saudat ta amsa sannan ta gayyace su duka biyu su ƙarasa gida domin tana buƙatar sanin wacece yarinyar da har take sauƙe ɗanta a mota bata sani ba.
Yanzu ƙofa ne mai kyau a jikin gidan su Yaseer, kuma gidan ya sha kwaskwarima sosai an lailaye ko ina da siminti ga fenti, sai kuma shuke-shuken su da ya daɗa ƙawata wuri amma sai tausayin Yaseer ya lulluɓe Meesha ganin irin gidan da yake rayuwa.
Ya shimfiɗa mata darduma ta zauna sannan ya kawo mata ruwa, sauran ƙannen shi duk sun tafi makaranta.
"Baiwar Allah daga ina?" Umma ta tambaya cikin taushin murya
"Ita ce ƴar yayan umman Jamal da nake faɗa miki, wanda ta nima min lesson teaching ɗin nan??" Yaseer ya amsa da rawar jiki.
Saudat ta haɗe fuska "kai na tambaya ne?!"
"A'a kiyi haƙuri" daga nan ya gimtse bakin shi.
Sai yau Meesha ta tabbatar ita ɗin cikakkiyar bafulatana ce domin kunyar Saudat ya kama ta sosai da ƙyar ta iya buɗe bakin ta tayi magana, ita da ta ɗauka zasu fara wasan suruka tun yanzu.
Bata wani daɗe ba tayi musu sallama, Saudat ta saka shi yayi mata rakiya zuwa mota, ƴan unguwa sai leƙowa suke yi suna hangen su ta katanga yara kuma suka yi cincirindo har jikin motar suna shafawa.
Sai da ta ɗan yi musu rabo kafin ta samu suka barta ta tafi, Yaseer kuwa kaman ya rufe su da duka, tsaki yaja yana faɗin "matsalar ƴan ghetto Area kenan wallahi, baka isa ka kankaro aji ba sai sun kwaɓar maka"
Da fargaba ya koma gida, kaman yanda yayi tsammani faɗan da yayi ma Meesha ɗazu saida Saudat ta ninka masa shi da ƙyar ya samu ya rarrashe ta don ma ta riga da ta san me yake tsakanin su ne. Sai ta rufe da mishi da nasiha da tuna mishi matsayin shi kaman ko yaushe, kada yaje ya jajiɓo musu abinda yafi ƙarfin su.
Washegari sai gata a gidan Hajiya Hauwa wai tazo bashi haƙuri, tun daga nan ya fahimci Meesha ta zamo mishi jarabawa.
A daren Lahadi yana cikin lissafin komawar shi makaranta sai ga alert ɗin Naira dubu ɗari biyu.
Bai sha wani mamaki ba ganin sunan account ɗin da ya turo Tahir Kamal.
Yaseer ya murmusa, shi da ya matsu ai gashi ya nimo account number ɗin sannan ma da personal account ɗin shi ya turo masa, lallai Alhaji Tahir da gaske yake.
Yanzu yana da har dubu ɗari uku da ɗoriya na kan shi, kuma nan da sati biyu za'a sake biyan shi kuɗin lesson ɗin Jamal.
Daman kuɗin makaranta yayi niyyan biya da dubu ɗarin farko, sai ya jinginar da komawa makarantar har sai an biya shi na biyu kafin yayi siyayya ya biya kuɗin hostel ya tafi. Amma a yanzu ya canza ra'ayi.
POS yaje ya ciro dubu ɗari da Saba'in, yana dawowa ya damƙa dubu hamsin-hamsin ma iyayen shi su biya bashin da ake bin su. Sannan sauran dubu saba'in ɗin yace ayi mishi siyayyan komawa makaranta da shi da ƙannen sa, ayi musu sababbin uniform, jaka da litattafai da sandals, idan yayi canji a ƙara cefane. kuma ya sanar ma Kamal kuɗin makaranta ma shi zai biya kayan shi.
Kowa ya zubda ƙolla wannan daren, har Saudat sai da ta sharara ma su Alhaji Tahir albarka. Babu daɗewa kuma ya sake fita ya dawo da gasassun kaji da yoghurt suka yi kwanan ƙoshi da jin daɗi tare da alfahari.
A washegarin bayan sun gama registration suka wuce kasuwa ya zaɓi yadi kala uku masu kyau Muhammad ma ya zaɓi ɗaya ya bawa tailor a ɗinka musu sannan ya siya sabbon takalmi da turare, bai dawo gida ba dai har saida kuɗin nan ya ƙare katt.
......
TV ne ke ɓaɓatu a parlourn dake a tattare yana fitar da ƙamshin turaren wutar da aka gama ƙonawa.
Tana kwance a ɓarin ta na dama hannun ta ɗaya a kan tumbin ta da ya fara fitowa, ɗayan kuma a kan wayar da take ta rubuta saƙo tana gogewa.
Mai zata ce ma Tahir ne ya kula ta? Wani irin fushi yayi haka da har yanzu ya gagara hucewa? Bata da burin da ya wuce yanzu ta koma ɗakin ta Saboda ba zata so ta haihu a gidan su ba.
Tambaya ta rubuta a kan lafiyar Maama da Reina da kuma ban haƙuri a tare da shi, tana nazari a kan yiwuwar amsawar shi tunda ta saba tura masa irin wannan saƙonnin.
Sai kuma wani tunani yazo mata ta goge ta rubuta wani saƙon kamar haka.
"T ina kwana, yaya Jikin Reina? Tana zuwa makaranta? Tana yin assignment ɗin ta a kan lokaci? Islamiyya fah? Don Allah a kula ana bata abinci saboda idan ta ƙoshi tana rage yame-yamen nan. Sannan idan maghriba tayi don Allah a rufe mata kai a zaunar da ita a ɗaki tayi addu'a. Tana kuma Sallan asuba a kan lokaci, banda fashin la'asar. Kada ta manta da addu'ar fita daga gida idan zata je makaranta"
Hannun ta na ƙaiƙayin tayi magana a kan Maama dai tayi jihadi ta tura, amma ji take yi kaman nan da wani lokaci zata iya mutuwa idan bata saka ta a ido ba.
Ko minti biyar saƙon bai yi da tafiya ba sai ga kiran shi ya shigo wayar ta, Ai zumɓur ta miƙe zaune ƙirjin ta na bugu kaman zuciyar ta zai faɗo daga kirjin ta.
*Saliha Ahmad Na'ibi (seemahwrites ✨)*
*REINA 💍*
30......Hello T?" Ta sake magana jin ta yi sallama babu amsa.
Furzar da numfashi yayi kafin ya amsa da "kina lafiya?"
Baki na rawa tace "da ƙyar nayi lafiya T, kaman ba zan rayu ba..." sai ta fashe da kuka.