← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 57

Sashe 26

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da yunwa a cikin shi, ga gajiya, ga ɓacin ran da Fauziyya ta ƙunsa mishi. don haka ha zauna yana ci ba kuma daɗin abincin yake ji ba, domin ba zallan Fauzah yayi kewa ba harda girkin ta mai shegen daɗi.
kuma a kullum cikin ƙirƙirar sabon abu take don haka ko yaushe a cikin ɗaukin me zai dawo ya ci yake.

"Ina Reina?" Ya tambaya yana kai lomar shinkafa da nama bakin sa, amma taurin naman yasa ya yanki tissue ya kai bakin shi ya fito da naman sannan ya ƙunshe a ciki, wannan ai sai ya kai gobe bai gama tauna shi yayi laushi ba.

"Oh sun fita wasa da yaran, ka gama sai a kira maka Ita kada ta zo yanzu ta hana ka cin abincin"

Ya gyaɗa kai tare da kai ruwa bakin shi, amma bai kai ga sauƙe glass cup ɗin ba ta shigo da ɗan iskan gudu tana "shegiya! Allah ya Isha!" Ta faɗa jikin Hajiya Jummai ta ɓoye don lokacin bata lura da mahaifin ta a wurin ba.

"My daughter wa ya taɓa ki?" Hajiya Jummai har wani daɗa rungume ta tayi kamar zata shayar da ita saboda idon Tahir ɗin.

"Jahya ne ta duke ni, Allah ya Isha kawai"

"Zahran Umman Jamal?" Ta tamabaya tana jin daɗin faɗar ba da yaran ta ake ba.

Reina ta gyaɗa kai tana nuna Zahran da yanzu ta shigo riƙe da hannun wata yarinya wacce ke ihu da kuka idanun ta a rufe gamm.

Dukkan su ba zasu girmi Reinan sosai ba, wacce idanun ta ke rufe ne tace "wayyo Mummy! yaji a ido na mummy!"

Ta miƙe tare da sauƙe Reina a ƙasa. "Zo mu gani, garin yaya kika saka yaji a idon ki?" Ta tsuguna ta fara hure mata amma kaman ƙara mata azabar take yi don wanda bai gama shiga ciki bane ɗazu take ƙara mata, ta shiga tsala ihu da tsalle a wurin.

"Reina ne ta watsa mata yaji a ido, wai don ta hana ta taɓa cake ɗin yaya Haydar a cikin fridge "

Takaicin ta naɗa ma Reina ɗan banzan duka ne ya kama ta amma ta danne.
Ta ƙwala kiran mai aiki da tazo ta ɗauke ta a wanke idon, Sannan ta koma ta zauna tana dariyar yaƙe.

"Ke kuma Zahra ba dukan ta zaki yi ba ai sai ki kawo ƙaran ta, amma kin jawo ta zage ki yanzu. Kuma ma ai itama ƙanwar Haydar ne, da Haydar da abun da ya mallaka duk na Reina ne" kalmar ta na ƙarshe yana ɗauke da ma'ana biyu, Alhaji Tahir ya ji ta amma bai kai zancen cikin kan shi ba ma balle ya fahimta, ba wannan bane damuwar shi ba a yanzu.

Miƙewa daga kan dining ɗin yayi ya maida hular shi yana faɗin "Mu zamu wuce Yaya."

Ya dubi Reina "ina takalmin ki?"

Da hannu kawai ta nuna mishi hanyar waje, ya ja hannun ta ba tare da yayi godiya ma Hajiya Jummai ba balle ya saka Reina ta bawa Amrah haƙuri.

"Daddy wurin Aunty zamu je?"

"Kina son zuwa wurin Auntyn ne?" Ya tambaya lokacin da ya tada motar.

"Eh daddy, muje inga baby pleash"

Shi daman ya san ba wai dai taje don tayi kewar auntyn ba sai ko don Maama.

"Shikkenan, Amma idan muka je kiyi kuka kice a bamu baby mu dawo da ita gida kin ji?"

Ta gyaɗa kai "Aunty ba jata jane ni ba ko?"

"Ba zan barta ta zane ki ba. Kiyi kuka kina birgima irin wanda kike yi idan aka hana ki cake kin ji?"

"Toh jaka shiya mun Tek ɗin tun da wancan Amyan ta min yowa?"

Yanda take complain ɗin Sai yaga kamar ta da Fauziyya ya daɗa fito mishi, don haka ya tallafo kan ta ya sumbaci goshin ta yana faɗin "Cake sai wanda kika zaɓa sarauniya ta"

....

Kaman yanda ya umarta da shigan su gidan ko gaisawa da mutan cikin ta basu yi ba Reina ta zube a tsakar falo tana birgima Ita a bata baby su tafi.

Sahre ta suka yi daga farko, Ummi ta dubi Tahir tana faɗin "Ai ɗazu da aka ce ka zo baka shigo ba nace toh ko sauri kake yi"

Sosa ƙeya yayi yana dariyan yaƙe "Wani aiki ne ya taso na gaggawa shine aka kira ni, daga nan kuma na je na ɗauko ita yarinyar saboda ta dame ni tana son zuwa wurin Auntyn ta"

Ummi tayi murmushi irin nasu na manya "ina dai ka gama aikin ko?"

"Eh, na..na gama. Daman saka hannu ne kawai babu ɓata lokaci"

"Toh masha Allah "

Zuwa yanzu kukan Reina ya gama isar Fauziyya.
"Kai zaro min tsintsiyar kwakwa a bayan ƙofa".
Tace da ɗan aunty Zeenat. Shima daman kaman jira yake yi don ta cika musu kunne, ya ciro su dogaye har guda uku ya miƙa ma Auntyn, ai kuwa tayi kanta gadan-gadan.

Kafin Alhaji Tahir yayi yunƙurin kwatar ta Ummi tayi saurin ɗaga ta. "Zo abin ki mai sunan." Ta ɗaura ta saman cinyar ta." Ina baby kike so a baki?"

Ta gyaɗa kai.

"Shikkenan an gama. Fauziyya sai ki tashi ki haɗa muku kayan ku, Idan abban ki ya shigo anjima kuyi mishi sallama ku tafi" still idanun ta na kan Reina take magana.

A razane Fauziyya tace "Ummi ban fa gama warkewa ba" lokaci ɗaya idanun ta na tara ruwa.

Ba wai son komawa gidan bane bata yi, Alhaji Tahir ne bata so ya yi Nasara a kan ta. Kuma tana da yaƙinin har yanzu bai canza sheƙa ba tunda abun na Reina cikin kwanakin nan kaman ƙaruwa taga yana yi.

Ummi ta ɗago ta kalle ta "Ta yaya za'a basu jaririya ba tare da uwar ta ba bayan ikon su a kanta suka gwada mana? Ai sai dai kiyi haƙuri ki je ki ƙarasa jinyar ki a ɗakin ki. Allah ya baki lafiya"

Alhaji Tahir ya sauƙe kan shi ƙasa a kunyace don saƙon ta ya Isa yanda ake buƙata, sauran aiki da shi.

....

Tana cikin haɗa kayan, Ummi ta shigo ɗakin hannun ta ɗauke da laida guda biyu ƙarami da babba.

"Wannan na baƙin laidan su ne magungunan ki, kada kiyi wasa da su don na san ki da ƙin magani shi yasa na riƙe a wuri na." Ta saka mata a zip ɗin da ke murfin akwatin ta rufe kafin ta gwada babban laidan.
"Wannan kuma duk na rubuta yanda zaki yi amfani da su, Amma duk abinda baki gane ba ki kira ni."

Godiya tayi a can ƙasan maƙoshi don ji take yi wani abu ya maƙure ta a wuya. Bata yi tsammanin zasu maida ta ma Tahir da sauƙi haka ba, ta ɗauka sai ya tsuguna a kan guiwowin shi ya basu haƙuri itama ya bata tukunna.

"Ni na baki shawarar ki zauna har wannan lokacin saboda na ga dacewar hakan, toh yanzu ma na umarce ki da tafiya ne saboda dacewar hakan da na gani.
Ki wanke duk abinda ke cikin zuciyar ki, ki ci gaba da zama da mijin ki da zuciya ɗaya Fauziyya. Yanzu ko kin ƙi ko kin so girma ya zo miki, ke uwa ce a yanzu ba zallar kan ki da jin ɗaɗin ki zaki dinga dubawa ba harda goben yaran ki.
Ba ko wani lokaci ne mutum yake samun adalci a kan gaskiyar shi ba, kamar yanda ba ko yaushe ake hukunta ka a kan kuskuren ka ba. domin da saki uku yayi ma aure kaɗan idan ba'a hakuri ba'a yafiya."

Ta ja hanci tare da share ƙwalla tana taryo itama rashin adalcin da tayi wa Tahir ɗin a iya zaman su. Kuma har a gaban Allah zata bada shaidar ya kyautata mata, ya kare mutuncin ta, ya kula da ita, sannan yayi ƙoƙarin sauƙe hakkokin ta dake wuyan shi.

Ganin Nasihar na ratsa ta yasa Ummi ta riƙo hannun ta.
"A game da Reina kuma... Fauziyya idan ke da kika ɗau cikin ta wata tara kika haife ta kika raine ta kin guje ta toh wa kike tsammanin zai ja miki ita jiki ya gyara kuskuren da kuka yi a wajen tarbiyyar ta? Yau idan Hafsatu ta ɓaci ina tabbatar miki kafin a nuna Tahir da yatsa sau ɗaya sai an nuna ki sau goma hala ma a samu wanda zai zungure ki da shi. Domin alhakin tarbiyyan ta ya fi nauyi a kan ki a matsayin ta na ƴa mace ke kuma uwa.
Ki jawo yarinyar nan a jikinki ki shiga cikin duniyar ta ki buɗe mata kofofin ciki masu alheri, kada ki barta tayi ta laluɓe a cikin duhu.
Ki ajiye damuwar Tahir a gefe ki saita yarinya yanda ya kamata, shi dama ba zama yake ba a gidan, lokacin da zaku ci ku cinye yana ina?.
Na faɗa miki kuma ina ƙara jaddada miki uwa bata taɓa fita daga lamarin yaran ta har Ranar da ƙasa zai rufe idanun ta, dalilin haka yasa kike tsaye a gaba na a yanzu Fauziyya, kuma nake baki shawarar da zai amfani rayuwar ki Saboda ni mahaifiyar ki ce, duk duniyar nan wanda zai so ki a baya na yake"

Bata tsaya ganin kukan ta ba ta juya gudun kada ta karya mata zuciya. "Ki yi wanka ki yi alwala gani nan zuwa" ta fice daga ɗakin, sannan Fauziyya ta zuge zip ɗin akwatunan su ta sauƙe su a ƙasa bayan ta kammala haɗa kayan kana ta faɗa ban ɗaki.

Tana shafa mai Ummi ta shigo da kasko mai ɗauke da garwashi da kuma wata ƴar jaka a hannun ta. Ta ajiye kaskon kafin ta fito mata da wani kulaccam da Humrah ta saka ta shafe jikin ta da su kana ta turara mata jiki, ta turara kayan da zata saka.

Sai bayan Isha kafin Abban ya shigo, itama Fauziyyar sai lokacin ta fito cikin dalleliyar lafaya gashi sai tashin ƙamshi take, haka duk inda zata yi yake bin ta da idanu.

Daman an riga an faɗa musu abin da za'a faɗa tun auren su sai dai maimaici, don haka ganin zaƙuwar nashi yasa Abba sallamar su da wur-wuri suka kama hanya.

....
Chapter 26 · 0% Book details