Sashe 14
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Parking yayi ya zuge window sannan da hannu yayi alamu ma mai ƙurƙura da ya tafi kawai, kana ya juya kan motar suka koma hanyar da suka baro.
"Lafiya Malam Adamu? Ina kuma zamu je?" Aina ta tambaya.
"Kiyi haƙuri nayi mantuwa ne, akwai kuɗin da tsohuwar ta bayar in maida wa alhaji shine hajiya tace in dawo mata dashi." Yayi mata bayani yana ƙara gudun motar don suyi sauri ya samu komawa kafin Alhaji Tahir ya dawo ya samu bayi nan on standby.
"Har Nawa ne kuɗin haka?"
"Dubu ashirin ne?"
"Shine zamu koma a kan dubu Ashirin bayan mun kai musu kaman shi sau biyar? Ka riƙe kawai mana ko kuma ka raba mana mu koma muce mun kai"
Kallon ta yayi a kaikaice harma ya manta da tuƙi yake, sai a lokacin idanun shi ya kai kan saiti na kayan wanka da shafa na yara dake boye a kasan seat ɗin shi. Murmushi ne ya ƙwace mishi yace "baki tunanin asirin ki zai tonu idan baki basu abin nan ba?"
"Toh wa yace maka nasu ne?"
Dariyan kinma raina min hankali yayi yace "tunda haka kika ce shikkenan"
Da suka isa gidan ma ita ya bada kuɗin don ta shiga ta bawa goggo hannu da hannu. "Sauran kuma ki zari wani abu a ciki, ta riga da ta san nawa ne, don ita ta ƙirga ta bani"
Baki ɗaya sai Aina taji ta muzanta, tunda har ya buɗe baki yake gaya mata magana haka bayan da gaisuwar arziƙi ne kawai a tsakanin su ta tabbatar ta gama zubar da mutuncin ta a idanun shi. Saima ta fara tunanin kodai ta haɗa da kayan shafar ne ta kai musu? Amma daga ganin packing ɗin ta san ba mai arha bane, kuma komai akwai a ciki harda soson shafa powder na yara da su soson wanka. Idan siyarwa zata yi zata samu abin da yafi dubu 50 wa'innan mutanen kuma ba sanin darajar kaya mai tsada suka yi ba.
Babu ɓata lokaci ta shiga ta maida kuɗin ta fito, a ɗarare haka ta shiga motar suka tafi.
.....
Su goggo sun gama shiryawa tsaff da gari ya gama wayewa zasu wuce tasha su kama motar Jama'are.
Dunƙulawa amarya kuɗin Saudat ta sake yi bayan ta maido mata da shi, idanun ta da maiƙon hawayen kewa tace. "Amarya don Allah ki karɓa ku rage kuɗin mota"
"Ke da'alla, ance miki don ki bamu kuɗin mota muka zo? Da ace bamu da kuɗin mota kinsan ba zaki ga ƙafar mu ba don haka riƙe kayan ki" ta miƙe ta bar mata kuɗin a wurin sannan ta ci gaba da shirya jikokin ta.
"Toh Saudatu, zamu koma inda muka fito, Zamu tafi mu barki da haƙurin ki. kina dashi amma ki ƙara, kina ƙokarin tarbiyya ma yaran ki don mun shaida a kan Yaseer amma ki ƙara sannan kuma ki ƙara addu'a sosai da sosai, duk macen da ta fara tara zuri'a cikakken bacci a ko wani dare ba nata bane, dole kina raba wasu dararen kina kai kukan ki ma Allah idan kina son kiga daidai a rayuwar yaran ki"
goggo ta miƙo mata kuɗin da suka haɗa wanda ya tashi dubu sha shida sai kuma dubu cassa'in da Aina ta kawo, ya tashi dubu ɗari da shida kenan.
Ta samu zannuwa ma wurin guda takwas duk da rabin su rubber ne ko mix cotton Amma goggo da amarya da wani kawun su mai gold suka saka mata manya har biyu. Haka ma jariri ya samu kaya daidai gwargwado ga kuma sauran kayan abinci da ya rage an jibge musu a ɗakin su Yaseer, lallai wannan haihuwa yazo musu da alkhairi.
"Kina samun kanki ki ci gaba da ƴan sana'oin ki, ban yarda ki bawa Kamalu kuɗin nan ba kiyi jari dashi kinji na faɗa miki."
Karɓan kuɗin tayi da godiya tana jujjuya shi a hannun ta, gani take yi sunyi mata yawa idan har aka ce ba zata bashi ba, zata iya sana'a koda babu jari don har wankin kuɗi tayi nauyin ciki yasa ta bari. Amma shi idan ta bashi kudin nan ko teburi zai kafa yana kasa wani abun idan ya dawo daga aiki, Yaseer kam tela take so ya zama amma da ko shima zai iya taya shi idan ya dawo daga makaranta.
Shima kamal saida yasha tashi nasihar da bata gajiya da mishi a ko wani lokaci kafin ya raka su har tasha har saida motar su ta tashi kafin ya dawo. Ya samu har Yaseer ya gama komai kaman yanda ya saba shi da suhail sun wuce makaranta.
Zama yayi a gefen Saudat yana cire taɓani kasha hadisin dake kan shi, "Saudatu goggo ta tafi. Satin ta guda a cikin gidan nan"
"Wallahi kuwa, bamu da abinda zamu ce sai Allah ya ƙara tsawon rai da albarkan rayuwa."
Ɗaura zancen shi yayi domin ta fahimci abinda ke ranshi. "A wannan sati gudan babu wanda ya leƙo ko ya turo kai ko Ita su turo direba ya kai musu ita su gaisa idan gidan nawa ne ba zasu iya zuwa ba."
Zata iya rantsuwa wannan ne karo na farko da taji ya koka da su a kan duk wani abun da zasu yi mishi kuwa, saboda a yanzu mahaifiyar shi suka taɓo.
Yaci gaba da cewa "kuma dukkan su babu wanda banje har ƙofar gida na shaida masa zancen haihuwar ki ba har matan, da kuma zuwan goggon a karo na farko cikin shekaru 4. Bayan Alhaji Tahir ɗin da muka samu matar shi babu mai tunanin ko aika ko saƙon gaisuwa."
Ba na gaya maka ba! Shine kalamin dake cikin ranta amma sai cewa tayi, " sai haƙuri, daman haka duniya take, ba kowa zaka so da zuciya ɗaya shima ya so ka haka ba"
"Hmm, babu komai, Allah ya bamu ladan soyayyar da muka yi musu saboda Allah " da ameen ta amsa ya miƙe shima ya shirya ya wuce wurin aiki aka bar Saudat a gidan daga ita sai baby suka sha barcin su tunda ga wutan nepa kuma mai sawa a kashe fankan yanzu bata nan.
......
Da lokacin da kake ƙirga shi da wanda baka bashi hankalin ka ba wanne yafi saurin wucewa ne? Don tun jiya Hajiya Fauziyya ke mamakin wai har kwanan abinda ta haifa 40 a duniya.
Kuma tun jiyan suke ta tiƙi-taƙa da Alhaji Tahir a kan yawon Arba'in. A karo na farko da zubar da hawayen ta bai saka ya canza ra'ayin shi ba, ya mata iyaka kuma ya kafu a kan zancen shi, A dalilin Ƴar shi Hafsatu Reina.
Ya jaddada mata yawan gidajen da ya amince taje daga fannin ƴan uwan ta, da wanda bai yarda ko unguwar ta leƙa ba. Sannan su wanda ya amincewa ya bata adadin lokacin da zata ɗauka a can ɗin ciki harda gidan nata iyayen kuwa. Maganan dubo ƴan uwa dake ƙauye kanma bata samu zarafin fara mishi ita ba.
Ɓangaren da bai kafa mata sharuɗa ba kawai shine bangaren gidajen ƴan uwan shi, saboda matakin da suke na rayuwa yazo ɗaya hakama tsarin su.
Taso ta fasa zuwan baki daya amma sai taga shi zaifi son hakan ma, kuma ita ce da asara. Haka ta shirya ranan ta fita suka fara zagawa da driver yana zaman jiran ta a waje, da lokacin da Alhaji Tahir ya bata kuwa ya cika haka zaiyi ta horn har sai ta fito, wasu gidajen ko ruwa bata samu ta saka a bakin ta. Kuma haka zaiyi ta addaban ta da kira yana tambayar ta yaya lafiyar Reina idan bata ɗauka ba shima ba zai fasa kiran ba har sai ta ɗauka.
Ƙarshe da abin ya ishe ta wajen gidaje 2 haka ta haƙura da zuwa tace driver ya kaita gidan su kawai tun kafin la'asar ma tayi.
....
"Matar Alhaji yaya aka yi?" Mahaifiyarta ta tsokane ta cikin jin daɗin yanda ƴar tata ta murje ta canza a cikin shekaru biyu, ga cikowar jego ya ƙara mata kyau, ba zaka ce Fauziyya ƙashi da rai bace kamar yanda ƴan unguwa suka saka mata tsabar rama Saboda rashin cin abinci gata kuma tana da ɗan tsayi shiyasa ramar yake nunawa sosai (kamar ƙawata Zahra😹)
"Ummi na kusa kamuwa da postpartum depression" tace tare da sauƙe ajiyar zuciya ganin wani kiran na Alhaji Tahir na sake shigowa cikin wayar ta.
Rejecting kiran tayi cikin jin haushi, duka-duka ko minti talatin bata yi da shigowa ba, kuma tazo ta samu umman da kanta a kitchen saboda shirin zuwan nasu, sai yanzu ta samu kanta aka zauna za'a gaisa.
"Subhanallahi, depression kuma? Me zai saka miki depression Fauziyya baki rasa komai ba, ko Tahir ɗin ya daina kula da ke ne?"
Girgiza kai tayi ta saka yatsar ta manuniya ta ɗan zunguri goshin Reina tace "takwarar ki ne take son shiga tsakanin mu" bata bawa Fauziyya kunya ba ta ɓare baki kaman yanda tayi tsammani kafin tace "kin gani Ummi, gaba ɗaya ta rikita ni ta rikita shi, Idan kika jini da shi to a kanta ne, ni kawai zan bar miki ita a nan in koma ni kaɗai idan ta gyara hali sai in dawo in ɗauke ta"
Dariya Ummi tayi kana ta karbi Reina daga hannun Fauziyyar, ta tabbatar tana iya kokarin ta. Daman Bata da son yara bata da hayaniya, ga ƙananun shekaru, ba don matsawar Alhaji Tahir ba da sai a yanzu da ta haura Ashirin da biyu zasu yi mata aure lokacin ta gama karatun ta amma ba haka Allah ya tsara mata ba.
"Idan bata gyara halin ba fa? Sai ki ci gaba da barin ta a nan? Mahaifin ta zai yarda?"
Wani kiran ne ya sake shigowa wayar ta bayan saƙon da saida kiran ya shigo ta lura da shi.
'kada ki kashe min waya Fauzah, ki dawo da Reina gida kafin wani ciwon ya kama ta, kinga jaririya ce bata da ƙwari'
Taɓe baki tayi da gadara ta sake rejecting kiran ta saka shi a Do not disturb kafin ta maida hankalin ta wurin Aina da ta shigo da abincin da Ummin ta bar mata ta ƙarasa.
"Yaya Aina irin wannan ai sai yunwa ya kashe mutum" tace lokacin da ta dire tray ɗin a gaban ta.