← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 57

Sashe 21

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani tafiyar lokacin kamar iska, yana wucewa bayi canza komai a cikin rayuwar mutum, yana tafiya ne kawai da abu marar nauyi kamar laida da yaayi, ya ɗan matsa da shi kaɗan daga muhallin sa zuwa wani sabon muhallin.
Amma wani tafiyar lokacin tana zuwa ne kamar guguwa. Ƙasa, shara, ƙura, idan yayi ƙarfi har mutum yakan iya ɗauka, yayi walagigi da shi kafin ya jefar da shi a wurin da yaga dama.
Zuwa lokacin da zai lafa zaka fahimci komai ya sauya ba tare da idanu sun lura ba.

Sallama yayi daga ƙasan maƙoshin sa kana ya shigo ɗakin da Saudat ke ciro kaya daga cikin sabon wardrobe din da bata daɗe da siya ba domin wancan ya kasa musu a yanzu.

Tsayuwa yayi daga ɗan nesa da Ita ba tare da yace komai ba yana jiran har sai ta lura da kasancewar shi a wurin kafin ta faɗa mishi dalilin kiran da tayi mishi.

Ɗago kai tayi tana kallon tsayin shi wanda ko ita dake tare da shi kullum tana mamakin shi balle wanda ya jima bai gan shi ba.
"Baka iya sallama bane?"

Tana ganin yanda wani abu da ya fara taso kai a wuyan shi ya motsa alamun sai da ya haɗiyi miyau kafin a hankali yace "nayi sallama" ya lashi laɓɓen bakin shi saboda ya gagara sabawa da wannan murya da ba tashi ba.

"Shine zaka tsaya min sheƙeƙe a kai?!"

Rage tsayin sa yayi ta hanyar sauƙe guiwowin shi a ƙasa yayi zaman tahiya kana ya sake buɗan baki yace "gani" ai kuwa duk yanda yaso tsuke muryar sai da tayi crack, ya rufe idanu tare da sauƙe kan shi cike da kunya, shi yasa bai cika son buɗan baki yana magana ba.

Murmushi Saudat tayi don abin nashi ma ya daina damun ta ya koma bata dariya.

"Me kake yi?" Ta tambaya.

"Karatu" ya bata amsa.

Ta san karatun boko yake nufi domin Last year ya sauƙe haddan Alkur'ani, a yanzun kuma yake shirin zana JSSCE, zuwa SS1.

"Toh daman Aunty ne ta kira ni ɗazu wai tana gayyatar yaran nan badday."

Ya ɗago ya kalle ta tare da kaikaita kai kaɗan yace "wata Aunty?"

"Aunty dai maman Hafsatu"

ta shiga mayar da kayan bayan ta zaɓa wanda Suhail da Sabir zasu saka.

Kenan na birthdayn ƴar ta Reina ce? Shekarun ta uku yanzu! Lallai a kwana a tashi babu wuya a wurin Ubangiji, last ganin da yayi mata tana tsumma bata wuce watanni biyu a duniya ba.

"Ina za ka iya zaman gidan kai kaɗai? Dan nasan abban ku ma ba zama zai yi ba idan babu kowa, in yaso sai kayi karatun ka babu takurin kowa.

"Toh shikkenan Umma, sai kun dawo a gaida min da auntyn"

"Zata ji, sai ka ɗebi shinkafa ka gyara ka dafa muku, akwai sauran miyan da nayi jiya a kitchen zai ishe ku, sai ka ɗuma shi".

Da toh ya amsa yana miƙewa don ya fahimci ta kai ƙarshen zancen ta ya koma jikin littafi kaman ko yaushe.

Yanzu karatun shine kawai abinda yake yi, domin tun da Abban shi ya samu sauyin aiki ya hana shi zuwa shagon koyon ɗinki, har umman shi ta so yana siyar mata da kasuwar ta a waje amma ya ƙi, ya hana shi komai bayan karatu.

Yana faɗa mishi a ko wani lokaci karatu shine gatan shi, shi ba kowa bane idan bayi da Ilimi. Haka ne, wannan gaskiya ne, duk wanda bayi da ilimi na addini shi ba kowa bane, ilimin addini shine gatan kowani musulmi. Amma kalamin shi na ƙarshe ya tabbatar mishi da tunanin su yazo bambam.

"Yaseer babu inda zaka je a duniyar nan idan baka da ilimin zamani, haka zaka ƙare ƙasƙantacce, a wulaƙance,"

Wannan ba haka yake ba, wannan gurguwar fahimta ce. Mutane nawa suka yi arziƙin da ake bugawa a jarida ba tare da ilimi ko na sakandare ba? Mutane nawa ne suka shiga siyasa ko kwalin jami'a basu da shi? Sannan mutane nawa ne suke da kwalayen ba ɗaya ba ba biyu ba amma suke kan fama da rayuwa?.

Lallai karatun boko nada amfani musamman a irin wannan zamani da yawancin wurin da mutum zai shiga a ko ina sai an buƙaci shaidar su? Amma fa ba shine hanyar arziƙi ba, wannan hurumi ne ba Ubangiji. Ya azurta wanda yaso a lokacin da yazo babu mai tambayar shi me yasa.

Amma tunda burin iyayen nashi shine yayi karatun, zai yi da dukkan lokacin shi, da dukkan ƙarfin shi, iya iyawar shi.

Sai da ta gama shiryawa cikin leshin da Hajiya Fauziyya tayi mata kyautar shi tun jegon Sabir, don zannuwan biyu su suka zamo mata na ganin gwamna, bata saka su jdan ba wani wuri mai muhimmanci za'a je ba. sannan ta shirya yaran suka yi shirin ficewa kafin kuma su sake ɓata jikin su, Yaseer ɗin ya fito daga bakin ƙofa yana musu Allah ya kiyaye.

kusan karo suka so yi da Kamal, ta dawo cikin tana mishi sannu da dawowa, sannan ya shigo shima yaran suka yi saurin rungume shi suna oyoyo.

"Har zaku fita"

"Eh ka san maghriba yana yi da wuri yanzu, gwanda muje muyi mu dawo"

"Haka ne. Toh shi yayan mu fah? Banda shi ne?"

"Eh Abbah, ina shirin exams ne" yaseer ɗin ya amsa.

"A'a abu na wuni ɗaya? Yi sauri ka shirya ku tafi"

"Abun yara ne fa Abban Yaseer " ta san da ba gidan su Alhaji Tahir bane koda Yaseer ɗin ya riga ya shirya hana shi fita zai yi yace mishi ya girma ma ana fita unguwa da shi.
Ko yaushe zai dawo daga rakiyar wannan mutanen ne?

Tabbas rayuwa ta zo musu da sauyi, amma ba irin sauyin da za'a ce mutanen nan sun rungume su hannu bibbiyu ba. Sauyi na walwalan rayuwa suka samu, sauyin rashin damuwar babu abinda za'a ci gobe.
Sauyin cin mai kyau da kwana a wuri mai daɗi da tsafta.

Amma ko suturar da suke sakawa har yanzu kallo ɗaya zaka yi ma yaran su kayi ma su Yaseer ya bambance maka ko goma ta zube ta fi biyar albarka.

Kafin ta gama tunani har Yaseer ya shirya cikin wani rigan polo Emrald green da jeans ya taje kan nan ya saka turare.

Sai Saudat ta gagara fahimtar yayi saurin shiryawar ne Saboda bayi son suna samun saɓani a kan shi kaman ko wani lokaci ko kuma don yana son zuwan ne da gaske? Saboda bata ga damuwa a kan fuskar shi ba.

Ta fahimci bayi son zuwa gidan sauran a gaisuwar Sallah ko idan hidima ya tashi an je musu barka. Shi yasa bata sake cewa ya raka ta idan wurin su zasu je, don itama bata da yanda zata yi ne.

Ɗaukan Sabir yayi a kafaɗa wanda yake tsotsan mintinnda Abban ya kawo mishi.
"Kada ka ɓata min kaya" ya mishi gargaɗi shi kuma ya gyaɗa kai kafin ya cigaba da tsotsar kayan shi.

Laidan hannun shi Kamal ya miƙa wa Saudat, ta buɗe taga packet ɗin sweet ne guda biyu a ciki.

Gashi sai ki basu wannan kuma a gaishe su sosai don Allah.
Karɓa tayi da toh, ya raba sauran wanda ke aljihun shi ma Yaran harda Yaseer don bayi ganin shi ya girma duk da a yanzun tsaff zasu jera a tsayi saidai ya fishi kaurin jiki.

.....

Tsaye take a gaban kitchen Island ɗin tana jujjuya abu a cikin roba da whisker, amma kallo ɗaya ya isa ya sanar da cewa bata cikin nutsuwar ta.

A gaban ta cake ne mai hawa uku wanda tayi shi kala daban-daban sannan ta saka butter cream ta haɗe su wuri ɗaya. Yanzu haka whipped cream da zata lulluɓe cake ɗin da shi ta saka wa condensed milk ta madara shine take juyawa da hannu.

Amma har ya fara sauƙa saboda sanyin jikin shi ya fara ƙasa saboda jujjuyawar da take mishi ya wuce iyaka.

Tunanin maganar su da Alhaji Tahir take yi a daren jiya. Hukuncin da ya sake yankewa a kan yaran shi. Yaran shi mana, tunda ya tabbatar mata bata da iko a kan abinda ya shafi rayuwar su, ikirari yake da su hakkin shi ne, don haka zan sauƙe wannan hakkin da duk abinda zai iya.

Toh shine kuma hukuncin har ya shafi abin da bai zo duniya ba? Harinyar da sanin jinsin ta ma basu daɗe ya yin shi ba? Ko shikkenan ita ta dawo injin haifa masa yara bata da iko a kan nata rayuwar ma?.

Ina a kan Reina ne? Ita ce taƙamar shi? Tun da haka ya zaɓa ta fara zuba mishi idanu da shi da Ita tun tana cikin tsumma kuma zata ci gaba da zuba musu har ranar da za su gane kuskuren su, su juyo ga gaskiya, idan lokaci bai kure musu ba kenan.

Mangaje ta aka yi har sai da tayi baya tare da tallafo ƙaton cikin ta tana salati. Ba sai an faɗa ba ta riga ta san waye, ita kaɗai ce mara nutsuwa a baki ɗaya cikin gidan.

A zafafe tace "me yasa baki da hankali ne Reina?! Ban faɗa miki ki daina min guje-guje ba sai na saka bulala na zane ki?! Wawuya kawai"

Ƙifi-ƙifi tayi da idanuwa don tabbas tana jin tsoron mahaifiyar ta, amma kuma bata iya bada haƙuri ba, bata san shi ba.

Juyawa tayi zata bar kitchen ɗin da gudu ganin mai aikin da tayi wa rashin kunya ta shigo hannun ta riƙe da ƙaramin carpet ɗin.

"Ki dawo nan nace miki" ta daka mata tsawar da har ita mai aikin Saida ta razana".

Ta juyo a hankali hawaye na fara bin fuskar ta. "Aunty wayyayi... Aunty wayyayi.."

Idon Hajiya Fauziyya ne ya kai kan rinannen carpet ɗin don itama Reinan shi take kallo.

Ba sai an faɗa mata ba ta san cewa ita ce ta ɓata don yanayin ta ya gwada.

Zagawa tayi ta ƙarasa ta zaro tsintsiyan kwakwa guda biyu ta nufo ta da shi.

Abun ya ishe ta, duka kan sai ta daki Reina idan yaso Tahir ya dawo yayi farfesun ta ya shanye.
Chapter 21 · 0% Book details