← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 57

Sashe 32

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yarinyar da idan miƙo kaza aka ce mata sai ta kawo maka uzuri guda hamsin kuma idan ba da jan ido ba bazata miƙo ba.

Reina bata aikuwa bata aikatuwa, saidai idan buƙatar tata ce, toh fa nan kam bata da nauyin jiki.

Domin yanzun ma makaranta ta ki zuwa firr wai ƙafafun ta na ciwo kuma uban ta ya biye mata. Ƙafar da har India suka je, suka shafe tsawon lokaci a can, aka yi mata aiki sosai saboda kada idan ya gama warkewa ya bar tabo da yawa.

An ƙarashe third term lokacin tana tsaka mai wuya amma haka aka cinye sabon first term da second term har wani third term ɗin ya sake zagowa ana shirin exams bai fi na sati biyu taje school ba a cikin shekara guda. Islamiyya kan ma ba'a magana daman bata shiga da wuri ba gashi ya hana a taɓa ta don haka babu abinda ta iya bayan fatiha da ƙulaƙuzai, shima Ita ta kai zuciya nesa ta koya mata.

Shine fa mai ciwon ƙafa taji ana zancen za'a yi waffles ta baje a kan kitchen Island tana buga buttern nan da sugar kaman Allah ne ya aiko ta, sai Maama ta koma kallon ta kawai tana shiru.

"Ki sauƙa ki wanke hannun ki zamu yi tafiya da Daddy" Fauziyya tace don bata son doguwar magana saboda saƙon mutuwar da ta samu.

Da murna ta dangwara ma Maama bowl din sannan ta taka kujera ta sauƙa don ta san duk inda za'a je da Daddy toh fa jin daɗi ne.

"Aina'u dan Allah bita ki haɗa musu kayan su kala ɗaya ko biyu"

"Toh Aunty" Aina'un ta amsa.

Har ta juya zata tafi ta kira ta "ba masu ado sosai ba, ɗan na canzawa kawai"

Nan ma da toh ta amsa sannan ta tasa ƙeyar Reina zuwa ɗakin kwanan su ita da Maama, ta ɗauko ƴar madaidaiciyar traveling bag ta shiga zaɓar kayan.

Karan tsaye Reina tayi mata, ita sai wanda take so za'a saka daga cikin jerin gowns ɗin ta kuma.

Share ta kawai Aina'u tayi ta ci gaba da aikin ta. Sai kawai ta saka mata rikici tana jawo gogaggun kayan dake ninke tana fatali da su a tsakar ɗakin.

"Hajiya ƙarama dan Allah ki bari!" Tace cikin ƙosawa kaman zata yi kuka sannan ta fara maida kayan bayan ta barta ta zaɓi wanda take so ɗin an haɗa a kan wanda ya kamata.

Handkerchief ne ya faɗo, Aina'u ta ɗauka zata mayar Reina tayi saurin faucewa daga hannun ta. Ta tuna da mai ita, kuma tun wancan Ranar Aunty take ajiye da shi a kan idan sun sake zuwa za'a maida mishi kayan shi.

Cikin jakar kayan sun ta cusa, da nufin idan sun fita sai tace ma Daddyn ta su je gidansu su mayar mishi.

....

Da wayan Saudat yake magana da abokin shi wanda suka yi paper tare sannan shima yaci Jamb da waec wanda sakamakon su sun daɗe da fitowa har an fara sake sakamakon neco ma.

Kuma tare suka je suka yi physical screening a Atbu tunda zancen University of Ibadan ya gagara.

Kamal ya buga ya buga amma abun yafi ƙarfin shi, don haka da yaga babu sarki sai Allah shine ya shafa ma kan shi ruwan sanyi ya bar komai a hannun rabbana, gwanda ma Yaseer ɗin ya zauna a kusa a gaban idanun su yayi karatun zai fi musu kwanciyar hankali.

Ta ɗaya layin aka ce da shi.
"Yanzu na gani kaima ka duba."

"Na taya ka murna Muhammad, zan duba nima yanzu in kira ka"

Da wannan suka gama kiran ya ajiye ma Umman wayan ta sannan ya fito ya same ta a kitchen ya sanar da ita zai je cafe ɗin da aka buɗe mishi e-mail a duba ko an turo mishi da admission letter.

Ɗari biyar ta bashi, ya canza takalmi daga silifas ɗin ƙafar shi zuwa wani kana ya fice.

Ya ɗauki kaman mintuna 40 kafin ya dawo riƙe da takardu guda biyu a hannun shi, ƙolla cike a idanun shi.

"Umma gashi sun turo min, sun amshe ni a matsayin ɗalibin su umma kuma sun bani course ɗin da nake so"

Da murna ta miƙe ta tunkaro shi, yana tsaye a wurin ya gagara motsawa don haka ta amshi takardar da ɗan guntun turancin ta dai ta duba.

"Masha Allah, alhamdulillah!" Addu'a tayi mishi sosai tana saka mishi albarka sannan tace yaje ya gwada ma su danejo da gidan Liman, don ko yaushe tambayar su kenan a kan makarantar tashi.

"Toh ki riƙe min wannan umma sai inje in gwada musu ɗayan"

Ya bata ɗaya takardan dake hannun shi.

"Wannan kuma na menene?" Ta tambaya tana dubawa ko shima zata gane.

"Bayanin registration ne a jiki da kuma kuɗin da za'a biya"

"Kuma har nawa?" Ta buƙata.

Dubawa yayi daga kuɗin makaranta, hostel da sauran su.

Sai ya kalle ta. "Umma da yawa fa"

Karɓan takardan kawai tayi tana ƙirga yawan zeros ɗin dake jikin total.

"Miliyan ɗaya nake gani haka ko nawa?" Tace cikin tsananin kaɗuwa.

Ya karɓe takardan don sake tabbatarwa kana ya saki murmushi "Haba miliyan? Dubu ɗari ne da sha takwas amma banda kuɗin su hostel da wasu abubuwan"

Jinjina kai tayi, In sha Allah ba zai gagara ba tunda sun daɗe suna tarawa. Amma zancen wani hostel kam sai Kamal ya dawo sun sake shawara.

.....

Ciki Aka wuce da su Hajiya Fauziyya shi kuma Alhaji Tahir ya tsaya a waje wurin karɓan gaisuwa tare da Alaji Abdou ɗin wanda ya gama yin sukuku har magana tana niman gagaran shi a yanzu.

A yanzun da yaje ya saka Malika a rami da hannun shi mutane suka taya shi ya rufe. Ya tabbatar da cewa ya rasa ta kenan har abada, kuma shi da Aicha sunyi rashin da zai canza ƙaddarar su baki ɗaya.

Kukan ta shine abinda ya fara riskar su da shigan su parlorn. Tana yi tana kiran mummy.
maƙale take a jikin ƙanwar mahaifiyar ta wanda itama kukan take yi balle a samu ta rarrasheta, Gashi anyi a raba su abu ya gagara.

"Amma me yasa za'a faɗi mutuwa ma yarinya ƙarama haka?"

Fauziyya ta koka cikin rashin jin daɗi tana ƙoƙarin jawo Aicha jikin ta.
Ganin ita ce yasa ta yarda tazo ta kwanta luff a jikin ta.

"A gaban idanun ta Allah ya ɗauki ran ta. Allah ya jiƙan ki lalla Malika, ashe wannan kwanciya ba na tashi bane" cewar ƙanwar mahaifin su tana fashewa da kuka.

Sai itama Aicha ta sake fashewa da kuka tare da ɗagowa. "Aunty dan Allah ki kaini wurin mummy na. Please bata mutu ba, she just fell asleep, idan naje wurin ta zata tashi"

Har yanzu Aicha tayi yarinta ma sanin mutuwa amma sun riga da sun fahimtar da ita, babu ƙyaryar kuma da zata yi ya rufe mata hakan saidai kawai ta kwantar mata da hankali.

Kitson da ya sauƙo kan fuskarta ta mayar baya ta fara share mata hawaye da hannun ta, wani kukan yafi gaban tissue. "Ki yi haƙuri Darling kin ji? Zamu je wurin mummy amma sai kin daina kuka"
Laƙanin da tayi amfani da shi sai ya tuna mata da Malika, a ko ina a gaban kowa takan kira ta da hakan, amma gashi yau mai yanke ƙauna ta raba ta da gudan jinin ta.

Ɗan ƙaramin farin hannu suka ga ya miƙo handkerchief navy blue mai manyan check ɗin light green zai shiga goge mata hawayen tayi saurin kawar da fuskar ta tare da matsawa daga Jikin Reina.

"Stop crying Please my friend" Reina tace itama idanun ta na kawo ruwa. Ita a lissafin ta Aicha ƙawar ta ne, tunda daddyn ta yana yawan zuwa wurin nata daddyn a Nigeria, sannan mummyn su ma suna zuwa gidan juna, don haka Aicha is her friend. Sai ta ƙara matsawa kusa da ita da handkie ɗin, Aicha ma tayi saurin sake jan baya.

Ita kuma a nata lissafin har yanzu ɗan uwa namiji take so, bata son mace, kuma idan tayi ƙawance da Reina shikkenan Aunty ba zata kawo mata brother ba don haka take share su ita da Maama ma.

"Ki bar kuka kinji? Please" zuwa yanzu S ɗin ta ya fara fitowa amma irin mai cika bakin nan domin sai ta fisge shi ta ƙarfi. don haka miyan bakin ta ya tsartu a kan fuskar Aicha, sai ta ƙwace handkie ɗin hannunta ta goge fuskar ta da shi sannan ta dunƙule shi a hannunta ta kwantar da kanta saman cinyar Hajiya Fauziyya tana ajiyar zuciya. Reina kuma ta rasa yanda zata yi ta karɓa handkien Yaseer daga hannunta tunda itama ba nata bane.

~~~~~~~~

*Eid Mubarak 💕*

*REINA 💍*

Instagram, tiktok, arewabooks and Wattpad @Seemahwrites.

23....... Ɗaga kai yayi ya kalli girman mashigar Jami'ar bayan sauƙar shi daga kan mashin.

Shima yanzu ɗalibi ne a nan.

Goye yake da madaidaiciyar jakar baya sai kuma green file a hannun shi wanda ba zai samu shiga jakar ba saboda ya fi shi tsayi.

Ɗalibai ne kala da iri, mata da maza, musulmai da arna, sabbin zuwa masu riƙe da file irin nashi da kuma gabatattu, sai kuma motoci da napep ɗin makaranta da ke shigar da wasu ɗaliban ciki.

Ko ƙafa bai ɗaga daga wurin ba yaji sallamar wata daga bayan shi. Ya fahimci yana tsaye a kan hanya don haka ya matsa mata ta wuce amma sai ta dawo gaban shi ta tsaya, itama tana ɗauke da file irin nashi amma kalar blue.

"Ina kwana, baka gane ni bane?"

Murmushi ne kwance a kan fuskar ta ga ƙawayen ta da suke tare sun ja gefe suna jiran ta idanun su a kansu don haka ya saki ƙaramin murmushi shima saboda kada ya disga ta.

"Yi haƙuri fuskar ta ɓace min" yace ba yabo ba fallasa.

Ɗage gira tayi tare da matse baki a yangance tace "kai da wani abokin ka kuka kai ni department ɗinmu lokacin da muka zo physical screening amma har ka manta?"

Abokin shi ya raka ta dai. amma shi hanyar bursary ya ɗauka ganin zasu ɓata mishi lokaci gashi wa'inda suka san wurin sun faɗa mishi akwai layi.

Sai kawai yace da ita "oh ayyah, yaya kike"
Chapter 32 · 0% Book details