Sashe 22
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuka ta saka tun kafin tsintsiyar kwakwan ya kai jikin ta tana tsalle cike da tsananin tsoro "Wayyo Aunty! na tiga uku!"
Sai ga fitsari tsirrr ta sake shi na tsoro daidai lokacin da aka yi sallama a ƙofar kitchen ɗin dake buɗe Saudat ta shigo ɗauke da murmushi, Reina kuwa tayi wurin ta da gudu domin ta san duk kitchen ɗin babu mai iya ceton ta.
Da wani ne yace mishi hancin yarinyar nan zai taɓa tasowa da sai yayi rantsuwa kafin ya musa.
*Saliha Ahmad Na'ibi (seemahwrites)✨*
*REINA 💍*
16....da sauri Saudat ta maida ta bayan ta, ya kasance ta mata shamaki tsakanin ta da Hajiya Fauziyya.
"Dan Allah ki barni in kewaya yarinyar nan Umman Yaseer" tace tana ƙoƙarin janyo Reina daga bayan Saudat.
Ganin zata iya cin mata daga wurin yasa da gudu ta kauce ta koma bayan Yaseer dake biye da Saudat ta ɓuya, ta riƙe wandon jikin sa gamm jikin ta na kyarma.
Da wani ne yace masa hancin yarinyar nan zai taɓa tasowa da sai yayi rantsuwa kafin ya musa.
Sai dai ɗan hancin caɓa-caɓa yake da majina saboda kukan da ta sha na tsoro.
"Haba Aunty, kiyi haƙuri mana, wanda ake wa murnan badday kuma ita ake duka?" Saudat tayi ƙoƙarin tausar ta.
"Idan ba zane ta nayi ba bana jin zata dawo cikin hayyacin ta. Haba! Yarinya kamar wanda ifiritai kewa fitsari a tsakar ka? Bata ji ko kaɗan? Kiga ta'adin da tayi min fa!" Ta karɓi carpet ɗin tana gwada ma Saudat.
Karɓan tsintsiyan kwakwar tayi daga hannun ta "yanzu kam ta ji tsoro, ba zata sake ba."
Ta watsa mata harara daga yanda take ɓoye. "Zaki zo a ɗauraye miki jiki ne ko sai na ƙaraso wurin?"
Sai ta ƙara ƙanƙame Yaseer domin ta san idan taje wurin ko da hannun ne sai ta dake ta tunda tayi niyya.
"Kije ba za ta miki komai ba"
Ɗaga kai tayi ta kalle shi, idanun ta sun sake cika da ƙwalla.
"Wayyayi duka na za ta yi"
"Ba zata miki komai ba" ya jaddada mata.
"Toh ka ce wayyayi" ta buƙata don idan ya rantse ta san da gaske yake.
Sauƙe Sabir yayi a ƙasa sannan ya kama hannun ta suka ƙarasa wurin Auntyn, da yanzu aka saka mata stool ta zauna tana fitar da numfashin ɓacin rai, daman ƙiris take jira.
"Kiyi haƙuri aunty, don Allah"
Harara ta watsa ma Reina sannan tace wa ɗaya daga cikin masu aikin wurin su ɗauke ta suyi mata wanka.
Sai da taga sun bar kitchen ɗin kafin hankalin ta ya kwanta.
"Ki daina barin karamin abu yana ɓata miki rai a yanayin da kike ciki. Kada ki saka jinin ki ya hau" Saudat tace tana zuba ruwan da aka miƙo mata a jiki da da kuma ƙafafun ta da suka shiga fitsarin Reina.
Hawan jini na nawa kuma,Tace a ranta. kana ta saki fuska kaɗan tace.
"Ku yi haƙuri kun zo kun same mu kaca-kaca amma yanzu zamu ƙarasa tattarawa. bari a kai ku falon sama ku sha ruwa kafin a gama kimtsa nan ɗin"
"Kada ki damu wallahi , yaran zasu jira ko a waje ni sai in taya ki da wani abun"
Da faɗar haka, Yaseer ya kama hannun yaran suka fice ita kuma ta ajiye jakar ta da laidar hannun ta a ƙasa alamun ta shirya ma aiki.
Yanzu kam sosai Hajiya Fauziyya ta saki fuska don ɓacin ranta ya fara washewa.
"Gamu da yawa umman Yaseer sai kin wahalar da kan ki?"
Ƙarasawa jikin cake ɗin Saudat tayi tana kallo "da kan ki kike yin cake ɗin kuma?"
"Eh, amma fa ba na kyauta nake musu ba, biyana suke yi" ta murmusa sannan ta ɗauƙi robar whipped cream zata mayar da shi fridge don ya ƙara kama jikin sa kafin ta ƙarasa.
Saudat ta hango wasu guda biyu da tayi su tun jiya a cikin fridge ɗin.
"Ah ashe fa kin iya aunty!"
"Ƙaraso ki gani" tace da ita tana wangale mata ƙofofin fridge ɗin, Saudat ta matsa kusa tana kallo cikin burgewa. Harda wasu doli aka yi masu kyau a kan dogon, guntun kuma an cika saman shi da wafer da chocolate.
"Ina yin sana'ar gashe-gashe ai sosai tun kafin in yi aure, kuma anyi min ciniki lokacin da ake neman soyayya ta" tace tana murmushin da ta kwana biyu bata yi wanda ya fito daga ƙasan zuciyar ta kaman shi ba.
Ita shaida ne a kan soyayyar da Alhaji Tahir yayi mata, irin son da ke saka ta kokwanton ko yana cikin cikakken hankalin shi.
Amma me yasa auren shi ya fara fita a kanta cikin shekaru biyar kawai duk da irin wannan soyayyar da yake mata?.
"Ahh kice kin ja ajin ki Aunty"
Gira ɗaya ta ɗaga tana jin kanta tace "sosai ma. Tausayin sa na ji a lokacin na sauƙe farashi"
Ba yi son talaka da talauci ta sani. Ba yi iya ɓoye son zuciyar shi ta sani. Soyayyar shi ya jawo mata baƙin jini a wurin dangin sa ta sani.
Amma me yasa duka wa'innan basu zamo mata matsala a zaman ta da shi ba sai Reina? Ƴar ta na cikin ta, ba wai ƴar riƙo ko ƴar kishiya ba?.
......
A hankali yake takawa idanun shi na yaba kyau da tsaruwa irin na garden ɗin. Ga hadari da ya haɗu a sama yana bada iska mai sanyi wanda ke kaɗa ciyayi, fulawowi da bishiyoyin dake wurin suna bada wani sauti shuuu mai sanya nutsuwa a cikin kunnuwa.
Jikin lilon dake kafe a tsakiyar wurin yaje ya zauna. Ya ja kanshi baya sosai kafin ya raba ƙafar shi da ƙasa shi kuwa lilon ya fara yawo da shi a hankali, ya lumshe idanu yana jin daɗin yanayin har cikin gaɓoɓin shi.
Ihun Sabir ya riski kunnen shi kaman daga sama sai kuka kuma ya biyo baya.
Miƙewa yayi sannan ya nufi yanda yake jiyo sautin kukan da gudu, ya kai shi har ƙofar shiga main parlour na gidan, yanda ya hango Reina tsaye sanye da riga da wando kalar ruwan ɗorawa ga ƙaton cikin ta da ya bulluƙo ta cikin rigar, tana fuskantar Sabir dake zunduma ihu ga wani abu kalan kashi a fuskar shi, rigan shi kuma a jiƙe.
"Sabir! Reina! Lafiya?"
Bata firgita da ganin shi ba ko kaɗan, soyayyun idanun ta a kan Sabir ta gwada shi da ɗan tsintsiyar yatsar ta.
"Gobe ka shake taka ni shai na mammaye ka, dirty boy!"
"Reina!"
Ɗagowa tayi tana kallon shi babu ko digon tsoron da ya gani ɗazu a idanun ta.
"Me kika mishi?"
Water bottle da laidan chocolate dake hannunta ta ɗaga mishi.
"Ina wasa ne ban ssani ba na..."
"Yi shiyu!!" Ta zungure shi tana zazzare idanu. Shi kuwa ba ma iya ganin ta yake yi ba kasancewar chocolate ɗin ya fara shiga mishi idanu don haka ya rintse idanun gamm.
"Yashin kunya yayi min" ta bada amsa kai tsaye.
"Don yayi miki rashin kunya sai ki jiƙa mishi jiki ki saka mishi abu a ido?" Yace yana rage tsayin shi sannan ya cire handkerchief daga aljihun wandon shi ya shiga share ma Sabir ido.
Fauce handkerchief ɗin tayi idon ta na kawo ruwa. Sai Yaseer kawai ya tsaya kallon ƙarfin hali, ya dai samu idon Sabir ɗin ya buɗe.
Da gudu Suhail ya ƙaraso wurin su, daman tare suke a wajen ya bar shi ya shiga ciki da ya ji an saka kiɗa sai yanzu da aka sake kashewa shine ya dawo.
"Kuje jikin famfo ka wanke mishi fuska" Yaseer ya umarci Suhail da bai san mai ya faru ba tukunna amma da tuni ya kai wa Reina hannu.
Sai da suka bar wurin kafin shima Yaseer ɗin ya juya zai barta a wurin tayi saurin riƙo ƙafar wandon shi.
"Ai gidan mu yajo"
"Okay, haka kike yi ma duk wanda ya zo gidan ku? Shikkenan, ba zamu sake zuwa ba balle idan Aunty zata zane ki in ƙwace ki"
"A'a kai kajo amma ban da shi"
"Shi ba abokin ki bane? Yazo miki Birthday ne fah"
"Ni dirty boy ba aboki na bane. Umma ta ce duk dirty boy talakawa ne"
Bai san waye umman ba amma numfashi kawai ya ja tausayin ta na kama shi, saboda mutanen da ke zagaye da ita basu da hankali.
Ya sauƙa a kan guiwar shi ɗaya don ya daidaita tsayin su duk da a hakan ma yayi mata rata sosai amma ta fi Sabir tsayi.
Kafaɗun ta ya riƙe duka biyu ga hawayen rashin gaskiya dake bin fuskar ta.
"Kina so in sake dawowa?"
Gyaɗa kai tayi.
"To ki bawa abokin ki haƙuri kuma kada ki sake cewa kowa talakawa"
Maƙe kafaɗa tayi. "O'o ban bashi akuyi ba"
"To shikkenan babu ruwana da ke" zai miƙe tayi saurin riƙo hannun shi.
"Kai ka fa'a wa Aunty pleash"
"Toh idan kika bashi haƙuri ba zan faɗa mata ba."
Hannun riganta ta saka ta share idanun ta sannan cikin dakiya tace.
"Ni ban bashi akuyi ba, ai shi ya faya taka ni"
Laɓɓan bakin shi na ƙasa ya ciza kafin ya kira sunan ta "Reina. Idan aka yi miki laifi ƙara zaki na kaiwa wurin babba kin ji ko?"
Ta gyaɗa kai.
"Toh muje ki bashi haƙuri"
Ta maƙe kafaɗa.
Girgiza kai yayi cikin rasa abun yi.
Zai sake magana ta ƙwala kiran "Daddyyy" kana ta kwace jikin ta daga riƙon shi ta ruga a guje ta faɗa jikin Alhaji Tahir wanda ya buɗe mata hannayen shi.
"Sarauniya tah!" Ya shiga juyi da ita a wurin yana bin fuskar ta da sumba ita kuma sai ƙyalƙyala dariya take yi.
Sauƙe ta yayi ya buɗe bayan motar da ya dawo a cikin ta sannan ya fito mata da farin teddy bear mai riƙe da jan heart a cikin shi, a jiki an rubuta Reina @3. Ta karɓa cike da murna sannan ta rungume a ƙirjin ta tana tsalle.
"Thank you Daddy"
"You're welcome my queen"
Ya ɗauke ta da dolin da suke tsayi ɗaya yana faɗin "muje ciki kiga sauran gifts ɗin ki ko?"
"Yayyy" ta fara zillon daɗi a jikin shi kamar wacce take kan doki.