Sashe 4
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Lale maraba lale, barka da zuwa sarauniyar T.K kingdom" cewar Aina'u shugaban masu aikin Hajiya Fauziyya cikin ɗaga murya tana tafa hannu cike da nishaɗi sannan ta saake sake guɗa "ayyyiiririii" tana taku da baya-baya a gaban su Alhaji Tahir da Hajiya Fauziyya dake shigowa fuskar su cike da annashuwa. "Ƴar gatan maman ta, Sarauniyar baban ta, ƴar kuɗi jikan kuɗi, walwalan talakawa, babbar mace mai ƙashin arziki, duk inda kika zauna, duk inda kika rarrafa, duk inda kika kama kika tsaya, duk inda kika taka sai ya wadata da dukiya in sha Allahu, lale maraba da matar mai tsantsan rabo..." Hannu kawai Alhaji Tahir ya luma cikin aljihu ya ɗebo abin da ya rage ba tare da ya ƙirga ba ya danƙa ma Aina'u wanda ta zube a saman guiwowin ta kafin ta amsa tana sake sakin guɗa sauran ma'aikatan suka shiga taya ta. Daga nan suka ɗunguma da mukarraban da suka biyo shi daga asibiti zuwa ɗakin da aka shirya mata a ƙasa domin Alhaji Tahir ya yanke cewa ba zata iya hawan bene zuwa ɗakin ta dake sama da ɗanyen jego ba.
Saida ya zaunar da ita a saman gadon sannan ya zauna suna fuskantar juna, kana ya buƙaci a Bashi Reina da ta fara ƴan ƙananun koke-koke saboda hayaniyar su ba zai barta ta mayar da barci ba.
Ƙura ma Reina, Jaririyar kwana biyu idanu Alhaji Tahir yayi ya dulmuya cikin tunanin da Allah kaɗai ya sani, mutanen da suka rako su kuma sun fita tanadar musu da kayan buƙata, kamar ruwan wankan jaririya da uwar ta, abinci da kuma tea mai kaurin da Fauziyya take ɗirka tun a asibiti don Tahir ya hana ta shan sirki. A bisa matsawan sa ma suka yi kwana biyu a asibiti dukda cewan dukkan su lafiyar su ƙalau amma yace a tabbatar tukunna kada sai sun koma gida wani abun ya biyo baya.
"My T" Ta kira shi, sai ya ɗago idanun shi daga kan ƴar shi ya zuba su a kan abin ƙaunar shi tare da sakar mata murmushi.
"Umm nace wani suna ka saka mata?" Ta tambaya don ta san yayi mata huɗuba yau da safen.
"Reina na saka mata"
Darawa tayi kafin tace "Reina suna ne?"
"Eh mana, ba ke kika ƙala mata ba?" Ya faɗa yana yiwa ƴarsa wasa tare da lakatar ɗan kumatun ta.
"Dan Allah da gaske nake T" ta riƙo hannun da yake wasa dashi ba tare da ta bar dariyan ba.
"Hafsatu sunan ta" yace yana kallon cikin idanun ta, abinda yayi tsammanin kuwa shi ya gani, tsananin farin ciki da jin daɗi ne ya bayyana a cikin su.
"Sunan Ummi na ka mayar T?" Ta tambaya cikin mamaki don bata yi tsammanin hakan daga gare shi ba, akwai mutane da yawa da suka cancanci a mayar da sunan su cikin familyn shi amma ya tsallake har tashi mahaifiyar da ta riga mu gidan gaskiya ya saka sunan nata.
Ya gyaɗa mata kai. Sai ta ƙara ƙarfin riƙon da tayi ma hannun shi.
"Nagode ƙwarai da gaske T. Allah ya saka maka da mafificin alkhairi ya raya mana Hafsatu Reina."
"Anything for you Habeebty" ya ɗan miƙa ya sumbace ta a kunci yayin da Reina ta callara wani ƙaran da saida ya razana, yayi saurin gyara zama yana tunanin ko ya matse mata wani ɓangare ne na jikin ta. Kuka take callarawa har tana watsa ƴan ƙiraren hannun ta sama, yayi saurin miƙa ta ma Fauziyya yana faɗin "yi sauri ki bata nono dan Allah"
Ita damuwar da ta gani a kan fuskar shi ne ya bata mamaki.
"Yanzun nan fa kafin mu baro asibiti na bata, Duk bayan minti 30 ne ake shayar da jarirai?"
"Eh mana. Ai haka abun yake, sai anyi haƙuri kuma ana haɗawa da madara kwanan nan zakiga ta cicciko"
Yamutsa fuska Fauziyya tayi bayan ta buɗe zip ɗin rigar ta, ta saka ma Reina nono a baki wanda tayi saurin cafka tana zuƙa kamar wanda ta kwana bata ci ba.
Ɗan ciza baki tayi tana mitan "Nikam wallahi na gaji, gashi bakin nonon har yanzu ciwo yake mun"
"Toh ko zamu koma asibitin ne?"
Saurin girgiza kai tayi "A'a don Allah, zai bari a hankali " ganin cewa da gaske yake yi.
Alhaji Tahir bai bar ɗakin ba har saida ungozoma ɗaya ta shigo da kayan wankan Reina ta karɓe ta don a wanke ta sannan ɗayan ta shige banɗaki tare da Fauziyya don a gasa mata jiki, ba tare da ɓata lokaci ba kuma aka fara jere mata kalolin abinci, farfesun jan nama da naman kai da kuma ruwan zafi.
.....
Dukan da Saudat ta kaiwa sauron da ya sauƙa a kan ƙafar Kamal ne ya sanya shi farkawa a gigice, kasancewar ta kai dukan har da na haushin shaƙar baccin shi da yake yi hankali a kwance bayan ita ta kasa rintsawa saboda zafi ga sauro, da kuma takuri irin na tsohon ciki.
"Lafiya Saudatu?" Ya tambaya yana murtsuka idanu saboda ya samu daman kallon ta da kyau cikin ɗan hasken tochilan da batirin shi yayi sanyi.
Bata ce mishi komai ba sai tafin hannunta da ta ɗaga mishi don yaga mataccen sauron da ya gama shan jinin su ya ƙoshi.
Sauƙe ajiyan zuciya yayi ganin tana lafiya sannan yace "yaya baki kwanta ba?"
"Ta ina zan iya barci a cikin wannan zafin ga sauro kaman zasu yanki naman mutum?!" Ta tambaya cikin faɗa-faɗa.
"Kiyi haƙuri, in sha Allah zuwa gobe zanyi ƙoƙari a haɗa wutan, kinsan register ɗin makarantar Yaseer shi yasa nayi katt har na bari nepa suka yanke wutan Amma gobe zanje in samu Alhaji Tahir"
Tsaki taja kawai ta juya tana mita sai ya ɗauki mafifici ya fara mata fifita nan da nan barci ya fara awon gaba da ita amma sai bugu suka ji ƙaɗan-ƙadan a ƙofa.
A ɗarare Kamal ya tashi ya ƙarasa jikin ƙofar yana tambayar waye ne? Bai duba lokaci ba amma yana da tabbacin dare ya raba.
Saudat ma sake tashi tayi ta zauna ta zuba ma ƙofar idanu.
"Abba Suhail ne ya gagara bacci" cewar Yaseer cikin ƙasa da murya.
Cire sakatan jikin ƙofar yayi ya buɗe ta sannan yaran suka shigo ciki ya mayar ya rufe.
Riƙo hannun Suhail yayi yana tambayar abin da ya hana shi barci.
"Abba zafii" yaron yace cikin muryar kuka ga ƙurajen zafin da suka mamaye kirjin shi, wuyan shi, da goshin shi. Daɗin abun ma su suna da gidan sauro da abin yayi musu biyu.
"Je ku kwanta in fifita ku"
Da sauri Suhail yaje ya ɗale katifan ya shige jikin mahaifiyar shi daman a can ɗan ɗakin su mai kaman store shimfiɗi suke yi a ƙasa su kwanta, Yaseer ma ya kwanta gefen mahaifin shi sannan shi kuma yayi zaman musu fifita har barcin su yayi nisa yana kai, sai ya shiga nanata istigfari da salatin annabi a kan harshen shi.
Sai wuraren asuba gajiya da kuma tsamin da hannun yayi mishi ya sanya ya haƙura ya kwanta amma Saudat bata yi saken barin shi ya makara sallar asuba ba.
Suna dawowa daga masallaci shi da Yaseer yayi ma Saudat sallama Sannan ya wuce kasuwar muda lawal don taya masu motar kaya sauƙe kayan gwari don a samu na sawa a bakin salati mai daɗi. Yaseer ma bokiti ya ɗauka ya fita ɗibo musu ruwa, sanda yayi sawu wurin goma lokacin rana ta fara zafi kafin ya karɓi Naira ɗari huɗu wurin Saudat ya shiga maƙwafta siyo musu gawayi na Naira ɗari da kuma ƙullin manja na ɗari uku.
Yana dawowa ya juye gawayin cikin murƙubur sannan ya nemi takarda ya saka mishi wuta. Har sanda wutan ya kama sosai kafin ya saka ruwa a madaidaiciyar tukunya ya ɗaura a kai, ya shiga sharan ɗakuna da tsakar gidan ya lailaye shi tass. nan ya jawo Suhail zuwa banɗaki ya cuɗe shi kafin shima ya shiga wankan. Ya ɗau lokaci yana tsaftace duk wata kafa na jikin shi kafin ya fito sanye da gajeren wando ɗan siririn ƙirjin shi na ɗigan ruwa, lokacin har ruwan da ya ɗaura ya tafasa Saudat ta saka taliya laida ɗaya ya nuna tana tsiyayewa cikin colander.
Da shigar shi ɗaki ya goge hammatan shi da alimun ya saka singlet sannan ya sanya jan riga da wandon jeans ya fesa turaren shi wanda bayi wuce ɗari takwas zuwa dubu ɗaya sannan ya taje gashin kanshi ya fito zuwa kitchen ya ɗauki plate ɗin taliyar shi da manja da yajin da yasha tafarnuwa da farin maggi ya saka cokali mai yatsu ya fara ci cikin nutsuwa.
"Yanzu yaushe zaka dawo kayi shirin Hadda?" Saudat ta tambaya tana daga ƙasar bishiyar neem dake samar da inuwa a tsakar gidan ta shimfida tabarma tana shan hantsi.
"Umma nayi tsammanin za'a bari sai na haɗa kuɗin uniform tukunna" ya amsa yana kai kofin ruwa bakin shi.
"A'a niman kuɗi ba zai hana ka karatun addini ba Yaseer, Yana nufin munfi bawa bokon muhimmanci kenan. kuma ma abban ka yace yau zaije ya kawo in sha Allah"
"Hmm" kawai Yaseer yace kasancewar ya sanar da shi a ina zaije ya kawon. Wurin da akwai ɗin amma samu da wuya da wulaƙanci sannan a baka abin da be kai ya kawo ba, in ta tashi ne da sun ci gaba da fafutukar su ne kawai Allah zai basu a lokacin da ya ga dama.
Suhail ne ya fito daga uwar ɗakin iyayen sanye da wandon uniform army green da rigan shi green check saidai ya saka rigan a baibai.
"Umma ina sandal ɗina?" Ya tambayi Saudat.
Yafato shi tayi da hannu ya ƙarasa kusa da ita ta kwaɓe masa rigan da hannun ta ɗaya da juya shi don ɗayan hannun manjan taliyar da take ci ya ɓata shi sannan Suhail ya sakalo wuyar shi ta taimaka mishi ya saka a dai-dai.
Zuwa lokacin har Yaseer yaje ya ɗauko masa sandal, Suhail ya dafa kanshi dake yana durƙushe sannan ya saka mishi ba'a batun socks dama. zuwa lokacin abokan tafiyan shi sun shigo da ƴar sallamar su.