← Book details Reina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 57

Sashe 55

Reina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ta murmusa Kawai, ta manta ne shi bayi zuwa aika sai za'a biya shi, idan kuma baka bashi ba toh zai ɗauka a cikin kuɗin aikan ka.

"Nagode" tace da Salisu alaman yayi tafiyar shi amma hankalin shi a kan mahaifin shi dake suɗe kwanon ɗanwake kaman yana son ya ga maƙerin ta.

Halime ma kallon shi take yi, sun yi da shi a kan zai ci rabi ne ya bar mata rabi saboda tana jin yunwa, kuma ta san mantawa yayi ya cinye don akwai shi da yawan mantuwa.

"Baba sammun" Salisu ya miƙo masa hannu daga nesa yana tsoron ƙarasawa kusa Kamal ya riƙo shi ya lakkaɗa masa na jaki. duk da ya gani babu komai a cikin kwanon samiran amma ko ɗan maiƙon ne shima a ɗan bashi ya lasa.

Mummunan harara ya watsa mishi wanda ya saka Salisu ɗibawa a guje, kafin Kamalu ya fara jan baki saboda yajin da aka baɗa a cikin ɗanwaken ya fi ƙarfin harshen shi.

Cikin hanzari ya sunkumi kwanon kunun da Inna ta gama zuba ma Halime sugar ko gaurayawa bata yi ba, ya saka ludayin ya gauraya da sauri-sauri sannan ya fara sha ba ƙaƙƙautawa.

Taɓe baki Inna tayi tace "Ku kuka fi kusa" sannan ta fita waje ƙarasa wankin da kullum Safiya Halimen ne ke musu tare don ita kaɗai Inna wacce take amarya a gidan ta samu ta haifa kafin mahaifin su ya kwanta rashin lafiya, shi yasa Halime ta tashi da son sauran ƴan uwan ta a ranta, kasancewar ta ita kaɗai a nasu ɗakin.

Bai fi ludayi biyu ya rage mata ba shima don kada ta ga zalaman shi ne, ya ajiye kwanon yana goge bakin shi da bayan hannu, sannan kunun da ya shafu masa a bayan hannun ya goge a jikin afaferan ɗin jikin shi, yana fitar da kakkaurar gyatsa mara daɗin sauraro.

Sai dai idanun Halime dake kan Kamalu babu komai a cikin su bayan so da ƙauna irin wanda Allah ke sanyawa a cikin jini ɗaya.

Kallon babban wa majingina take mishi, kallon shi take yi a matsayin gatan ta, wanda idan yaji daɗi ya samu wadata itama tana da tabbacin zata ji daɗin rayuwa cikin wadata.

"Gaskiya kin ciyar da ni ƴar ƙanwata Allah ya biya ki" yace tare da miƙewa zai tafi kasuwa, tana mishi addu'ar Allah ya tsare ya bada kasuwa mai albarka, ba don raunin ta ba ma da rakiya zata yi mishi har ƙofar gida kaman matan da ya ajiye har guda biyu basu isa ba.

......

Gidan su yana da girma sosai, domin mahaifin su babban manomi ne kuma ya ɗan taɓa tashen kuɗi a lokacin su, don haka ya yanki ƙaton fili ya zagaye shi, a hankali ya dinga tada gini sashe-sashe sai ya saka ƙannen shi ko ƴan uwa a ciki idan kayi naka sai ka tashi wani ya shiga.
Haka har yaran shi suka tasa suka fara aure wurin zama bai zamo musu matsala ba, sai dai yanzun da mahaifin ƙarfin shi ya ƙare ɗan abinda ya tara ma yana niman ƙarewa a kan jinyar shi, sai aka ɗauki manyan gonakin da yake da su aka yanka mo kowa fili ya shuka abinda zai ci da iyalan sa ya siyar da saura.

Kasancewar Jama'are suna daga cikin wuraren da Allah yayi ma ƙasan su albarka, girbi tana yin kyau sosai musamman ta shinkafa.
Sai dai cikin masu noman nan babu Kamalu, wanda shi kaɗai ne mai zalaman mata biyu duk cikin ƴan uwan shi duk da bayi da halin riƙe su kuwa. Ya nemi wanda ya karɓi hayan gonan kana da kuɗin ya je ya kama shago a bakin kasuwa don shi yana ji a jikin sa arziƙin shi na cikin kasuwanci ba noma ba.

.....

A sannu lokaci yake tafiya ma Halime mai karaya tana zaune a gida sauran sa'annin ta suna zuwa makaranta har aka zo zana jarabawar gama primary bata koma ba, haka suka zana suka bar ta, kuma daga nan shikkenan babu ƙarawa gaba sai dai aure. daman kuma karatun ba daga farko ta fara shi ba, don sai da mahaifin ta ya kwanta jinya kafin mahaifiyarta ta rufe Ido ta saka ta a primary 2 lokacin, ta kasance mace ta farko a gidan da ta fara zuwa makarantar boko.

Yanzu tana da shekaru 14, tsarar ta sun fara tsaida mazajen aure amma ta so ko da certificate ɗinta na primary ta riƙe, tunda ci gaban da take so ba mai yiwuwa bane. Shima yanzu Kamalu yayi mata sanadi sai ta maimaita ajin ƙarshe.

Da ita da mahaifiyar ta masu lura ne da sun fahimci tun fara jinyar ta sau ɗaya Kamalu ya kawo mata kaza guda ɗaya aka yi mata farfesu ya zo suka shanye tare, amma ko Naira 10 ya fahimci halime tana da shi sai ya roƙeta ta bashi aro zuwa ya fita yayi ciniki, kuma ba zai taɓa biya ba idan ba ta cire kunya bane ta tambaye shi.

Ba wai don tafiyar tayi daidai ba, sai don kawai ɓangare ɗaya ke nuna ƙauna Saboda Allah, ɓangare ɗaya ke bada yarda, ta aminta ana tauye ta don kawai tana tsoron warwarewar alaƙar da ɓangare ɗaya ne kawai ta ƙulla ta, don tana jiyar da ɗaya bangaren daɗi shi kaɗai.

Amma ƙaunar dake tsakanin Halime da Kamalu ta zama gaban kwatance ma duk wasu ƴan uwa dake Jama'are, mutanen da ke zagaye da su kuma gani suke yi babu mai moran Kamalu sai Halime shiyasa take son shi haka. A wannan dalili ta fita kan matan shi masu ganin su da hakkin su yake wuyan shi fama suke yi amma ya je ya buɗe bakin aljihu ma wata Halime, shiyasa da ta karye ko ita uwar kalabun bata iya zuwa ta duba ta ba, sai aikan shinkafa da mai can ƙasan roba da tayi mata sau biyu.

Bata fita daga wannan jarabawar ba rana ɗaya suka wayi gari Allah yayi ma mahaifin su rasuwa. Mutuwar sosai ya taɓa Halime kasancewar ita da mahaifiyar ta ne a jikin jinyar mahaifin su, ta saba da shi sosai.

A kwana na huɗu da rasuwa rikici ya tashi a kan gado. Ƙannen Kamalu suka tashi zasu dake shi sai da aka shiga tsakani saboda umartan su yayi da zasu bar gona an samu wanda zai siya har da shukan su dake cikin ƙasa sai a raba kuɗin.

Aka yi ƙoƙarin danne shi dole ya haƙura zuwa lokacin da suka girbe hatsin su sai a raba gado mai niyyan siyarwa ya siyar.

Washegari sai gashi da masu ganin gona, ya ɗaura aniyar sai ya siyar duk abinda zai faru ya faru tun da takardan su na hannun shi. Ganin za'a yi biyu babu aka yi rabon gado a take, sannan aka ce mai siyan gona sai ya bi masu ra'ayin siyar masa idan zai iya haƙurin sai sun yi girbi kafin ya karɓa.

Duk cikin su babu wanda yake da ra'ayin siyarwa tun da yana biya musu buƙatun su na yau da kullum har da ƙari, sai Kamalu kawai da kuma Halime da ya lallaɓata ta bashi nata kason ya haɗa ya siyar.

Ta sha mamakin ganin zunzurutun kuɗi har dubu ɗari uku a gaban ta, Kamalu ya ajiye. Dubu ɗari uku da hamsin aka siya amma ya riƙe hamsin ɗin lada.

Haka suka ɗauki wani dubu goma suka damƙa mishi kuma babu kunya ya saka hannu ya karɓa.

Ƴan uwan Mahaifiyar Halime suka shawarce ta a kan ta fara yiwa halime kiwo da dukiyar ta ko ta bayar ana juya mata saboda ajiyan kuɗi haka hatsari ne. Ta kuwa aminta da shawarar nan aka siyo shanu har da raguna da kaji aka saka a ɓangaren da ya shiga gadon su biyun a cikin gidan.

Shi kuwa Alhajiji Kamalu kwanan mahaifin shi 50 a cikin ƙasa ya ƙaro aure a karo na uku, yarinya kyakkyawa har halime ta bata shekara guda. Sannan sauran kuɗin ya shiga wani kasuwancin da shi, yanzu har cikin Bauchi yake kai bandan kifi.

A can ne ya haɗu da wasu da suka yi masa alƙawari zasu dinga karɓan kaya a wurin shi suna fitarwa ƙasashen da muke maƙwaftaka da su Amma kuma wanda yake kawowa yayi kaɗan sai ya ƙaro.

A fujajan ya koma gida ya saka ɓangaren da iyalan shi ke zaune a kasuwa, ganin yana matse aka mishi tayin wulaƙanci, bai damu ba saboda ya san arziƙin shi ne yake kusa, don haka ya zuba kuɗi ya sayi kaya ya bawa mutane suka yi tafiyar su.

Daman shi kaɗai yake hidiman sa, don haka ko da asarar ta hau shi Allah sarki kawai suka yi mishi. Gashi ya rasa muhalli don lokaci ɗaya mai wuri zai iya buƙatar ya tattara ya tashi, gashi ba kuɗi babu kadara ga amarya dake da ciki haihuwa yau ko gobe.

Kamalu sai da yayi ciwo kaman ba zai tashi ba.
Babu daɗewa amarya ta sintimo ɗan ta namiji aka raɗa mishi Ɗahiru da ragon da Kamalu ya ara cikin garken Halime, ta bashi ba tare da wata damuwa ba duk da ta sani ba Lallai ya biya ba amma cikin ranta ta saka ta bar mishi kyauta domin idan yayi kuɗin da yake faɗan nan zasu ji daɗi dukkan su.

A koda yaushe idan suka zauna labarin irin kuɗin da zai yi yake bata ita kuwa bata gajiya da sauraron shi cike da alfahari.

A yanzu ma suna zaune ne yana cin alalen da ta siyo masa da zata zo duba shi, hannu baka hannu ƙwarya yake magana, ko tauna alalen baya yi yanda sulɓin ta yasa wucewa kawai yake yi, ga yajin ya ji farin maggi.

"Hmm ..shh... Halime Kinga masu kuɗin nan daga kiji ɗan tata sai ɗan gwate, toh nima ɗan ƙanzo ko ɗan alale zan zama"

Santin alale ne Halime ta sani, don haka ta murmusa kawai.

Ƙanwar shi talatu da ta ɗaga labule ta shigo tace "ko ɗan yaji ba! Ji yanda kake faman jan baki kamar mace Yaya"

Ta ɗaga labulen yanda haske zai daɗa wadatan ɗakin kafin ta nemi wuri ta zauna tana share mummunan kallon da yake watsa mata ta dubi Halime.

"Wato Halime tsugudidi ya zauna yana lallaɓaki ki bashi gadon ki ko?"

~~~~~~~~~~~
Chapter 55 · 0% Book details