← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 57

Sashe 27

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Juyowa yayi ya sake kallon yanda tayi lamoo a cikin seat ɗinta, Maama kwance saman kafaɗar ta, tana kallon hanya kamar wata marainiya.

"Daddy a kunna min baby Shat" Reina ta faɗa a kunnen shi, don ba wai ta bar tsoron Auntyn bane.

"Toh sarauniya ta" sai da yayi parking ya gyara mata zama a seat ɗin baya ya maƙala mata seat belt, kafin ya fito da wata ƴar remote Ya danna play a jikin tvn da ke jikin headrest din shi, daman shi take kallo a hanyar su ta zuwa, nan da nan ya ɗauke hankalin ta kuwa.

Har suka yi rabin tafiyar bata ce komai ba shi kuma shirun ya ishe shi, sai jin hannun shi ta yi a saman cinyar ta.

"Fauzah ta yaya akayi ne? Meye labari?"

Da suka haɗa ido ya ɗage mata gira ɗaya, sai ta saki murmushin da ya saka shi jin daɗi a tunanin shi ta sauƙo ne, ba tare da ya sauƙe hannun shi daga jikin ta ba ya koma tuƙin da hannu ɗaya.

Ta dai mishi shiru har sai da ya tsaya a kofar wani modern bakery don siyan cake ɗin da yayi alƙawari ma Reina, itama ya siyo mata brownies da chocolate chip cookies.

Karɓa tayi haɗe da faɗin "na gode, amma ka san zan iya abu na da kai na, ko kuma dan a toshe min baki ne?!"

Nan ya fahimci rikici take nima amma a daren yau ko sheɗan ne ke tiƙa rawa a ƙwaƙwalwar ta shi ba mahaukaci bane da zai biye mata asara ya hau shi.

"Na san da hakan ai, kinga sai ki huta na kwana biyu tun da an siya"

"Hmm. T kenan"

Sai a lokacin ya ɗaga hannun shi ya mayar kan sitiyari, ya fahimci so take yi ta dawo da halin da ta aro tun da yammaci. "Ki faɗa min menene farashin fara'ar ki ni kuma zan siye ta duk darajar ta. A mance da abin da ya riga ya wuce kawai!."

"Ba kuɗin ka nake so ba ka sani"

"Ko menene shi ki faɗa zan yi miki shi"

"Ko menene kace fah?"

"Ko menene Fauziyya "

"Planning nake so in yi na shekaru biyar"

Wani wawan birki da ya ja ya sanya ta ƙara rungume Maama tsam a ƙirjin ta yayin da kanta ya kusan buguwa a gaban motar.

.......

"Umma Socks ɗin Sabir, na manta ban ɗauko ba"

Fitowa Saudat ta yi da socks ɗin a hannun ta, lokacin Yaseer ɗin ya koma ɗauko back pack ɗin shi a ciki.

Ya taje sumar kan shi, zuwa siririn sajen da ya ƙawata fuskar shi, zuwa ƴar gemun sa dake kan tsirowa kuma Alhamdulillah yana samun ban ruwa da taki kaman yanda ya kamata.

Kana ya ɗofana Jan Barrett din shi a gayence, ya bi ko ina na ilahirin jikin shi da turare, Kafin ya saka aninin hannun rigan.

fitowa yayi ya shiga ɗakin iyayen shi ma ya ɗauki turaren mahaifin shi ya ƙara, daman tun jiya ya roƙe shi kuma yayi mishi izini ko duka zai feshe, domin yau rana ce ta musamman.

Tsayawa yayi a gaban Mirrorn Umma yana kallon kan shi. yau rana ce ta musamman, wannan farin rigan jikin shi ƙall da ya ɓata lokaci wurin wanke ta da goge ta bayi da jaa a kan lokacin da zai dawo da Ita zata kasance a rine da kalolin marker da Biro. Yau zai kammala rubuta exams ɗin Waec, saura Neco kuma. daga yau zai tashi a matsayin secondarian, za su yi candy a yau.

"Yaya Headboy zaka saka ƙanin ka latti fah" cewar Saudat daga waje.

Zanin da ya rufe fuskar ƙanin shi mai shekara ɗaya dake barci ya yaye mishi, sannan ya gyara masa kwanciya saboda numfashin da yake yi a wahalce yana fita da kyau, kafin ya fito.

Saudat ta riga ta saka wa Sabir socks da sandal dan haka ya zura nashi takalmin kafin ja ɗauko keken shi ya goya shi a kai Saudat na bin su da addu'o'in kariya. kuma saida Yaseer ya tabbatar sun yi addu'ar fita daga gida kafin suka bar gidan, Suhail dama ya riga yayi gaba don har gobe a ƙafa suke tafiya shi da abokan sa.

.....

Paper tayi daɗi ta yi wahala a ranakun da invigilators suka hana shigo da expo. Da yawa a cikin dalibai sukan kwatanta makomar su a wannan gaɓar, da yawa kuma an yi dafsu ɗin da komai amma ranar da sakamako zai fito sai a ga saɓanin tunani saboda shi karan kanshi expo ɗin shirme aka kwafa.

Amma ba wannan bane damuwar su a wannan rana. Gurbin ajiye tarihi suke nema a zuciyoyin su, suturan su, da na'urorin su. Don yawanci sun zo da waya sai dai wainda basu da shi kaman su Yaseer ɗin.

Sai dai fa yanda ake jawo shi ta ko ina ya shiga hoton su ma har ya fi masu wayoyin farin jini. Rubutu ne ko ta ina a jikin shi.

Hango ƙatotuwar zanen zuciya a bayan rigan shi wanda aka yi da jan marker a ciki kuma an rubuta 'With Love Yasmeen' ya saka Yar uwar shi a muƙami wato headgirl ta ƙarasa ta cukumi wuyar Time keeper....... Wuhuhu🎉😂

~~~~~~

*The Longest chapter so far sannun ku sannu na🥲🥰. And Happy Ranan Yara👼🏻. If you've made it this far please ku yi addu'a ma yara da mutanen da ke rayuwa a palestine. Allah ya kawo ƙarshen wannan zalunci da ake musu, Allah ya mayar da dukkan sharri da makirici kan masu ita, ya tarwatsa su ya tarwatsa shirin su. Sannan Allah ya taimaki musulunci da musulmai a duk inda suke a faɗin duniya. Ameen*

*#Free Palestine🇵🇸❤️‍🩹*

*Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites✨)*

*REINA 💍*

19......ki daina cakalar abincin nan Reina!" Fauziyya ta tsawatar mata da kakkaurar murya, bayan ta goge wa Maama gaban rigan ta da ya ɓaci da maiƙon kifi da handkerchief ɗinta mai laushi.

Zumɓuro baki Reina tayi tana kallon Alhaji Tahir. Ya murmusa tare da tallafo ɗan fuskar ta cikin tafin hannun shi. "Yaya aka yi ne sarauniya ta?" Ya tambaya da kulawa a cikin muryar shi.

"Daddy bani son wannan abincin" tace tana riƙo hannun rigan shi.

Fauziyya kaman jira take yi ta hau ta da masifa.
"Kin san Allah ko mutuwa zaki yi sai kin ci?! Baki da aiki sai fidda fice baki son kaza baki son kaza Idan ba shegen ɓaci ba. Kin san mutane nawa suke niman abin da kike samu kike ci a kullum suka rasa?"

"Haba Fauzah, meye abun ɓacin rai a nan kina magana da ƴar shekara 6 kamar wata babba?"

Bata tanka ba, ta maida hankalin ta ga Maama dake ƙoƙarin ɗaukar glass ɗin ruwa ta sha da kanta, don haka ta taya ta riƙewa tana kurɓan ruwan a hankali har sai da ta ɗaga kanta alamun ta ƙoshi.

"Ya Ishe ki Maama na?" Ta shafa gashin kanta mai cika, laushin sa ya saka ya nannaɗe.

Gyaɗa kai tayi tare da murmushin da ya saka gefen kumatun ta ɗaya lotsawa kasancewar itama Fauziyyar murmushin ne a kan fuskar ta.

Ayyanawa take yi a ranta, idan Allah zai bata yara dubu kaman Maama ba zata gaji ba. Bata san meye wahalar raino a kanta ba, gata da shiga rai, ga kyau, ga fara'a, don haka son da take mata daban ne a cikin zuciyar ta.

"Sarauniya ta me kike so ki ci?" Alhaji Tahir ya maida hankalin shi kan Reina dake wasa da fork ɗin ta a kan chips and egg dake cikin nata plate ɗin, duk ta gama dama shi da ketchup da kuma baked beans da aka zuba a gefe.

Alama tayi masa da ya kawo kunnen sa. Ya matso, ya tanƙwaro, kana ta raɗa masa "Rice Krispies ko Cake"

Fauziyya ta sake amshewa da,
"Ai kuwa ke da sauƙa hala sai cikin kabarin ki idan ana ramewa. tunda kayan maƙulashe da sugar sune abincin ki a ko yaushe. Haka zaki yi ta zama da funkum-funkum ɗin kumatu kaman ana saka miki yeast, ciki kullum kaman mai shirin haihuwa"

Rai a ɓace Alhaji Tahir ya miƙe, ya sauƙe Reina daga kujerar sannan ya jata zasu bar gidan baki ɗaya.

Da sauri Fauziyya ta miƙe ta fara bin shi a baya tana faɗin "T. Zata yi shirin tafiya school fah!"

"Ba zata je ba" ya amsa a takaice, daɗi kuwa kaman ya kashe Reina.

Fauziyya ta ci gaba da bin shi har suka fita farfajiyar gidan, aka ƙaraso mishi da motar da zai fita da ita.

"Toh Zancen zuwa ofishin alhazan fa?"

"Direba ya kai ki" shine amsar da ya bata yayin da aka buɗe mishi mota ya fara saka Reina kafin shima ya shiga babu ɓata lokaci suka bar gidan.

.......

"Umma! Wallahi yau wasu mata sunyi faɗa a kan Yayan mu!!" Sallamar Suhail kenan bayan ya bankaɗe kyauren gidan su ya faɗa ciki, ya kuwa yi sa'ar riskar Saudat a ƙarƙashin inuwar neem ɗin da ya ƙara girma da kauri a yanzu, inuwar shi ya kusa lulluɓe tsakar gidan baki ɗaya.

Zaune take tana ƙulla sana'ar ta, sai yaron ta dake daga gefe yana wasa da igiyar tabarma.

Da sauri Yaseer ya riƙo Suhail ya rufe mishi baki da tafin hannun shi amma ya riga da ya fasa ƙwai.

"Nima na gani umma, har da marin mai jan ɗankwali aka yi, aka yaga mata hijabi" Sabir ya ƙara cikin nishaɗi amma suna haɗa idanu da Yaseer yaga irin kallon da yake masa sai ya sha jinin jikin sa tare da sauƙe kan shi ƙasa yana matse baki.

"Ashe yayan mu? Zo ka bani labari wacece amaryar mu a cikin su? Wacce ta yaga Hijabin ko wanda aka yaga mata?"

Hankali a tashe yace "Umma Amarya kuma?"

"Eh mana! Amarya kai! Tunda har an fara faɗa ba gwanda ayi a tantance, Abban ku yaje gidan su ɗaya a raba gardama ba? Ko ƙarya aka maka?"

"Wallahi Wallahi Umma ni ban taɓa kula ɗaya daga cikin su ba" yace yana durƙusawa a gaban ta don ta yarda da shi.

Cikin idanun shi ta kalla tana karanta saƙon dake cikin su.
Chapter 27 · 0% Book details