Sashe 50
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daddagewa yayi ya miƙe tsaye cikin dauriya ya ƙarasa gaban gadon ya riƙe bed sheet ɗin zai ja ya yaye, sai kuma ya kasa, kukan dake danne a ƙirjin shi yana dambe da bugun zuciyar shi don shima ya samu ya fito a saurare shi, amma ya ƙara jurewa yayi nasarar buɗewar sai ga fuskar Fauziyyar shi, matar aljanna.
Wani nishi yayi mai gunji kafin kukan ya biyo bayan shi, zuciyar shi yana maimaita innalillahi wa inna ilaihiraji'un amma bakin shi ya gagara nanatawa, sai kawai ya rungume gawar da ta sake tayi sanyi babu ɗumin rai a jikin ta.
Kan kace mene wuri ya koma ƙaramin makoki, babu ma wanda ya tuna da wani gawar jariri, har su Hajiya Hauwa sai da suka zubda ƙwalla. amma mutuwar da suka gani yanzu a gaban idon su bai saka sun ji tsoron zuwanta ta ɗauke su a duk lokacin da taga dama duk ikon su da dukiyar su ba. Basu ji kaman su canza ra'ayi ba, ko dan goben yaran su idan basa nan.
.......
Tun da Saudat ta haifo Yaseer duniya bai taɓa kwanan tashin hankali ba irin na yau, ga azaban raunukan dake jikin shi, ga tsamin da jikin shi yake masa, ga baƙar yunwa domin rabon shi da abinci tun karyawar safiyar jiya, ga kuma sauro kaman zasu yanki naman jikin shi, ƙuda ma ba'a bar su a baya ba wajen bidirin su a kan romon daɗin da suke samu.
Yayi tunanin yana da taurin zuciya amma sai ya samu kan shi yana kuka da roƙon su taimake shi ko iyayen shi su kira mishi ko su bashi ruwa ya sha.
Amma gargaɗi ma suke mishi idan bai rufe musu baki ba zasu ƙara mishi gajiya a kan wanda yake fama da ita.
~~~~~~~~~~
Cikin izinin Ubangiji mun kusa kammala littafi na ɗaya.
*Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites ✨)*
*REINA 💍*
36......da farar asuba Kamal suka iso, Saudat dake zaune saman darduma tana zikirin safiya tayi saurin miƙewa a kiɗime ganin suna tafe har da goggo halime tabbas wani mummunan abu ne ya samu Yaseer.
A maimakon ta amsa sallamar su sai cewa tayi "Allah yasa ba mutuwa yayi ba" ƙoƙari take ta sanya ma kanta dangana koma menene ya faru ta ɗau na annabawa, duk da haka burin ta bai wuce su ce mata A'a abinda take tunani ba haka bane.
"Kinga kwantar da hankalin ki, yana raye kuma zai kasance cikin aminci da izinin Ubangiji, yanzu bari mu samu muyi sallah sai muje mu duba shi ko?!". Goggo ta faɗi yayin da take ƙarasowa ciki, sai gaban Saudat ya ƙara tsinkewa.
"Goggo hatsari yayi?" Daga jin muryar ta zaka san a shirye take ta fara kuka, tausayin ta ya hana goggo cewa komai.
Kamal ya umarci Suhail da ya kawo masa ruwan alwala sannan ya tsuguna ya fara duk suka bar ta tsaye da gudun zuciya, gashi Kamal yaƙi yarda ko haɗa ido suyi.
"Hatsari ne ko?" Ta sake tambaya da muryar da tafi na farko rauni.
"A'a ba hatsari yayi ba. Yana hannun folisawa aka ce amma komai lafiya, ki kwantar da hankalin ki" Kamal ya amsa ta.
Ta kwantar da hankalin ta? Tun da suka maimaita har sau biyu dole abinda zata gani ya ɗaga mata hankali.
Don haka a sukwane ta jira suka idar da Sallah lokacin gari ya fara haske.
bata basu damar addu'a ba tace "toh bari na je na tsare mana napep"
"A'a Saudatu, yayi wuri da yawa ba za'a samu abin hawa yanzu ba, sannan Yaseer ɗin zai buƙaci abin karyawa, ki haɗa sai mu tafi masa da shi"
Ta amsa goggo da "toh" Cike da jin daɗin cewa zai iya cin abinci ta miƙe ta shiga kitchen. Akwai ajiyayyen tuwon da tayi niyyar ɗumama musu da safiyar amma sai ta kwaɓa mishi ɗanwake na musamman ganin tana da sauran flour.
Sai da ta gama ɗanwaken ta zuba a food flask ɗin shi kafin ta ɗaura musu ɗumamen tuwon.
haka dai kowa ya taɓa sama-sama, duk yanda yaran suka so bin su goggo ta hana don ko su basu san me zasu je su ji a kan dalilin rufe Yaseer ɗin ba.
Tun daren jiya Kamal ya tambayi masu gadin gidan station ɗin da aka rufe Yaseer, don haka kai tsaye can suka nufa ba tare da sun tuntuɓi Alhaji Tahir ɗin da ya saka aka rufe shi ba.
.....
Kaman jiya ne Alhaji Tahir ya ziyarci Alhaji Abdou a lokacin da ya rasa Malika, shima yau gashi ya ziyarce shi a dalili makamancin sa.
Ya ɗauka Alhaji Abdou ya kiɗime a lokacin da ya rasa uwar Aicha, amma shi kuka yake da hawayen shi a rashin majinginar zuciyar shi, ba ta Reina ko Maama yake ba.
Sosai ya bawa Alhaji Abdou tausayi, rashi har guda biyu a lokacin ɗaya ba wasa ba.
Amma ana buƙatar yayi ma Fauziyya gata ya sallace ta ya kai ta makwancin ta.
"Da ace na samu damar tunkarar ta a kan abinda ya sami Hafsatu, da ba zan taɓa yafewa kai na ba" zaune yake a dandamalin ƙasa hannun shi riƙe da kai, yana ji kaman ya ajiye shi ya huta da tunanukan da ƙwaƙwalwar shi yake faman kawo mishi.
Ya zalinci Fauziyya, ya ɓata mata, ya shiga hakkin ta, amma bai samu damar roƙonta ta yafe mishi ba, gashi ta tafi lokaci ɗaya babu notice. yana tsoron Allah ya ɗaga su a ranar alƙiyama tana ƙullace da shi.
"Allah ya gafarta mata, ya yafe mana baki ɗaya. Amma sai ka jure Tahir, na sani akwai zafi, akwai ciwo amma bata buƙatar komai a halin yanzu bayan ka sada ta da gidan ta na gaskiya sannan ka bita da addu'a"
"Fauziyya na yafe miki, Allah ya yafe miki, Allah ya haɗa fuskokin mu a gidan aljannah."
"Ameen, In sha Allah "
.....
Bayan dogon roƙo da suka yi, da bayanin da aka musu wanda ya ɗaure musu kai, da ƙyar suka samu aka basu daman ganin Yaseer. domin sai da suka ga alamun Saudat tana niman sume musu a wurin.
Da ƙyar yake iya takawa don ji yake yi kaman sunyi mishi targaɗe a ƙafa, yana tafe suna angiza ƙeyar shi har idanun shi da suka kumbure suka shiga na iyayen shi da kakar shi, kamannin fuskar shi ya sauya baki ɗaya.
Kukan da Saudat ta riƙo kayan ta tun daga gida sai yanzu ta samu damar sake shi ganin yanda ɗan nata ya dawo a wuni ɗaya kawai.
Shi kuwa Yaseer ganin hawaye a idanun mahaifiyar shi ya tsotse nashi baki ɗaya, babban baƙin cikin shi a duniya shine ya zamo silar kukan iyayen shi.
Kuka take yi tana sheshsheƙa har sai da numfashin ta ya fara sama-sama, dama Kamal a shirye yake ya shiga shaƙa mata inhaler daman ya san hakan zai faru.
Yaseer da tsayuwa ya gagare shi saboda tsananin yunwa ya tsuguna a gaban Saudat ya riƙo ƙafar ta, amma sai tayi saurin kwacewa tana maida numfashi.
"Ka ji tsoron Allah Yaseer, hukuncin duniya kenan ina ga wanda Ubangiji zai yi maka mai tabbatuwa a ranar da muma ta kanmu muke yi? Idan ka ƙaryata zan yarda da kai amma ka sani ka ci amana ta irin cin amanar da ba'a taɓa min irin shi ba, kuma ba zan taɓa yafe maka ba. ko da ban sani ba Allah ya sani Yaseer, ko dan ban gani ba Allah ya gani, ko da ban ji ba Allah ya ji, kuma bayi barin hakkin wani a kan wani komin kashin sa. Kayi ma kan ka gata ka faɗi gaskiya, mai ita bayi taɓa taɓewa, zata wahalar da kai amma na ƙanƙanin lokaci ne, sai dai idan ka zaɓi kayi ƙarya wahala ta har abada ya tabbata a kan ka." Kalaman ta ke harɗewa don haka ta tsaya ta ja dogon numfashi ta fesar da shi kafin ta ɗaura da.
"Ba don ni ba, sai don wanda ya isa da kai da zuciyar ka, mai hukunta wanda yayi zalunci kuma gatan wanda aka zalunta..... Yaseer ka taɓa musu ƴa? Kana da laifi a kan abinda ake zargin ka da shi??"
Baki ɗaya bakin sa a fashe yake, don haka zafin tauna laɓɓan shi da yayi ya ratsa har cikin ƙwaƙwalwar shi.
"Wallahi Umma, na rantse miki da sarkin da babu wani bayan shi, na rantse miki da wanda tsaron rai na da lafiya ta yake hannun shi, Wallahi Wallahi ban yi ma Hafsatu komai ba, ban taɓa yunƙurin ketare iyakokin da Ubangiji ya gindaya min a kan cikakkiyar mace ba ma balle yarinyar shekara tara Umma. Hafsatu ƙanwata ce, na ɗauke ta yanda na ɗauki su Sabir da Irfan, ƙoƙari na a kullum shine in kare su daga cutarwa, ta yaya za'ayi ni kuma da hannu na in cutar da su?"
Bata bari ya sauƙe numfashi ba tace "Na yarda da kai. Idan ka yi min ƙarya ka cuci kanka Yaseer."
Ɗagowa yayi ya kalle ta cikin ido, tabbas ya gani, yardar da tayi da shi ɗari bisa ɗari don haka ya dubi mahaifinsa shima hakan ne, haka ma kakar shi, don haka zuciyar shi yayi mishi sanyi.
"Umma" ya kira Saudat.
"Na'am Yaseer" tayi ƙoƙarin saka murmushi a kan fuskar ta duk da hawaye bai daina mata zuba ba.
"Umma yunwa nake ji, amma ba zan iya saka komai a ciki na kina min kuka ba. Ina tsoron azabar Allah Umma, soyayyar shi kawai nake so"
Sai ta murmusa tana share hawaye da ƙasar hijabin ta. "Allah ya so ka ɗana, Allah ya ƙaunace ka, Allah ya ji ƙan ka yayi maka rahama ba sai ka mutu ba"
Da ameen ya amsa sannan suka fito mishi da food flask ɗin da suka zo da shi. Nan ma sai da aka yi daru da police, Kamal ya ɗan miƙa musu wani abu kafin suka yarda suka bar shi ya fara cin abincin. Sun fi so su luguiguita shi ne sosai yanda idan Alhaji Tahir ya zo zai ji daɗi yayi musu alheri.
A baki Saudat take bawa Yaseer abinci yana karɓa da wani zaƙuwa kamar zai cire mata yatsu, ita tsoron fama masa ciwon bakin shi take ji.