← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 57

Sashe 13

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A take matan suka sake guɗa ganin girman ragon, "ahh wannan jariri yayi goshi, Tahiru yayi abun kai" aka shiga yaba ƙoƙarin shi, daman sun san tunda kamal ya dawo jikin su shikkenan kayan shi ya tsinke a bakin kaba, zasu ɗauke masa nauyin komai.

Guɗar tasu ya jawo hankalin goggo ta fito tana gyara ɗaurin ɗankwalin kana ta tambayi ba'asi, baki ɗaya zufa take da warin hayaƙi don yanzu ta gama fifitan itace a cikin rana ta samu ya kama mata sannan ta daura tafashen kayan miyan da aka markaɗo.

Bayanin da ya musu shi ya nanata mata,
Bata ɓata lokaci ba tace "Toh ka maida mishi kayan shi kace ba'a so an gode" wato da ya gama mata rashin kunya shine zai danne ta da wannan yanda gobe idan wani abun ya sake tashi ya samu na musu gori ko?.

"Haba halime? Yaushe maida hannun kyauta baya ya dawo abun yi?" Danejo ta buƙata da mamakin faɗin rai irin na talaka.

"Idan kyautar ba da zuciya ɗaya aka yi maka ba ƙwarai maida shi abun yi ne" ta ɗaga hannu ma drivern tana ƙarawa da "ɗan jira ni ina zuwa" sannan ta kutsa tsakanin su ta shiga ciki tana jin ƙananun maganar su na tashi.

Ɗakin da Saudat ke ciki ta shiga sannan ta ɗauko kwanon samira a cikin kwaba ta ciro purse ɗin ta daga ciki.
Kuɗin ciki ta ƙirga Naira dubu ashirin da bakwai ne ya rage a cikin gudumawan da mutanen jama'are suka yiwa mai jego, bayan ƴan saye sayen suna da suka yi. ta cire bakwai ɗin ta mayar cikin purse kana ta maida samirar wurin da ta ɗauko shi sannan ta dunƙule Ashirin ɗin cikin tafin hannun ta, juyawar da zata yi taga idanun Saudat a kan ta, kallon ta take yi amma ba kallon tuhuma ba, sai dai kallo irin na buƙatar sanin mai yake faruwa kuma ba zata iya tambaya ba.
"Idan Kamalu ya shigo ki faɗa mishi na maida ma alhaji Tahir kuɗin shi"

Da "toh goggo" ta amsa sannan goggon ta fice, a wurin da ta bar driver ta dawo ta same shi, ta kamo hannun shi cikin nata sannan ta dunƙula mishi kuɗin a cikin tafin hannun shi. "Gashi, daman na rasa yanda zanyi in maida masa kayan sa don bani son komawa cikin gidan. Toh kace mishi ga kuɗin da ya bawa Kamalu aro na dawo mishi da kayan shi"

Zaiyi magana tace "babu ruwan ka, bani son kaɗifiri, ba ɗan aika bane kai? Don haka yi abinda aka aike ka kawai" da haka tayi komawar ta ciki don duba tumatirin ta, tana jin yanda suka fara tuhumar ta abin da tayi bai dace ba amma ta share su, tana da tabbacin babu mai fahimtar ta a cikin su koda tayi musu bayanin abinda take karewa. wato mutuncin ta da na zuri'ar ta.

Haka suka ja rago har bakin titi suka ɗaura a ƙurƙurar da suka zo da ita sannan suka koma gidan Alhaji Tahir.
Driver ne ya shiga ciki ya danna doorbell sannan Aina'u ta buɗe ta bashi daman shigewa parlour ya jira Hajiya.

Ba'a fi mintuna goma ba Hajiya Fauziyya ta fito riƙe da Reina wanda yanzu rikicin tan da sauƙi.
"Malam Adamu kun kai aikan?" Ta buƙata bayan sun gaisa.

"Wallahi Hajiya wata tsohuwa tace sai dai mu dawo da shi, kalaman da tayi ma basu da daɗin maimaitawa, harda kuɗi ta bayar wai kuɗin da Alhaji ya bawa Kamalu aro ne ta dawo da shi"

"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, yanzu ina ragon?"

"Yana mota a waje"

"Shikkenan barin turo wani ku koma"

"Sun ƙi karɓa fa Hajiya, harda maganar banza"

"Za'a basu haƙuri, har su karɓa in sha Allah".

Ta miƙe ta koma ƙaramin parlourn ta na ƙasa yanda ƴan uwan ta mata ke baje suna kallo, baki ɗayan su yau suka zo mata wuni.

Tana shiga autar su Sajida ta karɓi Reina daman saboda za'a bada nono ta bada ita. "Yaya Aina don Allah ki min wani taimako mana" nan ta zayyane mata halin da ake ciki.
"Dan Allah kada ku bar gidan sai sun haƙura sun karɓa, kice na ce idan suka sake juyo da ku zan fito in kawo musu da kaina"

Taɓe baki Zeenat tayi tace "kema dai shiga ukun ki yana niman yafi ƙarfin ki, tunda sun ce basu so ba shikkenan ba? Ko ana kyauta dole?"

"Ana yi mana, tun da muma anyi mana kuma mun karɓa"
Sake taɓe bakin tayi ta maida hankalin ta kan tv don bata da cewa.

Kafin Aina ta mayar da ɗankwali da gyalen ta Fauziyya ta shiga ɗaki ta fito hannun ta riƙe da bundle ɗin sabbin naira dubu-dubu da babban laidar Diapers, wipes, sai set na kayan shafan yara ta bata. "Kice ga nawa gudumawar don Allah suyi haƙuri su karɓa kuma ina basu haƙuri da abinda ya faru, ki danne mun su yaya Aina"

"Toh Amma kuɗin nan baiyi yawa ba fauzee? Ina laifin dubu hamsin? Koma Ashirin tunda ga niƙi-niƙin kaya?"

Murmushi Hajiya Fauziyya tayi tace "da na baki kaman haka na siyan jaka da takalmi ai da kin bani canji tunda na san akwai sosai ma".

Kama bakin ta tayi ta miƙe haɗe da rataye jaka sannan tayi musu sallama ta fice.

Firr Aina tace ba zata shiga ƙurƙura ba don haka suka ɗauki motar Hajiya Fauziyya motar rago na biye da su har unguwar su kamal. Da sallamar ta ta shiga gidan da ake ta faman hada-hada ta samu Huwaila da amarya suka bata hankalin su.
"Don Allah mai jego nake nima"

Suka yi mata iso cikin uwar ɗakin Saudat aka bata bakin gado ta zauna sannan suma suka nemi wuri suka zauna a maimakon su basu wuri sannan aka shiga gaisuwa.

"Amma ban wayi fuskar ba" Saudat tace cikin jin nauyi.

"Allah sarki. Yayar Fauziyya ce ni"

"Fauziyya Fauziyya?" Saudat tace tana son ɗago sunan.

"Hajiya Fauziyya matar Alhaji Tahir dai"

"Ayyah Aunty ba? Tana lafiya? Yaya jaririya?" Ita ba zata ma iya tuna inkiyar Reina ba, kuma tasan sunan wata mai muhimmanci aka mayar mata balle tace Hafusatun.

"Suna nan Lafiya alhamdulillah. Daman shine ma suka turo ni bin sawu da bada haƙuri"

"Ni babu wanda yayi min komai Wallahi, daman goggo ne da abban su, bari a kira miki goggon kada mu ari bakin ta aci mata albasa"

Huwaila da kanta ta fita kiran goggo kuma tun daga wajen ta fara mata bayanin abinda yake faruwa don haka fuska a tamke ta shigo ɗakin ta zauna Aina ta gaida ta.

"Daga ina baiwar Allah?" Goggo ta sake tambaya don bata damar maimaita ƙudirin ta.

"Ƴar uwar Fauziyya ce ni matar Alhaji Tahir, saƙon ban haƙuri ta turo ni da shi Mama, don Allah kuyi haƙuri kada ku maida hannun kyauta baya"

"Kuna ta zancen maida hannun kyauta, shin kun duba kyan shi hannun da ya miƙo kyautar? Kun duba fuskar da ya bayar da ita?"

"Sai an san anyi wa mutum ba daidai ba ake bashi haƙuri mama, don haka anyi miki laifi amma kiyi haƙuri, tace kuyi haƙuri da abinda ya faru " sannan ta luma hannu cikin jakar ta zaro bundle ɗin da ta zare dubu goma a ciki tun a hanya ta miƙa mata "dan Allah ki karɓa goggo ba don halin mu ba, tace idan baki karɓa ba da kanta zata fito ta kawo miki"

"Lalala raba ni da fito da mai ɗanyen jego haka kawai, kuma ma ita Fauziyya ai ko dan halinta tace in karɓa zan karɓa amma ko Kamalu uban Tahir bai isa ya wulaƙanta ni ba balle shi ɗan ciki na, shi Tahir ɗin ya san da haka"

"Kina da gaskiya Wallahi Mama, kuma shima ya gane kuskuren shi ya bada haƙuri, sunce ma ko kwana zanyi a gidan nan idan baki karɓa ba kada in dawo, to ga ƴan marayu kuma a gidan suna zaman jira kada a ɗauki hakkin su."

Hannu goggo ta saka ta karɓi kuɗin tana faɗin "toh shikkenan", na haƙura na karɓa zaki iya tafiya.
Godiya tayi ta miƙe tana faɗin "toh bari a shigo da sauran"

"A'a harda wasu saura?" Amarya ta washe baki jin zancen arziƙi.

"Eh akwai rago da kuma kaya a mota, zamu je da yara su ɗauko.

"Ai bama sai anje da yara ba muje in taya ki ƴar nan"

Suka fita suka bada izinin a shigo da ragon a ɗaure shi a cunkusasshen tsakar gidan sannan Aina ta miƙa ma huwaila laidar pampers da wipes kayan shafar kuwa ta ɓoye su a ƙasan seat.

"Wannan ƙunzugu ai sai a shekara ma yaron bai gama sakawa ba" ta ɗaura da guɗa sannan ta shiga gidan tana shelar abinda aka kawo din harda kudin.
"Yaro ya samu jibgegegen rago, ƙunzugun shekara da ɗori, abin goge kashi har pakiti biyu da kuma gudmawar kudi Naira na dukan naira har dubu Ɗari, daga uban shi Alhaji Tahiru da Uwar gidan shi Hajiya Fauziyya. Don Allah ku taya ni bani da hanci"

Kowa ta kame hanci suka ɗauki kuwwar "Ayyiririiii...."

......

*Wattpad users Please a taimaki Seemahwrites ta cika followers dubu guda🙈 ina godiya wa duk wacce ta ɗauki lokacin ta wajen danna follow button💗*

*Masu karatun English Novels albishirin ku💃🏼💃🏼 Ayyiririiii ba guɗan haihuwa bane😂 Recent English novel ɗina mai taken THE BLEEDING ROSE 🌹 ya samu kammaluwa an haɗe shi document full in full kuma zaku same shi a kan Naira 500 kacal. Ga masu son ɗanɗano ku duba profile ɗina na wattpad zaku sami free pages. Ina faɗa muku labarin akwai tsayawa a rai, sai wanda ya karanta yaji✨. Ga mai buƙata ya tuntuɓe ni a wannan lambar 08021689184.*

*REINA 💍*

10.... Har driver sun ɗauki hanya ya tuna bai bada dubu Ashirin ɗin da goggo ta bashi ya maidawa Alhaji Tahir ba. kaman zai riƙe yayi tafiyar shi tunda sun kawo musu abin da ya ninninka hakan sai yayi tunanin Idan shi bai ƙara ma mutanen da suke rayuwa cikin irin wannan unguwan ba a kufayin gida toh bai kamata ya rage su ba, sa'annan ko ba daɗe ko ba jima zance zai iya dawowa kunnen Hajiya Fauziyya ko Alhaji Tahir.
Chapter 13 · 0% Book details