← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 118

Sashe 99

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sadik ne ya buɗe musu ƙofar part ɗin suka shiga bakunan su ɗauke da Sallama, kan Neehal a ƙasa, da ƙyar take iya d'aga ƙafarta, sosai take jin wata irin kunya tun ba ta yi tozali da surukan nata ba. A ƙasan carpet suka zauna dukan su. Afrah tana kallon falon ta ce "Uncle Sadik gidanka ne nan?" Ya kamo hannunta yana murmushi ya ce "Gidanmu dai ni da my Family ne." Neehal ta janyo ta tana hararar ta, ta zaunar da ita a gabanta. Sadik ya zauna a kusa da ita ya ce "Me tay miki kuma?" Kamar zata yi kuka ta ce "Ni dai ka tashi daga kusa da ni dan Allah kar Maamah ta fito." Ya tashi yana mata dariyar tsokana, sannan ya nufi ɗakin Maamah. Tare suka fito shi da Batul da Maaman, cikin fara'a Batul ta tarb'e su, suka gaisa. Maamah ma da fara'a ta zauna a Falon, suka gaishe ta cikin girmamawa. Daga yanda kan Neehal yake ƙasa Maamah ta gane ita ce sirikar ta_ta, and 100 💯 ta yaba da ita a matsayin surukarta. Batul ta cika musu gaban su da kayan ciye_ciye da na sha, wanda aka tanada domin su. Maamah ta ja su Afrah ɗakinta dan yaran sun burge ta ba kaɗan ba, gashi ba su da wahalar sabo. Maryam da Salma ne kawai suka ci abubuwan da aka kawo musu, amma Neehal ƙin ci ta yi, duk da Maamah ta bar falon, Batul ma korar ta Sadik ya yi duk dan Neehal ta sake amma ta ƙi sakin jikinta. Sadik ya dawo kusa da ita ya zauna ya ce. "Ki ci abincin mana Wifey, Maamah fa da kanta ta yi girkin nan musamman dan ke, ko in baki a baki?" Ya ƙarashe zancen da kashe mata ido. Ta harare shi dama ciki take da shi, ya nuna wa Maamah ita sai ka ce haka aka ce masa ana yi. Da ƙyar ta kurb'i juice ɗin da ya zuba mata a cup, ganin yanda ya wani marairaice mata. Kafin su tafi Abban Sadik da yake yana gari ya zo sun gaisa cikin fara'a da nuna jin daɗin ganin su. Umma ma ta zo sun gaisa ita ƴaƴanta ƴan'mata guda biyu, su kay ta satar kallon Neehal kuwa, amma duk kallon nasu ba su ga makusa a jikinta ba. Sai kusan Magriba suka tafi, Maamah ta sa Batul ta juye musu Gaba-ɗaya sauran kayan ciye_ciyen da suka bari, Abba kuma ya bawa su Afrah kuɗi wanda da farko ƙin karɓa su kay, sai Sadik ne ya karɓar musu. Sosai Abba ya yaba hankali da tarbiyya gami da kunyar Neehal. Suna fita Batul ta ce, "Gaskiya Yaya ya iya zaɓen mata, mai kyau da kunya." Maamah ta yi murmushi cikin jin daɗi, Umma kuwa tab'e baki ta yi. Gidan Aunty A'isha Sadik ya mayar da su, bayan ya shigar musu da kayan ciki, Neehal ta rako shi bakin Mota tana ɓaɓɓata fuska. Ya shiga cikin motar, amma ya bar murfin a buɗe ya ce mata, "To ba mun baro gidan Maaman ai, ki saki jikinki mana." Ta turo baki ta ce "Ina ruwanka da ni, ai mun ɓata." Ya marairaice ya ce "Ni ɗin Wifey, Please ki yi haquri na tuba." Ya ƙarashe zancen yana haɗa hannunsa biyu guri ɗaya. Ta kalli fuskarsa wadda take bayyana farincikin da zuciyarsa take ciki a yau. Ta ce "Sanda ka bani kunya a gaban su Maamah ai baka san da haqurin ba." Da ƙyar dai ya lallaɓa ta, ta haqura suka yi sallama. Bayan ya mata godiyar zuwa gaishe da su Maamah. Ana yin Sallar Magriba suka bar gidan Aunty A'isha, saboda Salma da zata wuce gida. Suna zuwa gida Salma ta fara bawa Mama labarin irin kyakkyawar tarb'ar da suka samu a gidan su Sadik, Mama ta ji daɗin hakan sosai. Salma bata jima ba ta tafi bayan Mama ta cika ta da Alkhairi, Neehal ma ta bata turaruka da sabbin undies.

Ranar Sunday kamar yadda Ahmad ya faɗa da hantsi ya sauka a Kano a gidan Mama. Neehal tana bacci su Afrah suka tashe ta cikin murna. Ta tashi da ƙyar dan bata jima da kwanciya ba, suka sanar mata Daddy ya zo. Sai ta ji gabanta ya faɗi, dan har yau ba su kuma magana da shi ba, tun ɗan chat ɗin nan da sukay ta message. Ta tashi ta shiga toilet ta wanke baki da fuska, sannan ta fito ta ɗauki Hijabi ta fice. A falon sama ta gan shi yaransa a jikinsa suna masa surutu. Ta zauna akan carpet kanta a ƙasa ta ce "Sannu da zuwa Uncle." Ya d'ago ya dube ta cike da d'okin ganin ta, ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani sanyi na ratsa zuciyarsa. Sauke su Afrah ya yi daga jikinsa ya ce su tafi gurin Mama, sannan ya sauko daga kan kujerar da yake ya zauna a kusa da ita. "Princesss!" Ya kira sunanta a hankali. Ba tare da d'ago kanta ba ta ce "Na'am." Ya lumshe ido ya buɗe ya sauke su akan fuskarta ya ce "I missed you so much." Ta d'ago ta kalli fuskarsa itama saboda azalzalar da zuciyarta take mata akan hakan, ta yi murmushi ba ta ce komai ba. Ya tallafi fuskarsa da hannunsa ɗaya ya ce, "Wow, Princess kin ƙara kyau, Please karki daina mun wannan murmushin." Kamar zuga ta ya yi sai ta ɓata rai tare da ɗauke kanta daga gare sa. Cikin damuwa ya ce "Why Princess?" Ta turo baki ta ce "Babu komai." Ya ce "No, akwai Princess, tell me what happened? Bana son na gan ki cikin damuwar nan." Ta yi shiru, ya kamo hannunta ya ce "Please." Ta k'wace hannunta ta ce "Ba kai ne ka daina kula ni ba, yanzu ma na san dan su Afrah ka zo ba dan ni ba." Ya yi shiru yana kallonta, yana tunanin abun da yasa yay mata hakan ko kuma ya ce sukai wa juna." A hankali ya ce "Ke kika fara daina kula ni Princess, idan baki manta ba ranar dana tafi na kira ki da daddare Twins suka ɗauka, nay ta jiran kiran ki idan kin dawo tunda sun ce mun ba kya nan, amma baki kira ni ba, dana kira da safe kuma sai na ji Twins ne suka ɗauka again. That is why na ƙyale ki, may be haka kike buƙata, i thought ina takura miki ne. But I'm sorry." Sai ta ji bata kyauta masa ba, amma ita kunyarsa ce tasa ta yi haka, yanzu ma kawai daurewa ta yi har ta iya kallon sa bisa tilastawar zuciyarta. Ta marairaice ta ce "Ka yi haquri Uncle." Ya yi murmushi ya ce "Babu komai Princess, Princess bata taɓa laifi a wajen Uncle ɗinta." Cikin shagwab'a ta ce "Kuma ni baka takura mun ba." Ya ce "To me yasa kika daina kula ni?" Ta juyar da kai gefe ta ce "Kunyar ka nake ji, ban san ta yaya zan maka magana a time ɗin ba." Ya matso ya juyo da fuskarta ya ce "Let me hug you, sai ki daina jin kunya ta." Ta ja baya da sauri kamar zata yi kuka ta ce "Ai na daina since." Ya yi murmushi yadda duk ta tsorata ya ce "Shikenan, amma idan kika ƙara mun haka, i know what I do." Ta kawar da zancen da faɗin, "Ya su Ummi?" Ya ce "Suna nan k'alau, Mamy ta ce "Kun je gidanta jiya." Ta ce "Uhm." Sai kuma ta shagwab'e fuska ta ce "Wai dagaske tafiya zaka yi da Twins yau?" Ya ce "Eh mana, Gobe za su yi resuming School, hutun nasu babu yawa 2 weeks ne kawai." Ta ce "Shikenan, but i will miss them." Ya ce "Ki bi mu, mu tafi tare." Ta ce "Soon, Insha Allah zaku ganni, Relatives ɗin Dad ma suna ta complain bana zuwa." Ya ce "I was so surprise fa, ace kin zauna a Abuja for some years amma Allah bai taɓa haɗa mu ba." Ta ce "To ai bana fita, daga gida sai School, in kuma zan fita tare da Mama ne." Ya ce "Haka ne, Mummy's girl." Sai ta yi murmushi, ta tuno Ameen saboda shi yake yawan faɗa mata haka. Sai bayan Azhar suka tafi suka bar Neehal cikin kewar su, su ma yaran kuka suka saka da za su tafi, wai sai da ita za su tafi. Da ƙyar Ahmad ya lallashe su ya ce zata biyo su itama soon.

*One week later*

Ranar Friday da safe Mama tana gyaran part ɗin Daddy Ameen ya kira ta a waya, ta ɗauka suka gaisa, daga yanda ta ji muryarsa ta san ba k'alau ba. Ta ce "Ya jikin Hafsan?" Cikin damuwa ya ce "Muna asibiti Mum, ta yi Miscarriage." Mama ta ce "Subahanallahi, yaushe?" Ya ce "Cikin daren jiya." Cikin jimantawa da damuwa Mama ta ce "Allah ya bata lafiya, yanzu tana ina?" Ya ce "Hospital." Mama ta ce "Wanne?" Ya faɗa mata wani private Hospital ne dake kusa da su." Mama ta ce "Bari ta shirya ta zo." Daga haka su kay sallama. Ta kira Daddy ta faɗa masa, sannan ta ƙarasa aikin da take cikin sauri ta shirya ta tafi ita kaɗai, tunda Neehal tana wurin aiki.
Chapter 99 · 0% Book details