Sashe 109
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
A falon sama ta tarar da Mama tana kallo. Ta tafi da murnarta ta faɗa jikinta tare da faɗin. "Oyoyo Mamana." Mama ta harare ta, ta ce. "Aina na ɗauka a can zaki kwana." Ta ƙara ruk'unk'ume ta tana murmushi ta ce "Sorry My Mum, hira ce ta yi daɗi." Mama ta ce "Ya yi kyau, idan da Daddy ya dawo sai ki faɗa masa hira ce ta yi daɗi shi ya sa kikai dare." Ta yi dariya kawai, Mama ta ce "Ya kika baro Haneefan?" Neehal ta ce "Lafiya k'alau, tana gaishe ki." Mama ta ce "Ina amsawa." Neehal ta miƙe ta shige ɗaki. Kwanciya ta yi akan gado bayan ta ajiye handbag ɗinta da mayafinta. Ta kwanta rub da ciki tare da tallafe kanta da hannunta. Tunanin Ahmad take da irin tarin soyayyar da yake mata, har yanzu ta kasa amincewa da zaɓin da ta yiwa kanta, tana ganin kamar ba za ta iya barin Ahmad ba a rayuwarta. To amma Sadik fa, kamar yadda Haneefah ta faɗa idan ta bar shi ta zalunce shi, ta cuce shi ta yaudare shi. Ta runtse ido cikin tsananin damuwa, ita ba ta taɓa dating samari biyu a lokaci ɗaya ba sai wannan karon, ta yi dana sani mara iyaka, amma kuma babu yanda zata yi wannan ma ta san wata jarabawar ce daga Allah . Ta tashi ta ɗauko jakarta jin wayarta na ringing a ciki, Sadik ne yake kiran ta. Ta d'aga cikin ƙoƙarin ganin bai fuskanci tana cikin wata damuwa ba, gaisawa kawai sukai ya tambayi lafiyarta saboda lokacin Sallah da ya gabato. A daren ranar ta sanar da Mama Sadik ta zaɓa, Mama ta ce Allah yasa haka shi ya fi Alkhairi. Washegari da safe Mama ta ce mata gobe Sunday ta cewa Sadik ya zo Daddy yana son ganin shi. Kamar zata yi kuka ta ce, "Toh Mama zan faɗa masa, amma Mama har yau na kasa sanar da Uncle Ahmad, wallahi ban san ta yaya zan faɗa masa ba, kuma na san zai yi wahala ya ƙi zuwa yau ko gobe." Mama ta ce "Shikenan idan ya zo ni zan yi masa bayanin da zai fahimta da kaina." Ta gyaɗa mata kai tana ƙoƙarin ganin bata bar hawayen idonta ya zubo ba. Ta tashi ta koma ɗakinta dan za ta iya fashewa da kuka saboda yanda take jin zuciyarta, ita kuma bata son ta yi kuka a gaban Mama. Tana hawaye ta yiwa Sadik text ta sanar masa abun da Mama ta ce ta faɗa masa. Ta kwanta tana kukan da bata san dalilin shi ba. Tana jin wayarta tana ringing amma bata bi ta kanta ba. Sai da ta gaji dan kanta sannan ta yi shiru, ta tashi ta ɗauki wayar ta duba ta ga Sadik ne ya kira ta, da ya ga bata ɗauka ba yay mata reply ɗin text ɗinta, tare da daɗaɗan kalaman soyayya a ƙarshe. Ta yi ɗan murmushi, sannan ta tashi ta je ta wanke fuskarta. Bayan Sallar Azhar tana zaune a ɗakinta da materials ɗin karatunta tana dubawa. Mama ta shigo ɗakin ta ce mata. "Neehal Ahmad ya zo." Ta d'ago da sauri gabanta na wani irin fad'uwa saboda razana. Mama data kula da yanayin da ta shiga ta ce. "Ki je ku gaisa, yana ƙasa yana jiranki, kuma karki nuna masa wani abu, idan zai tafi zan yi masa bayanin komai." Neehal ta gyaɗa mata kai kawai. Kamar wadda k'wai ya fashewa a ciki ta tashi cikin sanyin jiki ta yane kanta da mayafin abayar dake jikinta. Ta ɗan gyara fuskarta sannan ta fesa turare kaɗan, ta fice daga ɗakin cikin matuƙar sanyin jiki.
Kamar kodayaushe yana zaune a kan carpet idanunsa akan steps. Ta sakko cikin nutsuwarta kanta a ƙasa, gabanta na cigaba da faɗuwa ta zauna a kusa da shi tare yin sallama. Yana murmushi ya amsa mata. Ta ce "Ina yini Uncle." Ya ce "Lafiya k'alau Princess, ya weekend?" Ta ce "Alhamdulillah." Ya ce "Ya School da aiki?" Ta ce "Alhamdulillah." Ya gyara zama tare da juyowa ya fuskance ta sosai ya ce. "Kin yi kyau, kullum kamar ƙara miki kyau ake Princess." Ta d'ago tare da ƙirƙirar murmushi akan fuskarta a ƙoƙarin ta na ganin bata nuna masa akwai wata damuwa ba, ta ce. "Ni ɗin kuwa?" Ya ce "To da wa?" Ta sake yin murmushi ta ce. "Ina Yarana?" Ya ce "Suna gida." Ta ce "Da fatan dai suna lafiya, kuma baka barin wani abu yana damar mun su?" Ya kafe ta da ido ya ce. "Suna lafiya, ni kam me zan bari ya damu ƴaƴan Aunty? Ai lallaɓa su nake kar Aunty ta ce ta fasa Aure na." Ta yi ƙasa da kanta da sauri saboda yanda ta ji bugun zuciyarta ya sauya, ta hasaso yanda yake cikin farincikin nan da nishad'i ya zai ji idan Mama ta yi masa bayanin ta kusa zama mallakin waninsa, daga yau ba zai ƙara zuwa su yi irin wannan zaman ba, duk soyayyar da ya nuna mata ta zama tahiri, a...... "Neehal!" Ya katse mata tunani ta hanyar kiran sunanta. Ta d'ago tay masa kallon cikin ido cikin dakiya. Ya lumshe ido ya buɗe su a cikin nata ya ce. "Tunanin me kike?" Ta ce "Babu komai Uncle." Ya karyar da kai ya ce, "Bari na yi miki hoto, kin mun kyau sosai yau." Ya ɗauko wayarsa yay mata pictures, ita kuma tana ta murmushi, sannan ya ɗauke su tare. Ta karɓi wayar tana dubawa, hotunan sun yi kyau sosai. Ta yi murmushi ta cigaba da kallon pictures ɗin wayar, wanda fiye da rabi na twins ne. Ta tura wanda yay musu yanzu sannan ta tuttura wasu na twins da nasa ta whatsapp. Mama da kanta ta sakko ta shiga kitchen ta zubo masa abinci ta kawo masa, ya dinga yi mata godiya cikin jin kunya. Bayan Mama ta koma sama ya dubi Neehal ya ce. "Ina son Mama sosai, saboda kirkinta, da sanin darajar ɗan Adam gami da karamci." Ta yi murmushi kawai, sannan ta zuba masa abincin, yana ci suna hira, wanda Neehal ta ji kusan rabin damuwarta ta tafi. Sai da aka kira Sallar la'asar sannan ya tashi ya je masallaci ya dawo. Neehal bata sakko ba tana ɗakinta akan darduma bayan ta idar da Sallah, addu'a take yi akan Allah ya sanyaya wa Ahmad zuciyarsa, Allah yasa kar abun da Mama zata faɗa masa ya yi hurting ɗinsa over.