Sashe 13
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Haka a ka ci gaba da zaman makokin mutuwar Anwar, Neehal kullum su na zuwa gidansu Anwar da safe sai dare suke tafiya har a ka yi sadakar uku, daganan kuma bata Æ™ara komawa ba saboda ita ma ana zuwa gida yi mata gaisuwa, sai ranar sadakar bakwai suka kuma komawa. Yau Juma'a wanda ya kama kwana goma sha biyu da rasuwar Anwar, zuwa yanzu Neehal ta sakawa zuciyarta dangana game da rashin da ta yi, Anwar ya riga ya tafi ya zama tarihi addu'ar su kawai yake buÆ™ata, duk da wani lokacin ta na damuwa sosai har ta zauna ta yi ta kuka, Mama,Dad, Haneefah sune 'yan rarrashin ta da bata baki gami da nasihohi, Ameen ma yanzu wata kulawa yake bata ta musamman saboda tausayi take basa sosai, ta zama wata so silent wannan rigimar da neman magana gurin Mama duk ta daina, Magana ma ba sosai take yinta ba, ga rama da ta yi. Misalin Æ™arfe Biyar na yamma Neehal ta na zaune a falon Æ™asa ita kaÉ—ai ta na kallon Sunna TV, gani ta yi Dije mai aiki ta fito daga dakinsu da sauri, ashe Æ™arar bell ta ji, ita ba ma ta ji ba ta na can duniyar tunani. Dije ta na buÉ—e door d'in ta ga kanwar Dad ce ta zo tare da 'yarta, hanya ta ba su ta na musu sannu da zuwa cikin girmamawa, Matar ce kawai ta amsa mata a wulak'ance amma 'yarta ta ko kallon ta ba ta yi ba, ta wuce ciki ta na taunar cingum Æ™as_Æ™as ga takalmin Æ™afarta mai shegen tsini sai Æ™ara yake a kan tiles É—in falon, k'amshin turarenta mai hawa kai ya cika falon, fara ce tass kamar ka tsaga jikinta jini ya fito amma gajeriya ce ta na da madaidaicin jiki, ta na sanye da wata doguwar riga 'yar kanti, ta yafa mayafi kalar rigar kanta babu É—ankwali sai fuskarta da ta sha uban make up. Neehal ta bita da kallo fuskarta ba yabo babu fallasa, ita kuwa wani matsiyacin kallo take bin Neehal É—in da shi. Neehal ta yi É—an murmushi ta ce "Sannunku da zuwa Aunty Hamida" kamar ba ta ji ba, ta yi banza da ita, Neehal dama ta san za'a rina, duk da kasancewar Hamida 'yar gidan k'anwar Dad ce amma ba sa shiri ko kaÉ—an, ko dan hakan ya samo asali ne daga rashin shirin Mahaifiyar Hamidan da Mama ne?. Neehal ranta ya É“aci a kan abin da Hamida ta mata, dama shi ya sa bata son shiga sabgarta, Mama ce ke tursasa ta dole, ta rasa me ta yi wa Hamidan ta tsane ta over. Hamida ta zauna ta na kar kaÉ—a Æ™afa, Mahaifiyarta wadda suke k'ira da Mumy ta Æ™araso cikin falon ta zauna ita ma ta na huhhura hanci, Neehal ta dube ta ta ce "Sannu da zuwa Mumy ina yini?" Ta mata wani kallo ta ce "Lafiya k'alau, ya hak'uri kuma?" Neehal ta ce "Alhamdulillah." Daga haka suka yi shiru, Neehal ta maida hankalinta a kan kallon da take, bayan wasu mintuna Mama suka sakko ita da Hajiya da Dije da ta je kiranta. Ba yabo ba fallasa Mama ta ce "Sannunku da zuwa" Mumy ta ce "Yawwa" Mama ta ce "Ya gida Suwaiba?" Mumy ta ce "Lafiya k'alau" Mama ta ce "Masha Allah" tare da zama a kan kujera, Hajiya ma ta zauna. Hamida kamar ba ta so ta ce "Ina yini Mama?" Mama tace "lafiya k'alau, Hamida ya aiki" tace "Fine." A taÆ™aice. Hajiya kuwa yadda ba su mata magana ba, itama ba ta musu ba, TV kawai take kallo hankalinta kwance. Su Dije suka dawo falon da ruwa da lemo gami da drinks, Zulai ta gaishe su kamar yadda Mumy ta amsa wa Dije haka ta amsa wa Zulai a wulak'ance. Can dai Mumy ko me tuna sai ta dubi Hajiya ta ce "Ina yini Hajiya?" Hajiya ta ce "Lafiya" tana keb'e fuska, Hamida da ke ta latsa wayarta ita ma ta gaishe ta a yangance. Mumy ta gyara zama ta dubi Mama ta ce "Sai muka ji kuma an kashe saurayin Neehal kuma" Mama ta ce "Eh Æ™addara ta riga fata." Mumy ta ce "To Allah ya ji k'an shi, amma ni fa ina ganin wannan abun kamar da sa hannu, a ce yarinya duk wanda maganar aure ta shiga tsakaninsu sai an kashe shi, sai ka ce film ko labaran tatsuniya?" Mama ta yi shiru ba ta ce komai ba, domin da rainin hankali Mumy ta yi maganar. Hamida ta tab'e baki ta ce "Hmmmm gaskiya dai Mumy, dan Ni na ma fi tunanin ko wani baÆ™in Aljanin ne ya aure ta, shi ya sa yake duk wanda za ta aura.........âœï¸
[7/21, 9:00 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
_By_
_Zeey Kumurya_
0ï¸âƒ£9ï¸âƒ£
A fusace Hajiya ta dubi Hamidah ta na mitsi_mitsi da ido ta ce "Ke! Ki iya bakinki, mugun nufinki Insha Allahu ba dai a kan Neehal ba, ato, bakinki ya sari ɗanyen kashi" Hamida za ta kuma magana Mommy ta girgiza mata kai, tab'e baki ta yi ta ci gaba da latsa wayarta a gadarance, Mama kuwa kamar ba ta ji su ba, ta musu banza. Neehal ma ko d'aga kanta ba ta yi ba, balle ta nuna ta san me su ke cewa. Hakan kuwa ba ƙaramin k'ona ran Mommy ya yi ba, domin kuwa ta so Mama ta kula ta su yi ta yi, ko kuma Neehal ta tankawa Hameedah Dad ya dawo ta haɗa mata sharri, sai kuma ba ta samun haɗin kai ba. Mama tashi ma ta yi ta wuce sama abin ta, Neehal ma bin bayanta ta yi dan zaman falon ya ishe ta. Hakan kuwa ya ƙara kona ran Mommy. Ɗakin da suke sauka idan sun zo Mama ta sa su Dije suka gyara musu, da yake daga Abuja suke a can suke da zama, su Dije suka kwasar musu kayansu zuwa d'akin. A gadarance su Mommy da Hameedah suke yin komai a gidan, Mama kuwa ba ta tanka musu haka ma Neehal, Hajiya ce ma sarkin magana, amma Mama ta roƙe ta a kan ko me za su yi kar ta kula su. Ko da Dad ya dawo part d'insa suka je su na hira, har sai da dare ya yi sosai sannan ya ce ya kamata su je su kwanta, Mama kuwa dama ta san hali shi ya sa ba ta je ba, sai da ya kira ta da kansa a waya. Washegari Neehal tun safe ta wuce gurin aiki, dama tun ranar mutuwar Anwar ba ta koma ba sai yau.