← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 57

Sashe 17

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Toh ko aron rabi ka karɓa ka fara wani abun, zan yarje maka har lokacin da Allah ya baka sai ka biya ni, dubu tamanin ne a nan kaga koma wani irin sana'a zan fara dubu 40 zai yi."

Ya girgiza kai. " Ni yunwa nake ji a taimaka a bani abinci" ya ce haka ne don kawar da zancen.

Babu musu ta miƙe ta shiga kitchen sannan ta ɗauko kular dake ɗauke da abincin nashi tare da ruwan wanke hannu.

Hannun ya fara wankewa ta kawar da ruwan kafin ya shiga cin jollof ɗin shinkafa na manja da wake.

Komawa tayi ta zauna kana ta ɗaura zancen daga inda suka tsaya. "Toh ko buhun gawayi ka siya ka fara kasawa da ɗan kayan miya, kaga Yaseer ma sai yana taya ka zaman wani lokaci, duk da akwai masu siyarwa da yawa a layin amma kowa kasuwan shi yake ci ko?"

A zafafe ya ɗago yace "Yaseer dai naji kika ce? Toh kada na ƙara ji! Kada na ƙaaara ji Saudatu!. Yaron da ya maida hankalin shi a kan karatu kike son a rabawa hankali? Ribar nawa ne zai samu a wani saida gawayi ko kayan miya da har zai fi mishi karatun shi mutunci?"

"Hmm, Abban Yaseer naga karatu babu a inda ba'a yin shi, ba sai yaje can ɗin yayi ta karatun shi ba? Wai gani nayi asirin mu ne zai rufu don abin da aka bamu ba tabbata zaiyi ba har abada. Kuma buƙatu kullum ƙaruwa suke yi, zuri'a tana ta ƙara faɗi yara suna ƙara girma"

"Rufin asiri? Akwai nufin asirin da yafi mishi karatun ne? Kina gani da yanzu ni na jure nayi karatun mai zurfi kuma ba a ƙurarren lokaci ba da yanzu muna cikin wannan wahalar ne?" Bata barshi ya dire ba ta cafe da faɗin.

"Naga dai ko karatun ne sai da kuɗi ake yinsa, Idan karatun zai yi dame zamu biya kuɗin makarantar matakin gaba? Ko shima komawa zamu yi mu sake roƙa a wurin wa'inda suka ajiye mu??"

Jan numfashi yayi yana ƙoƙarin daidaita fushin sa ganin itama ta haura. Ba zai biye mata yau maƙwafta su fara jiyo abinda ba'a taɓa ji ba a tsawon zaman su a gidan na tsawon shekaru 4, ko zasu yi rikici bata bari a jiyo muryar su don haƙura take yi bata jaa shiyasa wannan karon yayi mata uzuri.

"Ni dai na faɗa miki Yaseer sai yayi karatu har matakin PHD in dai inada rai da lafiya ta. Aikace-aikacen gidan nan ma da yake faman yi kamar mace daga yau na soke shi." Ya bangaje kwanon abincin ya faɗi tare da miƙewa tsaye, juyawar da zai yi idanun shi ya sauƙa a kan Yaseer ɗin riƙe da kunnuwan Suhail duk sun kafe su da idanu.
Ƙaramin tsaki kawai yayi ya ratsa su ya wuce ya bar gidan, su kuma jiki a saɓule suka ƙaraso ciki.

Abincin da Kamal ya zubar Yaseer ya sunkuya ya fara tattarawa kafin ya rufe kulan ya mayar kitchen. Bai cewa Saudat komai ba ya ci gaba da wankin sa yana bitar hadda ƙasa-ƙasa don ya samu Alkur'ani ya kawar mishi da damuwar da yake son shiga ciki.

Kafin dare kuwa sai ga yunwa ta sake koro Kamal ya dawo, siɗin-siɗin ya shiga kitchen ɗin ya ɗauki kular abincin da ya zubar ɗin ɗazu da ƙasa da komai haka ya zauna ya ci.

Har washegari da ta gama shirin tafiyar ta ya raka ta tasha tare da yaran yana wani ciccin magani don ta fahimci zancen da ya faɗa mata babu wasa a cikin sa.
"Muma zamu zo muyi sati guda da yaran kafin su fara jarabawar Islamiyya in yaso sai mu dawo tare"

"Toh Allah ya kawo ku lafiya" tace kafin ta faɗa bayan motar, saida ya gama cika aka mishi lodin kayayyaki kafin Yaseer yana ɗaga mata hannu Suhail na kuka har motan ta tashi.

.....

Hajiya Fauziyya ke faman kai komo tsakanin babban falourn ta da kitchen. Tana shirye cikin sabuwar maroon ɗin abayar ta ƴar egypyt wanda kalar ya dace da hasken fatar ta matuƙa.

Baki daya yau yanayin gidan daban yake, hada-hadan da ake yi a cikin ta ya ninka na kullum, kalolin abinci ake faman girkawa ana shake saman dogon dining table ɗin da shi, an share ko ina an daɗa goge shi, ƙamshin da yau yake tashi a gidan yafi na kullum.

Agogon hannunta ta duba bayan ta ajiye tray ɗin coleslaw, a kowani lokaci baƙin zasu Iya shigowa, don an ɗauki fiye da awa guda da Alhaji Tahir yaje ɗauko su daga airport da kanshi. ta daɗa gyara zaman kwanukan da masu aiki suka jera sannan ta tabbatar sun tanadar da duk wani abun buƙata cikin tsari da ɗaukan ido.

Kiran shi da ya shigo wayar ta ya sanya annurin fuskar ta bayyana domin sun ƙaraso a daidai komi ya gama kammala, ɗaki ta koma ta ɗauko mayafin kayan ta yane kanta tare da dan gyara fuskar ta da soson powder kafin ta fito cikin takun ta na manyan mata zuwa farfajiyar gidan a lokacin da baƙi da farin motoci suka yi parking a ƙofar shiga.

Alhaji Tahir ne ya fara fitowa daga cikin baƙar bayan an bude mishi, Fauziyya ta ƙarasa kusa da faran lokacin da aka buɗe ƴar yarinya ta fito sanye da riga da wando kanta da kitson da aka zubo da na gaban a kan fuskar ta.

Suna haɗa idanu da Fauziyya tayi kanta da gudu tana "Oyoyo Aunty" lokacin da dattijuwar mata ta ƙarasa fitowa daga motar tare da mai gidan ta.

Da mamaki amma cike da jin daɗi Hajiya Fauziyya ta rungume yarinyar don ba wai sun taɓa haɗuwa bane kwata-kwata tun da aka haife ta sai a wannan karon mahaifin ta ya yarda aka zo da ita Nigeria amma yanda ta sake da ita yayi mata daɗi.

A hankali ta sauƙe ta tana gyara mata kitson dake rufe mata idanu gashi yasha beads masu kyau.
"My daughter yaya sunan ki?"

"My name is Aicha Abdou Hamissou" tace tana duban mahaifiyar ta domin ta tabbatar mata daidai tayi, itama cikin jin daɗi ta ɗaga mata kai alamun tayi daidai, sannan ta maido da duban ta wurin Fauziyyar.

"Aunty ance kin haifa mana baby. Ina yake?" Tace tana leƙa bayan Fauziyyar kaman babyn takowa zaiyi da ƙafar shi ya fito.

"Ina taje dai ko Aisha?"

Girgiza kai tayi beads ɗinta na ƙara "uhm- uhm. Aicha ba Aisha ba"

Mahaifiyar ta tayi dariya kana tace "Ai duk abu ɗaya ne Darling"

"Toh ina babyn? Where is my brother?" Wannan karon bata jira amsar ta ba tayi cikin gidan a guje.

A kunyace Hajiya Fauziyya tace "kuyi haƙuri Ina ta fama da ɗiya ta na barku a tsaye, Bismillah mu shiga"

Alhaji Tahir da mijin matar ne suka fara shigewa ciki kafin ita kuma ta ƙaraso ta rungume Hajiya Fauziyya ba tare da tayi tsammani ba. "Sai yau Allah ya haɗa fuskokin mu my dear. Mun sha ganin wace irin mace Alaji Tahir zai dirje ya zaɓo ashe baiyi rawan ido a banza ba"

Ta sake rungume Hajiya Fauziyya dake murmushin jin daɗi lokaci ɗaya matar da ƴarta sun shige cikin ranta. Ba a banza Alhaji Tahir ke yabon mijin ta ba baki daya familyn su abin sha'awa ne.

Hannun su cikin na juna suka shiga ciki mazajen har sun riga da sun sama wa kansu matsuguni sun shiga gaisawa da hirar duniya. Sai ga Aicha ta fito daga kitchen tana bin duk wani ƙofa ɗaya bayan ɗaya tana dubawa.

"Me kike nima please?" Mahaifiyarta ta ƙarasa ta riƙo ta.

"Aunty Ina babyn ban ganshi ba?" Tace idanun ta na kawo ruwa.

Upstairs Fauziyya ta haura zuwa ainihin bedroom ɗinta da jego ya saka ta barin shi, babu daɗewa ta sauƙo riƙe da Reina cikin purple baby towel mai laushi ta ƙaraso wurin da su Aicha yanzu suke zaune tare da iyayen ta, kana ta zauna itama tace "gashi zo ki karbe ta"

Cike da zumuɗi ta ƙarasa jikin babyn tana leƙa fuskar ta saidai ganin ɗan kunnen dake kunnen ta da kuma kalar kayan jikin ta yasa ta fara baya-baya a hankali sannan ta saka kuka.

......

*A wannan gaɓa bayan uban Sarauniya wa ke sonta don Allah Please? Har ta kaiga idan an kalli fuskar ta ayi kuka? 😂*

*So far labarin wani gida yafi muku daɗi? Na su Saudatu ko Fauzah ko kuma duka?.*

*Saliha Ahmad Na'ibi ✨*

*REINA 💍*

Saliha Ahmad Na'ibi.

13...... Da mamaki Fauziyya ke kallon yarinyar da ke kuka har da bubbuga ƙafa ta koma wurin mahaifiyar ta.
"mummy ce na ki kai baby boy ne?"

Gwada kanta tayi tana mamakin lokacin da suka yi hakan "Kada ki min ƙazafi Please. Ce na nai an haifi baby amma ban ce boy ne ba"

"Toh a mayar da ita a karɓo min boy please, baby brother ina so" tace tana share hawayen sakalcin da ya fara bin kuncin ta.

Riƙo ta Hajiya Fauziyya tayi ta jawo ta a hankali ta dawo kusa da su sannan tace "wannan sister ɗin ki ce, zata kula da ke idan ta girma idan kina mata kirki"

Fuskar ta dai a haɗe tana yiwa Reina dake barci kallon tara saura kwata.

"Haba Nana, yaya kike mata kallo kamar kishiyar ki na?"

Bata san me kalmar kishiyar ke nufi ba amman sai ta samu kanta da daɗa yamutse fuska, wannan karon wurin mahaifinta ta nufa tana ƙunƙunin "Ni dai bani son ta"

Haka har aka sake sabunta gaisuwa, aka gabatar da kai ma Fauziyya da bata gama sanin su ba, da tambayar gajiyar hanya, Aicha na maƙale jikin ubanta.
Da aka zo cin abinci ma sai wurin nanny Fauziyya ta mayar da Reina don firr Aicha ta ƙi zuwa kusa da dining table ɗin.
Chapter 17 · 0% Book details