← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 118

Sashe 106

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana gama cin abincin ta ɗauki wayarta ta kunna data, ko 5 minutes ba ta yi da ɗaukar wayar ba kiran Ahmad ya shigo. Ta yi murmushi sannan ta d'aga ta kara a kunnenta, muryar su Afrah ta ji a maimakon ta Ahmad, suna kiran sunanta cikin karaɗin su. "Aunty! Aunty!" Ta ce "Na'am, Yaran kirki dafatan kuna lafiya?" Amrah ta ce "Lafiya k'alau Aunty." Ta ce "Ina Ummi da Aunty Zahra da Abba?" Suka ce "Suna gida." Ta ce "To ku gaishe su." Suka shiga yi mata hirar makarantarsu da bata labarin kayan wasan da Daddy ya siyo musu. Ta ce "Lallai ƴan gatan Daddy, ina Daddy'n yake?" Amrah ta ce "Gashi nan a kwance, bashi da lafiya." Cikin damuwa ta ce "Bashi da lafiya kuma, me yake damunsa?" Ahmad dake kwance yana sauraren su ya tashi zaune tare yi musu alamar su kawo masa wayar. Amrah ta ce "Ya tashi Aunty, ya ce na bashi wayar." Yarinyar ta miƙa masa wayar, ya karɓa ba tare da ya cire ta a speaker ba ya ce "Princesss.!" Cikin kasalalliyar murya. Ta ce "Na'am Uncle, meke damun ka?" Ya sauke numfashi ya ce "Babu komai." Cikin shagwab'a ta ce "Please Uncle ka faɗa mun, hankalina gaba-d'aya ya tashi da aka ce mun baka da lafiya." Ya ce "Ba ciwo nake ba Princess, kawai ina jin wani iri a cikin zuciyata kamar zan rasa ki." Ta yi shiru ba ta ce komai ba. Twins dake kallon sa suna sauraren su duk da ba fahimta suke ba, Afrah ta ce "Daddy Aunty ta yi shiru, ko ta kashe wayar ne?" Ya ce "A'a bata son magana da ni ne, Aunty ku kaɗai take so bata so na." Yarinyar ta waro Ido ta ce "Tana son ka Daddy." Ya ce "No, ask her" Yarinyar ta ɗauki wayar da sauri tare da ɓata fuska ta ce "Aunty wai bakya son Daddy'n mu?" Amrah ta tari numfashin ƴar'uwarta da sauri da faɗin "Daddy yana da kirki fa Aunty." Neehal ta sauke numfashi tare yin murmushi domin ta gane wayo Ahmad ya shirya mata. A hankali ta ce "Ina son Daddy sosai Yarana, wasa yake muku." Ahmad ya lumshe idonsa tare yin wani sassanyan murmushi, duk da ba direct shi ta faɗa wa tana son shi ba amma kalmar ta doki zuciyarsa. Afrah ta kama hannunsa ta ce "Daddy Aunty ta ce tana sonka." Ya girgiza kai ya ce "Ai bata faɗa mun ba, ku ta faɗa wa." Cikin shagwab'a Amrah ta ce "Aunty please ki cewa Daddy kina son shi, tunda kina son mu ai kina son Daddy'n mu ko?" Ta ce "Eh mana, bawa Daddy wayar za mu yi magana da shi." Ya karɓa ya cire ta a speaker sannan ya kara a kunnensa ya ce "Uhm? ina jin ki." Ta ɓata fuska kamar yana ganin ta, ta ce. "Uncle meke damun ka?" Ya ce "Babu komai sai son ki Princess." Ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba. Ya yi ƙasa da murya ya ce "Princess please ki ce kina so na, baki taɓa faɗa mun ba fa." Ta ce "Gashi nan kai ka faɗa, kuma already ka san ai ina s....." Sai kuma ta yi shiru. Cikin zak'uwa ya ce "Please Princess say it, ko zan ji daɗi a raina." Ta lumshe ido cikin shauƙi tare da yin ƙasa da murya sosai ta ce "I Love You Doctor Ahmad!" Sai kuma ta yi saurin zare wayar daga kunnen ta, ta yi hanging up. Sai jin ɗil ya yi alamun ta kashe wayar. Ya yi murmushi cikin tsananin farinciki ya ajiye wayar a gefen sa, sai ya tuno lokacin da tana ƙarama da ya ce mata I love You, ta ce "Love You too Uncle." Ya janyo ƴaƴansa da suka fara wasan su da sabbin teddy's ɗin da ya siyo musu ya rungume su a jininsa ya ce "Aunty ta kusa dawowa nan gidan mu zauna tare da ita." Yaran suka waro suka ce "Daddy When?" Ya ce "Soon Insha Allah." Sai suka bar jikinsa suka fara murnar Aunty zata dawo gidansu." Ahmad ya bi su da kallo yana tunanin farincikin da kids ɗinsa za su yi idan ya auri Neehal, da shi da su suna buƙatar ta a cikin rayuwar su, yaran suna sonta sosai dan har mamakin hakan yake, dan yanzu komai za su yi sai sun ambaci sunan Aunty, in unguwa suka ce suna dawowa za su je akira musu Aunty su bata labari, idan makaranta ce ma haka ne. Ya koma ya kwanta tare da janyo pillow ya rungume a ƙirjinsa gami da lumshe idonsa. A daa ya bar Neehal ta ƙarasa school ɗinta kafin ya tura a yi maganar auransu, amma a yanzu sai yake ganin kamar ba zai iya jiran watannin da suka rage mata ba ta ƙarasa karatun, ba tare da ya mallake ta a matsayin matarsa ba. A ɓangaren Neehal itama lumshe ido ta yi ta kwanta a jikin a kujera bayan ta katse wayar da murmushi ɗauke akan fuskarta. 'Uncle rigima.' Ta faɗi haka a ranta. Ƙarar shigowar text message cikin wayarta yasa ta buɗe ido ta ɗauki wayar ta duba, kamar yadda ta zata shine yay mata text ɗin, ta shiga karantawa a zuciyarta kamar haka. _Thank You so much Princess, kin saka ni farinciki sosai, I love you_ Ta yi murmushi ba tare da ta yi masa reply ba ta tashi ta haye upstairs.........✍️
[8/7, 9:21 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*

_By_
_Zeey Kumurya_

*5️⃣7️⃣*

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*

Bayan Sallar Magriba Neehal tana zaune a falon ƙasa tana sauraren karatun Alkur'anin dake tashi a cikin speaker, wanda ta yi connecting ɗinsa da wayarta. A hankali take bin karatun idanunta a lumshe. Ameen ya buɗo ƙofar falon ya shigo tare da yin Sallama cikin kamilalliyar muryarsa. Bata ji sallamar ba ma hankalinta yana kan karatun, har ya nemi guri ya zauna, k'amshin turarensa ne ya fargar da ita zuwan sa. Ta buɗe idonta da sauri tare da tashi daga kishingid'en da take. Ta waro Ido cikin murmushi tana kallon sa, kamar yadda shima yake kallon ta. Ta tsayar da karatun, sannan ta tashi ta koma ta zauna a kusa da shi. A hankali ta ce "Ina yini Yaya." Ya ce "Lafiya k'alau." Ta ce "Ya Aunty Hafsah?" Ya ce "Tana nan k'alau." Ta murmusa ta ce "Yaya na ga sak'on ka, thank you so much, Allah ya ƙara buɗi mai albarka." Ya lumshe ido ya buɗe a kanta ya ce "Amin." Ta miƙe tare da faɗin, "Bari na kira Mama." Bai ce komai ba har ta haye upstairs. Ta shiga ɗakin Mama da sallama, Mama dake shiryawa ta amsa mata, ta ce "Mama Yaya ya zo, yana ƙasa." Mama ta ce "Okay ina zuwa." Ta juya ta koma ƙasa ta zauna a kusa da shi, ta shiga aikin kallon sa, shi kuma yana ta aikin latsa waya. Sai ta ga kamar ƙara kyau yake, ko dan ƙarshe ne shi a iya wanka da iya ɗaukar dressing. Ta kalli bak'ar sumar kansa wadda daga gani babu tambaya ba ƙaramin kuɗi ake kashe mata ba. Ta lumshe ido a ranta tana faɗin 'Ba a ƙasa ya ɗauki gayu ba, dan Mama ƙarshe ce itama a wannan fannin. Mama ta shigo falon tare da faɗin, "Neehal ki kawo masa abinci mana." Ta miƙe tare da amsawa ta nufi kitchen ɗin. Mama ta zauna a kujerar dake fuskantar sa, fuska a sake ya ce "Ina yini Mum." Mama ta ce "Lafiya k'alau, ya Hafsah?" Ya ce "Tana nan k'alau." Mama ta ɗan ƙura masa ido na wasu sakanni sannan ta ce "Ameen! Kana lafiya kuwa?" Ya ce "Komai lafiya Mum, me kika gani?" Mama ta ce "Kamar akwai abin da yake damun ka." Ya yi murmushi ya ce "Nothing Mum, idan ma da akwai wani abu yanayin aiki ne kawai." Mama ta ce "Allah ya taimaka ya bada sa'a, sai a cigaba da dagewa da addu'a." Ya ce "Insha Allah." Dai-dai lokacin Neehal ta fito daga kitchen ta ajiye tray a gabansa, ta tsugunna dan serving ɗinsa, Mama ta dakatar da ita da faɗin. "Barshi Daughter, je ki gyara mun bedroom zan zuba masa." Ta ce "Toh Mama." Tare da nufar sama. Mama ta sakko ta zuba masa abincin a plate, ta dube shi ta ce "Sakko ka ci, kuma kar ba ni wani excuse ko ka ce ka ƙoshi." Ya yi murmushi tare da saukowa ya zauna a kusa da ita, ya jawo abincin gaban sa ya ce "Yaushe da rabon da ki yi serving ɗina Mum?" Mama ta harare shi ta ce "Kasan jariri ne ai kai, da sai na zuba maka abinci zaka ci." Ya yi murmushi ya ce "Kafin ki samu Daughter ai kina mun, tunda kika yi ƴa kika daina yayi na." Mama ta yi murmushi ganin yanda ya wani marairaice ta ce "Au har wani daina yayin ka na yi?" Ya lumshe kyawawan idanunsa ya buɗe ya ce "Eh mana." Mama ta ce "Never Ameen, ai babu wani abu da zai yi replacing ɗinka a zuciyata, kai ɗin ne sometimes nima ba gane kanka nake ba." Ya yi murmushi bai ce komai ba sannan ya yi Bismillah ya fara cin abincin sa. Mama ta bishi da kallo cike da k'auna, a ranta tana ƙara jinjina zurfin ciki da ɓoye abu irin nasa." Ta yi zaton idan ya yi aure zai rage, amma sai ta ga jiya i yau, kamar ma ƙara masa a kay. Kaɗan ya ci abincin ya ajiye spoon ya ce ya k'oshi, sannan ya sha ruwa yay mata sallama ya tafi. Mama ta tattara kayan ta kai kitchen bayan ya fice.
Chapter 106 · 0% Book details