Sashe 44
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da yayi attending lectures ɗin safe kafin ya koma ya shirya kayan shi a ɗakin, su Muhammad suka taya shi. Daga nan kuma aka cigaba da fafatawa a fagen daga na karatu.
Abu ɗaya ne ya canza kuma ya fara damun shi, yanda Meesha yanzu ta dawo mishi wata mannani katanga, har mutane sun fara gulman su gashi saboda alkhairin da tayi mishi ba zai iya wulaƙantata ba.
Yaran manya da masu ji da kansu dake binta tana wulaƙantawa kuma sai suka fara jin haushin shi, shima yammatan dake ra'ayin shi yana gwada musu bayi da lokacin su sai suka shiga aibanta shi tunda gashi ya makalewa ƴar masu kuɗi hala ma biyan shi take yi suna wani abun da bai dace ba, tunda shi bai yi ma kowa ƙaryan shi ɗan wani bane.
Haka dai wannan semestern yazo masa a takure, ita kuma ta gagara fahimta ta rabu da shi.
.....
Sai yanzu ne Alhaji Tahir yayi ainihin lalacewa saboda kula da Maama da ya dawo wuyan shi, babu yanda Hajiya Farida bata yi ba amma yana tsoron kada shima a sake cutar da ita. Daɗin abun ma bai ji wani complain daga bakin Reina ba bayan ƙananun mitan da ta saba, gashi ta daɗa maida hankali a kan karatun ta da Yaseer harma a makaranta yanzu tana cin tests fiye da average.
Sai dai fa Jamal bai sauya sheƙa ba, yana nan yana kan laluɓe ta a sirrance, sannan yana kan lallabar ta da razana ta a kan kada ta faɗa ma kowa, dukda a yanzu tsoron hukuncin da zata fuskanta idan aka ji, da kunyar da zata sha shi yafi damun ta fiye da wani abu saboda a yanzu ta fahimci munin abinda take aikatawa musamman a irin nasihohin da Yaseer yake musu wanda burin shi ta rage sake jiki da maza barkatai ne amma bai san abin har ya fi haka muni ba.
Taso ta faɗa mishi amma tana tsoron irin kallon da zai fara mata gashi yanzu suna mutunci sosai don haka ta ja bakin ta ta gimtse shi.
Sai dai ta rage zuwa ɗakin Jamal a karan kanta. Wani lokacin idan ya kira ta sai tace tana zuwa har ya gaji da jiran ta ba zata je ba. Ko kuma idan yace ta fara zuwa ta jira shi yana zuwa Saboda kada a lura da shigewar su ɗakin a tare sai tace ya fara shiga tukunna. bayi son ya takurata ta bauɗe masa don haka sai yayi kaman yanda yace ita kuma ta gudu.
Sannan yanzu tana ƙoƙarin sallah a kan lokaci saboda irin azaban da Yaseer ya sanar da ita za'a dinga yiwa duk wanda bayi sallah a cikin kabarin shi da ma makomar mai wasa da Sallah.
Shi kuma Sallah tsari ne daga alfasha da munanan ayyuka. A hankali kallace-kallacen banzan nan ya fara sane mata a rai, ta koma maida hankali a kan educational program wanda zai taimaka ma karatun ta da ma wanda zata kalla saboda nishaɗi kawai tayi dariya.
*Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites ✨)*
*REINA 💍*
31......Tafiya ne ya taso ma Alhaji Tahir na sati biyu zuwa Abuja. Tunanin yanda zai yi da Maama ne ya dame shi, ya rasa ya kai ta ma Hajiya Farida ne ya bi ya ja mata kunnen kada ya ji kada ya gani ko kuma? Babu ma zancen su tafi tare saboda shima ba zama ya kaishi ba.
Da sallama suka shigo gidan, Reina na faman zungure ma Maaman kai amma bata ce komai ba kuma ta saka ma ranta ba zata yi mata kuka ba, sai tafiya kawai take yi a hankali Reina kuma bata fasa ba.
Sauƙowar Alhaji Tahir daga saman bene ya saka Reina ƙarasawa da gudu ta rungume shi domin kwanan nan bata wani samun ganin shi sosai.
Daman tayi mamakin ganin driver ɗaya ne ya ɗauko su daga school ita da Maama kuma sai yayo hanyar gida da su.
"Daddy aunty ta dawo ne?" Ta tambaya cikin zaƙuwa.
Kai ya girgiza kafin ya miƙawa Maama hannu itama ta karaso.
Itama so take yi ta tambaye shi auntyn amma nauyin baki ya hana ta, don haka sai ta tsura mishi ido tana jiran taji yace wani abu.
"Ku shirya zamu je bikin Aunty Sajida ne a gidan Ummi"
Duk sun fahimci dai waurin mahaifiyar su za'a je don haka suna rige-rige suka wuce sama suka kwabe kayan su aka shirya su suka sauƙo.
Babu mai nutsuwar cin abinci a cikin su amma haka Alhaji Tahir yayi jan ido Saboda bayi son su je su ci abincin biki.
Sama-sama suka ɗan taɓa sannan Reina ta saka masa rigima ko sallar la'asar bai kai ga yi ba suka fice.
Yau kam Maama tayi farin ciki da hakan.
Bayan mota ɗaya suka shiga da yaran sai kuma wani dake bin su a baya har cikin gidan su Hajiya Fauziyya, yayi umarni da a fito da kayayyakin dake bayan motar da ta biyo su.
Babu ɓata lokaci aka yi masa iso zuwa parlourn abban su saboda ƴan biki dake ta shirin zuwa kamu a babban parlour.
A hankali take takowa kaman bata son taka ƙasa, tayi siririyar sallama sannan ta shigo idanun ta a kan shi.
Yau ga idanun ta cikin na Tahir, yau ga Tahir ya ga daman zuwa yaga lafiyar abin cikin ta.
Kafin ta ida tunani Reina ta ruga ta faɗa jikin ta har saida Fauziyya ta dafa garu saboda kada su kai kasa domin jikin ta babu ƙarfi sosai.
Miƙewa Alhaji Tahir yayi shima yana kallon ta, kaman wanda suka shekara goma basu ga juna ba gabaki ɗaya Fauziyya ta canza.
Ya daɗe yana danasani amma a yanzu yayi ya sake.
Ta shafa kan Reina tare da mayar da idanun ta kan Maama. Bata zo gare ta ba, tana tsaye jikin mahaifin ta amma hawaye ke wanke mata fuska.
"Maama na ba zaki yiwa auntyn ki oyoyo ba? Ko kin manta da ni ne?"
"Kiyi haƙuri don Allah Fauzah"
Fauziyya ta mayar da duban ta gare shi jin raunin muryar da yayi amfani da ita.
Murmushin da yafi kuka ciwo tayi tace "Babu komai Tahir, dama na san wa na aura"
Tahir! Tahir! Bai taɓa jin sunan shi ya fito daga bakin ta ba sai yau. Mai kuma take nufi da ta san wa ta aura?.
Miyau ya haɗiya bayi son ya saka ma ranshi tunanin wai ya fara sanewa a ran Fauziyya ne, don ya sha ji a bakin masana soyayya wai mace bata iya faɗan sunan wanda take so take mutuntawa, bai tabbatar ko hakan bane amma da ƙamshin gaskiya a zancen tunda gashi yana ganin abinda bai saba gani ba a cikin idanun ta.
"Zauna mana, kada ki gaji da tsayuwa" ya ɗaga mata filallukan dake kan dogon kujera domin ta sake. Haushin kanshi matuƙa ya kama shi na rashin zuwan shi ya ganta a tsawon watanni huɗu sai yau.
Mai ya sha kanshi?
Ya fara hauka ne?
Babu musu ta karasa ta zauna ɗin, sai kuma ta kishingiɗa ta kwantar da kanta a jikin hannun kujera.
"Yaya lafiya? Ko jikin ne?" Ya ƙarasa da nufin taɓa ta yaji zafin jikin ta, tayi saurin riƙe hannun shi tana mishi wani irin kallo.
Basarwa yayi ya zauna tare da ɗago ta ya kwantar a jikin shi yana taɓa goshin ta da wuyan ta ga jikin ta yayi rau kaman garwashi.
"Tun ƙarshen wancan watan nace ma Abba zamu koma gida yace na bari sai jikin ki ya ƙara kyau"
Samu tayi ta ƙwace daga riƙon shi ta matsa gefe tana dariyan yake wa yaran da suka kafe su da idanu.
Waya ta ɗaga ta kira a turo a ɗauke su a basu abinci.
Yanzu kam Alhaji Tahir bai damu ba indai zata saurare shi, don haka yayi shiru yana kallon ta tana kallon yaran da tayi kewar su kaman zata cika har aka shigo aka tafi da su.
"Amma shine baka ga daman zuwa ba sai yau? Ko baka zo don ni ba Tahir ba zaka zo don abinda ke ciki na ba?"
Bayi da amsar da zai bata, sai kawai ya canza zancen tunda ya san bayi da gaskiya.
"Ban kai Maama Nijar ba, ƙarya nayi miki" yana da yaƙinin hakan zai canza wani abu.
Taɓe baki tayi tace "idan ma ka kaita ba gashi ta dawo ba?"
"Fauzah kiyi haƙuri mana? Me yasa baki da haƙuri ne?"
Kallon shi tayi tare da sakin dariya mai sauti tana jin yanda fitar shi ya ƙona mata ƙirji.
Bani da haƙuri? Ni lokacin da nake baka haƙurin halan naka aika yaje. Shine kalaman da zuciyar ta ya tanada mata ta faɗa mishi amma sai "Hmm" kawai bakin ta ya furta.
Duniyar ma da abin cikin ta baki ɗaya nawa yake?
"Toh ko zamu je asibiti ne?" Ya sake magana.
Girgiza kai tayi, ba don tana son magana dashi ba sai don ya ƙyale ta yasa tace "zazzaɓin yammaci ne kawai nake fama dashi kwanan nan, anjima zai sauƙa"
"Amma kin fada ma doctorn da yake zuwa? Ya baki magani?"
Sai ta gyaɗa masa kai kawai.
"Allah ya sawaƙe. Yanzu kinga ba ma iya halartar bikin zaki yi ba, in dauke ku mu koma gida ne ko in bar miki yaran idan kun gama ku dawo?"
"Kaje zamu dawo"
Bai gaji ba yace "akwai kuɗi a wurin ki ko ya ƙare?"
Ita ko kuɗin shin ma kwana biyu bata son taɓawa gashi duk sati sai taga alert, saidai kawai tayi ta alkhairi da shi.
"Akwai"
"Kunga aika jiya?"
"Mun gani Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi"
Kusan shi ya ɗauki ɗawainiyar baki ɗaya bikin nan da za'a yi, tun daga ci da sha har kayan ɗakin amarya.
"Fauzah ki saki jiki kiyi min maga Please, bani son ganin ki so dull hakan nan. Kinga tafiya zanyi gobe don Allah ki faranta min ko zan samu kwarin guiwar fuskantar abinda yake gaba na"
Yanzu kam ya fara damun ta don haka ta riƙe kai tare da rintse idanu kaman wanda take cikin tsananin ciwo.
"Likita yace ina hutawa sosai T, kuma kada ana damu na da magana"