← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 57

Sashe 6

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuwan Saudat gidan karo na biyu kenan, tun auren Alhaji Tahir da Hajiya Fauziyya shekaru biyu baya sai kuma yau da Allah ya azurta su da samun ƙaruwa, amma kuma gani take kaman an ƙara wa gidan girma da kyau. wai duk wannan gidan mace ce ƴar mace?- take tunani a ranta.

Shi kuwa Kamal ƙiyaste yawan miliyoyin da aka zubar wurin tada gini irin wannan kamar ba a ƙasar shi Nigeria inda miliyoyin mutane suke fama da yunwa bane.

Yanzu har mutane zasu iya rayuwa su kaɗai a irin wannan wargajejen gida suyi barci cikin kwanciyar hankali?- tunanin Yaseer Kenan.

Dakatar dasu da security yayi daga ƙofar shiga ne ya dawo da hankalin su zuwa gare shi, tun kan aje ko ina Saudat har ta fara shiga ɓacin rai bayan yanzu wasu suka shige a gaban su ba tare da an tuhume su ko an bincike su ba.

"Malam Ina zuwa?" Cewar security da ya toshe Idanu da baƙin gilashi.

Ba zuwar Kamal na farko ko biyun sa ba kenan don haka ya saki murmushi tare da cewa "officer Baka gane ni bane?"

"Ban gane ka ba kai wa?"

"Ɗan uwan me gidan ne fah! Sunana Kamal, mun haɗu shekaran jiya nazo gun me gidan ka manta?" Ya ƙarashe da sakin ƙaramin dariyan sanayya don yasan yanzu kam dole ya ɗago shi tunda zuwan shi na bayan ma hana shi shiga yayi sai cikin Sa'a Alhaji Tahir ɗin ya dawo a lokacin, yace masa yaje ya dawo saboda abinci ya dawo ci kuma ba daɗewa zaiyi ba ana jiran sa a office.

Yayi tsammanin yau idan ya dawo yana da direct pass na shiga gidan amma sai security ɗinnan ya ɗan zaro glasses ɗin idanun shi ya lanƙaye ta a karan ƙaton hancinsa ya ƙare musu kallo daga kan Kamal har Suhail a wulaƙance sannan ya maida glasses ɗinshi ya ƙwama.
"Toh idan haka ne ai muma ƴan uwan nashi ne, Please don't waste my time, ku bar wurin nan"

"Mu tafi" Saudat tace da Yaseer. Ya kuwa ja hannun ƙanin shi suka juya zasu bar wurin sai Kamal yayi saurin riƙo hannun ta, yasan idan ta tsaya shima Yaseer nata zai bi.

Kamal ya ƙara faɗaɗa murmushi kafin yace "wallahi ni ɗan uwan shi ne officer, mahaifin su da mahaifiyar mu uba ɗaya uwa kawai suka raba"

Yi yayi kaman bai jishi ba ya juya wurin wani mota da ya tunkaro gidan ya gaida su fuska a sake sannan ya bada izinin a wangale musu su shiga.

"Abban Yaseer ko aljanna ake rabawa a gidan nan ya kamata mu haƙura haka nan" Saudat tace cikin ƙosawa da ɓacin rai.

Juyawa yayi ya fuskance ta cikin faɗa-faɗa yace "Haba Saudatu, ki zamo mai hakuri mana, zai barmu mu shiga fah, ki barni muyi magana dashi"

Jinjina kai tayi "toh shikkenan, munyi gaba sai ka Iso" ta riƙo hannun yaranta da niyyar yanzu ko ya tsayar da ita ba tsayawa zata yi ba.
Wannan wani irin wulaƙanci ne? Wasu sunzo a gaban su wasu sunzo a bayan su duk a keke napep an barsu sun shiga dake su sun sanya kaya masu kyau da tsada sun sha kwalliya kamar suna suka zo tun yau.

Juyawa suka yi suka fara tafiya har sun kusan ƙure garun gidan shi kuwa Kamal yaji haushin ta don haka bai dakatar da ita ba kuma bai bi bayan ta ba, yaci gaba da roƙon mai gadi ya barshi ya shiga don yaje ya haɗu da Alhaji Tahir Idan yana ciki.

"Umman Yaseer!!" Aka ƙwala mata kira daga cikin adaidaita da ya wuce su, hakan ya saka ta saurin waigawa don ganin waye mai kiran. A ƙofar gidan da suka baro mai napep ya faka Inna larai ta fito tare da yafato Saudat da hannu.

Sakin fuska tayi suka nufi wurin ta, sauran ƴan aikin suna fito da kayayyakin da suka zo dashi. "Kardai mun sha saɓani umman Yaseer" cewar Inna larai domin a tunanin ta sun fito daga gidan ne zasu tafi.

"Wallahi Inna larai, Ina wuni yaya zafi"

Miƙawa mai keke naira dubu tayi bayan sun gama cire kayan ya miƙo mata canjin ɗari biyu "Lafiya alhamdulillah, yaya mazaje na?"

Rage tsayi kaɗan Yaseer yayi ya gaidata ta amsa da "mai gida Irin wannan swagger haka! inafa jiran cefane" sai ya murmusa tare da sosa ƙeya a kunyace.

"Toh ku shiga wannan napep ɗin ya maida ku mana, kinga sauƙi yazo muku ba sai kun take ƙarshen titin nan da ba'a samun abun hawa cikin sauƙi ba"

Ta luma hannu cikin jakarta ta ciro wani  ɗari biyun ta haɗa da canjin hannun ta sannan ta danƙa wa Yaseer tana cewa "toh gashi na sayi wankar nan don yayi min"

Saurin jan baya yayi yana ƙoƙarin kwace hannun shi amma ba ƙaramin ruƙo tayi mishi ba don tasan halin shi sarai.
"Ki barshi kawai Inna don Allah" yace kaman zai saka ihu.

"Naƙi na barin, salon gobe ka kunce auren tunda kayi wanka naƙi yabawa?" Ta dunƙula masa kuɗin a hannu kafin ta sake shi sai ya shiga mata godiya.

Kwatance tayi ma mai adaidaitan na unguwan da zasu je, kana tayi musu ciniki. Saudat kuwa har ta shige ciki ganin Kamal ya tunkaro su, ta riga ta saka ma ranta ba zata shiga gidan nan ba kada ma ya ɓata lokacin shi, don haka tace ma su Yaseer suyi sauri su shiga su tafi.

"Inna Larai ba'a barmu mun shiga ba fah" cewar Suhail ganin da gaske komawa gida zasu yi.

Kallon Saudat a kaikaice Inna larai tayi don tabbatar da zancen Suhail, "wai haka Umman Yaseer?"

"Babu komai wallahi Inna" shine abinda bakinta yace amma hannun ta duka ya kaiwa Suhail saidai ya riga ya gudu ya ɓoye a bayan Yaseer.

"Toh me yasa?!" Ta tambaya a fusace.

Shiru Saudat tayi ganin kamal ya Iso ta kawar da kai gefe shima kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai ya gaida Inna Larai sannan ya amsa da. "Kinsan dake an canja masu tsaron gidan shiyasa nake ga wannan bai wayi fuska ta ba"

Kaɗan ya rage Saudat ta saki tsaki amma ta matse.

Inna Larai ta ƙarasa wurin security "akan mene zaka hana ɗan uwan me gida shiga?"

Saida ya sake cire madubin idanun shi ya kalli Kamal wannan karon a mamakance, daga rigan gwanjon dake wuyar shi, haɗe da wandon jeans din da duk sunji ruwa sun gama koɗewa gashi basu samu guga ba, har komai nashi baiyi kama da wanda ya haɗa sanayya da masu gidan da suke gadi ba balle haɗin jini.

"Oh wai dama ɗan uwan shin ne da gaske?"

Cike da takaici Inna Larai tace "Haba kai kuwa malam ɗan sanda? Aikin da aka ɗauke ku yi kenan saboda Allah? Idan tsare mutane za'a dinga yi ana musu tambayoyi kamata yayi ana tsare kowa da wanda yazo a mota da wanda yazo a ƙafa babu bambanci, amma wannan ba yi bane ko kaɗan. Wulaƙanta ɗan adam ba abin yi bane wallahi..."

Taje ta jawo hannun Saudat, mai napep daman ya riga ya dire ta ganin za'a ɓata mishi lokaci. Har ta wuce dasu ciki tana balbali, Kamal ma yayi saurin bin bayan su, Suhail sai tsallen murna yake yi, Yaseer kuwa yunwar cikin shi ne ya dame shi.

Yawan Mutanen da suka tarar a parlourn Hajiya Fauziyya yaso bawa Saudat tsoro har ta fara tunanin ko dai sun ɓata ƙirge ne yaune suna?.
Yawanci baƙin fuska ne sai ta rasa gaida su ne zata yi ko ta share su? Saidai koma ta share sun bata ga ƙyallin Hajiya Fauziyya a parlourn ba.

"Zo muje kiga" cewar Inna larai bayan taje ta ajiye laidar hannun ta a kitchen ta dawo ta riski Saudat tana ta dibi-dibi don haka suka nufi ƙofar bedroom ɗin da hajiya Fauziyya take.

Knocking tayi saida aka ɗauki minti guda kafin kofar ta buɗu Aina'u ta leƙo.
"Ah-ah, Inna Larai kun Iso? Bismillah" ta buɗe mata ƙofar don ta shiga amma ganin su Saudat biye a bayan ta yasa tayi hanzarin riƙe ƙofar.
"Au Inna tare da baƙi kike ne? Da sun jira mu a parlourn ai"

Kafin Inna Larai tayi Magana daga cikin ɗakin suka ji Muryar Hajiya Fauziyya tana tambayar "Aina'u wanene?" Rufe ƙofar tayi kafin ta juya cikin ladabi tace "Hajiya Saudatu ce, Matar Kamalun Jama'are"

Fuska ta saki sosai cikin jin daɗi tace "Ahh, Umman Yaseer zaki ce ba sai kin wahalar da kanki da wannan dogon bayanin ba. Buɗe musu su shigo"

Bata da zaɓin da ya wuce tayi yanda aka ce ba tare da musu ba ta buɗe suka shigo sannan tayi saurin sake datse ƙofar kafin sauran ƴan parlourn su fara tuttuɗowa ciki.

"Ni nama yi fushi tunda sai yau uwa take zuwa ganin ƴarta" cewar Hajiya Fauziyya tana Gyara zama a kan gadon tare da sauƙe ƙafafuwan ta ƙasa, ga bakin Reina manne da ƙirjin ta tana aikin ci ba ji ba gani.

Shimfiɗar fuskar da Saudat ta samu ya saka ta sakin fuska itama cikin ɗan jin nauyi tace "kiyi haƙuri Aunty, jikin ne yaƙi daɗi."
Kallo take ƙarewa makeken bedroom ɗin da take ayyana idan baiyi girman gidan su ba baki ɗaya toh tabbas zai iya fin rabi.

Ga wani makeken gado da bata taɓa ganin mai kyau da girman shi ba, tsayin saman gadon kuwa ya doshi taɓa ceiling. Ɓangaren Kayan jarirai kuwa ga wardrobe girman shi kamar na wanda za'a kai ɗakin miji saidai anyi shi ne Musamman na jarirai abun sha'awa da cartoon ɗin Masha and the bear a jiki. Ga kuma set na drawers shima, haɗi da gadon jarirai shima pink a gefen gadon uwarta.

Cikin zuciyar Saudat tace "Allah ka azurta mu da mai albarka."

Sai muryar Hajiya Fauziyya ta jiyo Cikin tausayawa tana cewa "Allah sarki, Allah ya raba ku lafiya kema ki samu mai hana ki barci" ta ƙarashe cikin sigar zolaya.

"Bata barin ku kuyi barci ko?" Saudat ta Isa bakin gadon tana leƙa fuskar Reina dake tsotson mama idanun ta a rufe daga ɗan nesa.
Chapter 6 · 0% Book details