Sashe 3
Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gadan² haihuwa tazo ma Hajiya Fauziyya don haka suna isa asibiti aka shiga da ita labour room. cikin ƙasa da minti 30 Alhaji Tahir ya ƙaraso tare da wanda yake bi Alhaji Salisu mijin Hajiya Hauwa dake lokacin suna tare yayi waya da Saudat. Isowar su bada jimawa ba Alhaji kalabu babban yayan su shima ya iso haka duk suka jeru cirko-cirko ana zaman jiran tsammani, kafin wani lokaci sai ga ƴan uwansu mata ma sun ƙaraso daga gidan ɗaukan amarya suma suka shiga sahu.
Bayan awa ɗaya saƙo mai daɗi ya iso gare su. Hajiya Fauziyya ta sauƙa lafiya kuma an samu ƴa mace, turus suka yi da jin haka don sunyi tsammani namiji zata haifa, yanda Alhaji Tahir yake son ɗa namiji don ya samu magaji da kuma ganin yanda yake rawar ƙafa akan cikin nan yasa duk suka yi tunanin an riga an faɗa musu namiji zata haifa amma kuma shi ya riga da ya san kwanan zancen.
Shi ya fara shiga bayan an kai su ɗakin hutu an gama kintsa Fauziyya da ƴar ta aka kwantar mata ita a saman kirjin ta.
Da murmushi a saman fuskar shi ya ƙarasa jikin gadon. Peck ya fara sauƙewa Fauziyya a kan goshin ta, daɗin hakan da yayi ya sanya ta lumshe idanun ta itama tana murmushi.
"Nagode. Fauza kin biya ni, Allah ya sanya ki a gidan aljannah" laɓɓan bakin ta ne ya nuna alamun ta amsa da 'ameen' amma bai fitar da sauti ba.
Hannu yasa da nufin ɗaukan babyn cikin kiyayewa da taka tsantsan, nurse ɗin da ta gama kintsa musu ɗakin ta taimaka mishi ya rungume babyn shi a ƙirjin shi kafin ta fice don basu wuri.
Kallon tatsitsin fuskar yarinyar yayi tare da furta "Tabarakallah masha Allah. Fauza see her cute little face" ya faɗa idanun shi kafe a kan yarinyar kamar zasu zubar da ƙwolla.
"I'm sorry T. Ba namiji bane" ta faɗa cikin kasasshiyar murya.
"No Fauza, namijin ma Allah zai kawo. Idan ma Allah bai bamu ba baby mai ta rage mu dashi? Zata zama magajiya kuma sarauniyar T.K Kingdom ko baby na?" Ya shafa ɗan bayan ta.
Har cikin ranta Hajiya Fauziyya taji daɗin kalamin shi. Ya matso mata da yarinyar ganin ta buɗe idanun ta tana mommotsa baki. Yatsar ta manuniya Fauziyya ta zura cikin tafin hannun yarinyar ta kuwa damƙe yatsar, dukkan su suka saki murmushi mai sauti kafin Fauziyya ta ɗan jijjiga yatsar dake hannun babyn a hankali ta furta "Helloo REINA".
"REINA? Sunan da kike so a saka mata kenan?"
Dariya Fauziyya tayi tace "A'a yana nufin Sarauniya. Sarauniyar dadyn ta kuma sarauniyar T.K Kingdom". Suka sake sakin murmushi yayin da ƙofar ta buɗe Hajiya Lubabatu ta leƙo.
"Nace a bamu yarinyar mu gani kafin ku gama".
"A'a Addah ku shigo don Allah" Hajiya Fauziyya ta amsa tare da zare hannun ta daga cikin na Reina.
Shiko Alhaji Tahir ba haka ya so ba, don bai ƙi a basu babyn ba, su barsu su ci gaba da zantawa domin ji yake yi kaman ya haɗiye Fauzar shi tsantsan so.
Suna ganin an baiwa Hajiya Luba damar shiga duk suka yi dandazon shigowa ɗakin ciki harda saudat riƙe da hannun Yaseer harma da Kamal da ya biyo su a acaɓa ganin mota ya fito daga cikin gidan ya fita da ɗan iskan gudu ga kuma Yaseer a gidan gaba, sai kuma Suhail ya fito yana kuka an koro shi daga cikin gidan kuma baiga umman shi ba, ga jikin shi duk datti.
Miƙa musu babyn Alhaji Tahir yayi aka fara passing-passing da ita duk wanda yayi arba da tatsitsin fuskar ta sai ya ambaci masha Allah gashi ta ware idanun ta dar a kan mutane tana turo harce daga cikin ɗan bakin ta.
Hajiya Jummai wanda Alhaji Salisu yake bi itace last ɗin karɓa a cikin su sai ya zamo Saudat ne kawai bata ga fuskar babyn ba jira take idan sun gama su bata amma sai Hajiya Jummai ta riƙe ta tsamm a jiki ba don bata san Saudat ɗin jira take ba sai don ba zata bayar bane kawai.
"Hajiya bari in ɗan ga jaririyar" Saudat ta miƙa mata hannu ganin bata da niyya.
Kallon sama da ƙasa Jummai tayi wa Saudat, tana jin yanda take tashin tsami² saboda aikin da suka sha a cikin rana. Abin ka da babu turare mai karfi.
A maimakon ko nuna mata fuskar babyn tayi a hannun ta ba tare da ta bawa Saudat ɗin ba sai cewa tayi.
"Wai me ma yasa kuka wani tattaro zuga kuka zo ne? asibiti kaman wani gidan biki?"
Maganar ya doke ta. Su ba zugan suka yi ba harda sakawa a je a ɗibo musu yara kaman mai jegon ba gida zata koma ba?
"Ba don Saudat ba maybe da wani zancen ake yi. Ita ta taimaka min na iso asibiti a kan lokaci don Allah ku bata Reina taga ƴar ta" cewar Hajiya Fauziyya cikin sassanyar murya yanda ba zata ɓata ran Hajiya Jummai ba ta hanyar yi ma Saudat adalci. amma duk da haka sai da Jummai ta ƙufula gani take saboda an haifa wa mai dukiya ƴar So ne har take iya bata umarni tana matsayin yayar mijin ta.
"Wacece kuma Reina?" Kusan dukkan su suka hada baki wurin tambaya.
Ƙasa Fauziyya tayi da kai don bata san lokacin da tayi suɓutar baki ba sunan ya fita.
"Gata a hannun ku, sarauniyar T.K Kingdom" Alhaji Tahir ya basu amsa.
riƙe baki Hajiya Hauwa tayi "tohh, ai shikkenan munyi kamu. Jamal zo kaga matar ka" ta riƙo hannun yaron ta mai shekaru 9 da nufin su karɓi babyn ya ganta.
Daɗa rungume Reina Hajiya Jummai tayi a ƙirji. "Ko kuma matar Haydar ɗina ba"
"Ko ta lukman dai" Hajiya luba ta tsuke fuska. Da mamaki Hajiya Farida mai bin Hajiya luba tace "haba yaya. Lukman mai shekaru fiye da 20 me zeyi da babyn da aka haifa yau? Ai kafin ta girma ya zama magidanci da ƴaƴa"
"Kuma sarauniya ta ba zata zama kishiyar wata ba" Alhaji Tahir ya faɗa. Yana karɓar yar shi daga hannun hajiya Jummai.
"Shiyasa nace Jamal ɗinne ya dace da ita. Tazarar shekara 9 a tsakani yayi dai²"
Nan suka ci gaba da musu a ƙarshe dai Kamal waje ya fita ganin zancen na manya ne, yarinyar da bata shaƙi iskar duniya na fiye da minti 30 ba har an mata miji.
Saudat ma har aka ƙarashe kacaniyar su basu bata babyn ba daga ƙarshe ne likita ya buƙaci ganin mai jego nan kowa ya watse.
Yaseer shine ƙarshen fita bayan Saudat. Har yaje bakin ƙofa ya dawo da gudu jikin crib ɗin da yanzu aka kwantar da babyn bayan ta koma barci.
Leƙa fuskar ta yayi tare da taɓe baki.
"Caɓdi, ashe mummuna ne ma Reinan aka wani dame mu"
ya faɗi hakan ne sanadiyyar jin haushin banzantarwan da aka yi wa mahaifiyar shi amma ji yake kamar yayi ta lallatsa fuskar babyn.
Da sauri saudat ta dawo ta riƙo hannun shi. "Yi hakuri don Allah aunty, yarinta ke damun shi."
Murmushi Fauziyya tayi tace "kiyi haƙuri umman Yaseer, sannan kizo kiga baby idan mun koma gida dan Allah. Na gode sosai da taimakon ki, kema Allah ya sauƙe ki lafiya"
"Ameen, in sha Allah" Saudat ta amsa sannan tayi saurin fita da Yaseer saboda likitan ya ƙaraso.
....
"Ashe an samu ƙaruwa Alhaji, Allah ya raya" cewar Kamal da yayi arba da Alhaji Tahir tare da Alhaji salisu bayan sun fito daga ɗakin.
"Ameen Kamalu na gode" ya juya yaci gaba da maganar shi da Salisu.
Sunan mahaifinsu gare shi amma yana shan mamaki duk lokacin da suka kira gatsau babu wani sakaye.
Ganin kamal ya ci gaba da tsayuwa yasa Alhaji salihu tambayar
"Yaya dai? Da wani abun ne?".
Yasan cewa environment ɗin da suke bai dace da maganar dake ƙunshe a bakin shi ba amma bayi da yanda zaiyi ne. Yayi ta niman yanda zaiyi ya haɗu da Alhaji Tahir ɗin amma abu ya ci tura sai yanzu kuma nan da kwana biyu za'a rufe registration.
"Daman maganar makarantar Yaseer ne. Nace an fara registration na jss1 har ana niman rufewa bamu samu daman yi ba" rufe bakin shi ke da wuya Alhaji Salisu yace.
"Amma baka da hankali wallahi Kamalu!. Haba! Mutumin da aka yi wa haihuwa a asibiti kake tambaya kuɗi?"
Shiru kamal yayi don bayi da ta cewa.
Taɓe baki Alhaji Tahir yayi kafin ya zura hannu cikin aljihun shi yana ƙirga kuɗin kafin ya zaro dubu 10 ya miƙa wa kamal.
"Ga wannan a masa register daga baya sai kazo ka karɓi na uniform"
Godiya kamal yayi yana shirin karɓa Alhaji Salisu yayi saurin wafce kuɗin.
"Haba kai kuwa Tahir, an haifi sarauniya guda baka sallami ma'aikatan asibitin da suka taimaki matar ka ba zaka cire kuɗi ka bashi? Ai saidai ya biyo ka daga bayan ya karɓa duka".
Gyaɗa kai alhaji tahir yayi alamun gamsuwa. "Toh shikkenan gobe sai kazo gida ka same ni ka karɓi gaba ɗayan"
Yana gani Alhaji Salisu ya zura kuɗin cikin aljihun shi suka juya suka yi tafiyar su yayin da Kamal ya bushe a wurin da mamaki. In ba baƙin hali ba me Alhaji Salisu zai yi da naira dubu10 fisabilillahi!?.
*Mrs Imran ✨*
*REINA💍*
بسم الله الرحمان الرحيم
03.....hankali, a hankali. Kamar zaiyi mata tafiyar haka Alhaji Tahir ke riƙe da Hajiya Fauziyya yana ƙirga dukkan takun ta cikin kiyayewa har suka shiga Babban parlourn. Kaman daga sama aka shiga saka guɗa ta ko wani kusurwa har saida Reina dake bacci a hannun aunty Zeenat ta ɗan firgita.