Sashe 40
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Nima ina da abun daɗi idan kina so" cewar Jamal cikin sigar ruɗin ta kaman yanda ya saba amma Yaseer bai kawo komai ba domin har yanzu mamakin ta bai sake shi ba.
Maƙe kafaɗa tayi "O'o ni na Yaseer nake so"
"Shikkenan ki je kiyi wasa zan kawo miki" yace da ita don ya daina ganin ta a gaban shi.
"Yayyy" da gudu ta koma wurin yaran da suka baza abin wasa tana murna, Yaseer kuwa kaman ruwa ya cinye shi.
Haka suka cigaba da zaman shiru, Jamal na ta browsing ɗin classwork ɗin a waya ƙarshe ma sai ya koma chatting kawai ganin Yaseer ya zurfafa cikin tunani.
Bai tashi dawowa cikin hayyacin shi ba sai da muryar ta ya shiga cikin kunnen shi tana cewa "nine mummy, nine mummy! ni zan bawa Junior nono tunda shine ɗa na, idan ya sha sai in bawa Zahira ma, Abdallah kuma shine Daddy, zamu shiga ɗakinmu mu kwana tare a gadon mu...." Haka ta ci gaba da tsara musu yanda wasan zai kasance.
*Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites ✨)*
*REINA 💍*
28......A hargitse Yaseer ya miƙe ya juya yana fuskantar yanda suke zaune suna sauraron huɗuban Reina.
Cikin ƙaraji yace "Hafsah!!!"
Har Jamal saida ya firgita domin yau ne karo na farko da ya taɓa jin Yaseer ya ɗaga murya.
Juyowa duka suka yi suna kallon shi banda ita hajiyar domin ta san abinda tayi ba dai-dai ba, bata yi tunanin zai iya jiyo ta ba.
"Baki ji na kira ki bane?" Ya tambaya cikin kausasshiyar murya.
Ɗagowa tayi muryar ta na rawa tace "Na... Na'am"
"Sai na ce kizo?"
Jiki a sanyaye ta miƙe ta zaga mashigar rumfar sannan ta taka matakalar ƙafar ta na rawa ta ƙarasa wurin shi idanun ta a ƙasa.
"Ka bita a hankali mana" cewar Jamal ganin yanda gabaki ɗaya ta firgice sai jikin shi yake bashi a cikin wannan yanayin zata iya fallasa abinda ke tsakanin su ma Yaseer idan ya buƙata.
Banza yayi da shi yace "Maimaita abin da naji kina faɗa"
Haɗiyan miyau tayi kafin tace "wasan Mummy da Daddy ne zamu yi"
"Wani irin wasa ne haka?"
Ɗagowa tayi a hankali, amma yin arba da ɓacin ran dake kan fuskar shi yasa tayi saurin sadda kanta ƙasa "kayi haƙuri Yaseer, ba zan sake ba" kalmar haƙurin kawai zamowa yayi daga harshen ta ba tare da ta sani ba saboda bata saba da amfani da shi ba.
Laɓɓen bakin shi ya tauna yana ƙoƙarin dakatar da kanshi ya ɗauke idanun shi a kan koma menene zatayi, amma sai yaji ya kasa.
"Get on your knees"
"Iye?!" Jamal yace cikin kaɗuwa. Ita kuwa hawaye ne suka shiga wanke mata fuska yayin da a hankali ta zuba a kan guiwowin ta.
Ganin haka ya saka sauran yaran suka tattari komatsan su zasu gudu. Da hannu kawai ya yafato su suka dawo don tunda ya iya saka Reina kneel down toh fa no nonsense ne.
"Miƙe bayan ki, ki ɗaga hannu sama kuma ki rufe ido"
Sheshsheƙar kuka take yi a fili yanzu amma bai hana ta yin kaman yanda yace ba, suma sauran ukun da ƙarasowar su suka yi niyyar yin kaman yanda tayi amma sai ya dakatar da su tunda su bai ji maganar banza a bakin su ba, ba zai bari laifin ta ya shafe su ba don haka yace su nemi wuri su zauna sannan ya shiga duba shirmen Jamal ya barta a wurin.
Minti goma kacal amma jikin ta gabaki ɗaya rawa yake yi, hawaye da zufa sun wanke mata fuska babu abinda bakin ta yake maimaitawa sai kalmar haƙuri.
Tausayi ta bashi yace ta miƙe ta buɗe idon ta.
Zaman dirshan tayi mishi a wurin tana maida numfashi idanun ta a cikin nashi. Lokaci ɗaya sai fushin ya yaye tausayin ta ya maye gurbin shi.
"Ajin ki nawa a islamiyya?" Ya ajiye ainihin tambayar da yake son mata a gefe domin bayi da amfani tunda ba komai zai iya yi a kai ba.
"Ajin farko" tace don har ga Allah bata san ma mai ake cewa ajin ba tunda ba damuwar ta bane.
"A wani Surah kike?"
"Wal Aadiyaati dabhan ne"
"Karanta min in ji"
Babu Bismillah ta fara karatun aya uku tayi ta fara kame-kame.
"Karanta min Suratul takaathur toh"
Rau-rau tayi da farin idanun ta da hawaye suke kwance a cikin su cike da tsoro tace "wanne ne kuma shi?"
"Alhaakumuttakasur toh"
"Oh, na manta shi Allah"
Dogon numfashi ya shaƙa ya fesar domin kada ya sake hasala yace "Al-qaari'a kam kin san shi ko?"
Gyaɗa kai tayi "Eh"
"Toh idan baki karanta min Al-qaari'a har ƙarshe ba sai na zane ki. Kuma kiyi Bismillah kafin ki fara"
Zata cigaba da kuka ya daka mata tsawa a dole ta haɗiye shi ta fara karatun, burinta bai wuce wani ya fito daga cikin gidan ya cece ta ba amma har tayi nisa da karatun babu wanda ya fito. duk inda tayi kuskure sai ya gyara mata ko idan ta kakare ya ɗago ta har saida ta karance suran tsaff.
Dakatawa yayi domin ta maida nutsuwar ta, ya koma kan sauran yaran ma da tambayoyi.
Kaman yanda yayi tsammani suma ba wani abun arziki suka iya ba domin cikin su babu wanda ya wuce izu biyu amma dai sun fita kuma ita ce babba.
Ya haɗa su duka ya tambaye su adduo'in da ya kamata yara irin su ace sun riƙe irin su na shiga ban ɗaki da su kwanciya barci da sauran su, a nan kam ta bashi mamaki domin da daɗi da babu daɗi Hajiya Fauziyya ta dage ta koya mata, sanin muhimmancin su.
Su hadisai, ƙawa'idi da ahlari kan ma ba'a magana bata ma taba yin su ba sai dai wanda ta tsinta a bakin Aunty.
Don haka ya maida akalar tambayoyin shi zuwa fannin boko.
Shikam sauran yaran sun yi zarra, itama babu laifi don yanzu tana primary 4 amma shima babu abinda ta iya domin kuɗin ubanta yasa take hayewa amma da ta sha repeating.
Har lokacin su da Jamal na karatun safe ya ƙare amma yana zaune dukda Yaseer ɗin ya sallame shi, domin har yanzu bai gama nutsuwa de Reina ba zata fallasa shi ba.
Yaseer da a yanzu ya karyo reshen bishiya a matsayin bulala ya gwada yaran da shi yana faɗin "daga yau, duk ranan da wani yaro yayi fashin makaranta ɗaya ko islamiyya ko boko sai ya kwanta a nan nayi mishi bulala goma! Sannan har weekend zaku dinga zuwa islamiyya idan nazo na samu wani yaro yana wasa lokacin makaranta ko? Hmm hmm hmm!" Ya jujjuya kai irin yana tausayin sun nan, baki ɗaya ya gama tsorata su sai gyaɗa kai suke yi kaman ƙadangaru suna rantse-rantse.
"Kuyi min shiru!" Ɗiff kake ji kaman anyi ruwa an ɗauke, sai ƙifi-ƙifi kawai suke da idanu. "Kuma idan kun dawo da islamiyyan safe duk asabar da lahadi zaku zo kuna bita mun karatun ku, zan duba idan kuna class work da assignment kuma, duk wanda bai yi dai-dai ba hmm.. sorry ganda. Yanzu na baku minti goma kacal ku wuce ku ɗauko jakar makaranta mu fara extra lesson, duk wanda ya ƙara minti ɗaya bulala biyar!"
Bai rufe bakin shi ba suka ɗauki hanyar cikin gidan da mugun gudu har suna bangaje juna kuma babu daɗewa suka dawo, Hajiya Hauwa na biye dasu ganin yanda suke a kiɗime tayi tunanin wani abun ne ya faru.
Amma sai taga duk sun nemi wuri sun zauna sun fito da littafi da abun rubutu.
Gaishe ta Yaseer ya sake yi, ta amsa mishi da hannu kawai sannan tayi tsaye tana kallon gudun ruwan shi.
Ko a jikin shi cikin Muryar umarni yace "baku iya gaisuwa ba ko?"
Jiki na rawa suka miƙe "good morning sir, we are happy to see you, may god bless you sir" murmushi yaso kuɓce masa ganin Reina bata iya ba bin baki take yi amma ya fuske.
"Morning how are you"
"Fine thank you sir"
"Sit down"
Suka zauna. Har sai da ya fara musu karatu kafin Hajiya Hauwa ta koma ciki. Haka suka cigaba har saida aka kira azahar kafin ya sallame su kuma dolensu su dawo.
Don haka suna gama cin abincin rana suka sake komawa wurin, Yaseer ma ya samu a wurin masu gadi sun gayyace shi ya ci.
Don haka da ƙarfin su ya fara musu karatun Alkur'ani amma Reina tayi baya da yawa don haka dole ita yayi mata nata daban. Sai da ya gama da su ya haɗa su da aikin aji kafin yace ya matso.
Ta taso ta dawo gaban shi ya ara mata ƙur'anin sauran yaran don ita bata da shi sannan ya fara bita mata tana amsawa har saida ya tabbatar ta gaji kafin ya sallame su.
A daren Junior ya saka drama Hajiya Farida tazo ta ɗauki abinta ya rage sauran su uku kawai da zaman gidan ya zama dolen su, sai a yau Reina fara kewar auntyn ta domin da itama daddynta yazo ya ɗauke ta sun koma nasu gidan.
Tun daga wannan rana Reina ta shiga taitayin ta, kafin ace mata driver na jira har ta shirya ta fita kuma da ta dawo take fito da assignment Hajiya hauwa ta taya ta sannan ko bata yi sallan la'asar ba zata yi shirin islamiyya shima ta fita a kaita.
Wannan ya fara kawo sauyi a cikin hidimomin ta na yau da kullum, gajiyar jigilar makaranta ya saka ta fara barci da wuri kuma da ta tashi sai shiri don haka yanzu bata da lokacin game ko kallace-kallace, tsoron hukuncin Yaseer yayi mata diran mikiya a zuciya don gani take yi ma gwanda Aunty a kan shi.
Sati na zagowa kaman yanda Yaseer yayi alƙawari ya duba littattafan kowannen su, bai damu da tafiyar junior ba daman Reina itace damuwar shi, sakaya sauran kawai yayi.
Hafsatu Reina ƴar Aunty, Auntyn da tayi wa iyayen shi Rana, Auntyn da ya ɗauka wa alƙawura masu girma.
......
"Kin shirya zama ki fuskance ni Fauziyya?" Ummi ta tambaya.