Sashe 39
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wanda ya gagara cin ko wani irin jarabawar gama secondary har zai iya gama matakin gaban ta a turai? Idan na tura ka ma ai asarar kuɗi na zan yi ga ni mai kuɗin banza. Don haka ka maida hankali wallahi " Alhaji Salisu ya miƙe yana kallon agogon hannun shi, lokacin da mai aikin gidan suka fito da Reina wanda tayi wanka ta shirya.
"Yaseer!!" Ta ƙwala mishi kira daga ƙofar mashigar gidan, wanda yayi sanadiyar karkatowar hankalin su baki ɗaya zuwa gare ta, sai ta ɗaga hannun ta sama tana yiwa Yaseer ɗin bye-bye kaman hannun zai tsinke.
Jamal ne ya ɗaga mata hannu yana washe baki yayin da Alhaji Salisu ya maido da duban shi wurin Yaseer, yana tsaye ne kawai fuska ba yabo ba fallasa yana kallon ta har suka saka ta a cikin mota tana murna zata je wurin daddyn ta.
Daman wurin Alhaji Tahir yake da niyyan zuwa, tunda yanzu shi bayi da weekend kullum yana office.
Idanun shi ya mayar kan Jamal yayi maganar da Yaseer ya fahimci da shi yake yi "Idan ka sake zuwa bai fito a kan lokaci ba, ka tura a sanar da ni." Sannan ya sauƙe murya daidai kunnen Jamal yace "alƙawarin da na ɗauka last week tabbas zan cika shi"
A firgice Jamal ya waro idanu zai yi magana ya ɗaga mishi hannu. "Please try me and see young man." da faɗan haka ya wuce ya ƙarasa wurin motar da tun fitowar shi ake warming ɗinta, ya shiga gidan baya wurin da Reina take, driver ya ja, idanun Jamal da suka ciko da ƙwolla suka mishi rakiya.
Ran Yaseer tass ya buɗe wani sabon marker ya cigaba da bayani daga inda ya tsaya.
Babu laifi ya ɗan saurare shi suka cinye sauran lokacin, sannan Jamal ya koma gida, yaseer ma ya tafi nashi hidiman sai 3:30 ya dawo yayi sallan la'asar suka ci gaba, sannan bai sake Jamal ba har saida suka cinye lokacin da aka bashi tass, dukda Hajiya Hauwa ta turo a kira shi ya kai sawu uku.
.......
"Anya Fauziyya ba aljanu gare ki ba? Ko su ne suka aure ki suka hana ki zaman aure?" Cewar babban yayar mahaifin ta.
Daga kai Ummi tayi ta dube matar amma sai ta mayar da duban ta gefe domin bata da ta cewa.
"Ko kuma dai ta samu mai hure mata kunne ba? Domin kin san idan aka lura mutum na cikin kwanciyar hankali maƙiya ba su barin shi haka nan" cewar ƙanwar mahaifiyar ta.
"Ba'a hure mata kunne tun tana amarci ba sai yazu da ta shekara fiye da goma a gidan aure?"
Sun haɗu sun tasa Fauziyyar a tsakiya da faɗa a kan abinda ya haɗa ta da Tahir har ya yanke shawarar sakin ta, bata ce da su kanzil ba, tun da ta san ba don saboda ita suke wannan tada jijiyoyin wuyan ba, sai don saboda abinda duk familyn suke samu daga gare shi da suke tsoron yankewa.
Bin su tayi da idanu, ba zallan ƴan uwan mahafiyar ta kawai ba har da na mahaifin ta, duk sintirin da Aina take yi a tsakanin gidajen aure basu taɓa irin wannan meeting ɗin ba.
Hasali ma idan ta tasu ne sun so kiran ta family house ɗin su Abban ta ne ayi mata faɗan a can amma laulayin dake nuƙurƙusan ta ya saka yanzu bata iya fita ko nan da ƙofa, gashi tun da ta dawo bata komai sai aikin kuka.
Autar su mahaifin ta ne ta girgiza kai "samm ni bani tunanin matsalar daga gare ta ne, domin ko ɗan kishiya aka bawa Fauzee zata riƙe har ace ƴar cikin ta take azabtarwa harda yunƙurin Kisa. Sai dai idan asiri ake mata domin a raba su ɗin"
"Kisa fa kika ce Amina. Ta yaya uwa zata yi yunƙurin kashe abinda ta haifa?" Ummi da abun ya fara isarta ta amsa.
"Hmm Aunty Hafsatu asiri fa aka ce miki, ai abinda yafi haka ma za su iya saka ta tayi kawai don su ga sun fitar da ita daga gidan, kuma gashi sun ci riba. don haka zama bai gan mu ba magani za'a bazama nima mata tayi ta koma"
Miƙewa Ummi tayi kawai ta bar musu parlourn, domin idan ta matsa da bada shawarar a bi abun nan a hankali gani zasu yi kaman ita ce bata son Fauziyyar ta koma ɗakin ta.
Tana miƙewa yayar ta da bata saka baki a zancen ba ta tashi ta bi bayan ta suka rufo uwar ɗakin.
"Ki kwantar da hankalin ki don Allah Hafsatu, in sha Allah komai zai daidaita. lokacin da za su shirya ya maida ta ɗakin ta ma babu wanda zai sani sai dai su ji labari"
"Ni tawa jarabawar kenan, a duk lokacin da zan yi auren ƴa sai wata a cikin su ta dawo min" Ummi tace da ƴar uwar ta cikin jimami.
"Ta yaya zaki ce haka Hafsatu? Keda zaki gode ma Allah duk yaran ki babu wanda ya taɓa rasa mijin aure? Da sun tasa suke samun manema mu ba ga namu nan jibge a gida ba"
"Haka ne alhamdulillah, amma wani auren da za'a ta yi maka jeka ka dawo ko kuma hankali ya gagara kwanciya sai nake ga kaman gwanda ba'a yi ba. Sannan ki ga yanda aka yi auren yarinyar nan abubuwan da suka dinga faruwa. wallahi ban sake samun cikakkiyar nutsuwa a kanta ba tun Ranar da ta saka ƙafa a gidan shi".
"Kada kice haka don Allah, dukkan mu yanzu fatan mu ta koma ɗin, tunda rabo har biyu ya ratsa ga na uku a hanya kamata yayi a manta da baya da abinda ya ƙunsa. Ta koma kan yaran ta kawai shi ya fi"
Ummi ta ja dogon numfashi ta furzar. "Gashi duk sun gama razanar da Sajida, tun da Fauzee ta dawo itama take kukan ta fasa, auren da watanni huɗu kawai ya rage mun riga mun karɓi tambaya da sadaki, yaro bayi da aibun komai bai mata komai ba kuma, ta ina zamu fara ce masa mun fasa?"
"Lallashin ta zaki yi, ki haɗa su da Fauziyyar ki yi musu nasiha idan komai ya lafa, kinga itama yawan koke-koken nan zai iya cutar da abinda ke cikin ta"
"Shikkenan, zan ƙoƙarta, Allah ya shige mana gaba"
......
Miƙewa yayi bayan ya gama gaida Hajiya Hauwa ta amsa, ganin Alhaji Salisu bayi kusa ya juya kawai yayi tafiyar shi.
"Zahra hau sama ki taso Reina ta karya" cewar Hajiya Hauwa da ƴarta wanda zasu kusan zuwa tsara da Reinan amma ta girme ta.
"Hmm, ba barci fa take yi ba wallahi Umma, tun asuba ina jinta tana danne-danne a tab sai gari ya waye ki ganta kaman mushe"
Da faɗa-faɗa tace "kul! Kada ki bari Daddyn ku yaji wani magana daga bakin ki a kan yarinyar nan idan ba haka ba zai iya sassaɓa miki, ki bar ta ta ƙaraci zaman ta har ta tafi...."
Kirif! Yaseer ya rufo musu ƙofar don haka bai jiyo ƙarshen zancen su ba yayi gaba abinsa.
Yau minti 20 kawai Jamal ya ƙara a kan lokaci ya fito, cikin shiga ta mutunci jallabiya har ƙasa. sannan ya shiga bawa Yaseer haƙuri murya can ƙasan maƙoshi fuska a turɓune, tare da uzurin karyawa ne ya riƙe shi.
Kasancewar mahaifin shi ya tilasta shi yayi hakan kuma yace zai tambayi Yaseer ɗin kafin ya tafi.
Taɓe baki kawai Yaseer yayi ya shiga abinda ya kawo shi.
karatun dai bayi wani tafiya saboda daƙiƙanci irin na Jamal amma dai Yaseer yana kamanta ƙoƙari.
Ƙarfe goma da ɗoriya ta fito tare da sauran yaran gidan tana baza idanu ko zata hango shi dukda kuwa bata da yaƙinin hakan, daman zumuɗin zuwa wurin daddynta da ta kusan kwana biyu bata gan shi ba ya saka ta tafiya a jiyan.
Amma da mamakin ta yau ma sai ta hango shi a wurin jiya.
Da gudu ta ƙarasa Wurin su ta faɗa jikin Yaseer dake zaune bayan ya bawa Jamal classwork yana jiran ya gama, tana haki da dariya.
"Yaseer ka zo?"
"Baki iya gaisuwa ba ko?"
"Na iya" tace kawai.
"Sai nace ki yi?"
Sai ta girgiza masa kai kawai bata kuma yi gaisuwan ba.
Girgiza kai yayi ya ɗan tura ta daga jikin shi da hannun shi na hagu amma a maimakon ta matsa sai ta kama hannun ta dafa ta ɗale kan cinyar shi ta sha zamanta tana kan washe masa haƙwara.
Shi kuwa mamaki ya hana shi motsi ganin buskuɗa ƴar nine years mai garin jiki irin ta ma wai har yanzu tana zama a cinya.
"Baby baki gan ni bane?" Jamal ya kira ta da ya lura baki ɗaya hankalin ta yana kan Yaseer.
Kafin tayi wani yunƙuri Yaseer ya sauƙe ta daga jikin shi ya haɗe fuskar nan kaman bai taɓa dariya ba don ya lura akwai suntattun notuka a kan yarinyar.
"Babba da ke kike zama wa maza a cinya? Ba'a faɗa miki babu kyau ba a islamiyya?"
Kan kace me har idanun ta sun tara ruwa.
Ta girgiza masa kai. Toh yaushe ma taje islammiyar balle har a faɗa mata ta ji?.
"Auntyn ki bata faɗa miki ba toh?"
"Ai aunty na bata nan, wai daddy ya sake ta" ta amsa da muryar kuka saboda bata saba da wasu bayan Auntyn ba suna mata faɗa ba.
Yaseer ji yayi kaman an watsa mishi ruwan sanyi a jikin shi, cikin zuciyar shi yace "mai ya faru da har Alhaji Tahir zai iya rabuwa da ita?" Amma ashe maganar a fili yayi.
"Na ƙona ma Maama baki ne shine ta dake ni na faɗo daga stairs na suma shine Daddy yace wai ta je gida ya sake ta" ta labarta abinda ya faru babu kwama babu full stop kaman yanda ta ji ƴan uwan mahaifin ta na mayarwa a tsakanin su.
Shiru Yaseer yayi, don ji yake yi idan har ya sake tambayar wani abun toh Reina zata cigaba da sanar da shi abubuwan da zasu girgiza duniyar shi.
Domin yanda take amsar laifin ta da ƙwarin guiwa babu tsoro ko fargaba ma ya bashi tsoro.
"Toh yaushe zaka kawo min abun daɗin?" Ta tambaya jin yayi shiru.