Sashe 87
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
cika da mamakin ganin ɗan *senator Na_kowa* a matsayin wanda zai ba da shaida. Wata mata kuwa har zabura ta yi ta miƙe, na kusa da ita su kay saurin mayar da ita ta koma ta zauna. Barrister Garba ɗan_ladi ma ya firgita ba kaɗan ba, dan har gumi ya fara gogewa, sai dai babu bakin magana tunda ba shi da abun cewa da kotu zata saurara. Bilyaminu ma ido k'walalo waje alamun razana yana kallon Hashim. Cikin nutsuwa Hashim ya faɗi sunansa kamar yadda Barrister Murtala ya ce masa. Sannan ya buk'aci da ya ba da shaida kamar yadda ya fito da nufin hakan. Ya gyara tsayuwa ya ce "Mahaifina Senator Na_kowa shine wanda ya saka su Bilyaminu yin wannan kisan." Kafin ya gama rufe bakinsa kotu ta barke da hayaniya gami da sallallamun jama'a. Alk'ali ya buga gudu ma tare da faɗin "Order." Nan dan kotun ta ƙara yin tsit kamar ba mutane a ciki. Alk'ali ya dubi Hashim ya ce "Cigaba da baya nanka kotu na sauraren ka." Ya cigaba da magana. "Watarana tun ina saurayi kafin na yi aure na je part ɗin mahaifina dan amsa kiran da yay mun. Ina shiga falonsa na ji yana waya a balcony inda yake cewa. "Kar ka damu mutumina, ko Alhaji Muhammad Gabasawa ya yarda ko kar ya yarda sai na biya buƙata ta da ƴarsa tunda zuciyata ta ƙwadaitu da ita, kasan bana had'iyar yawu a banza. Ya yi shiru na wasu sakanni sannan ya kece da dariya ya ce, Kar ji komai na waje na kamar kaima ka huta da wannan yarinyar nan ne, kasan dama muna neman yarinya ta cikon goma kamar yadda boka ya ce mana akan aikin mu, to ina tabbatar maka da ita za'a za mu cike, zan biwa Gabasawa ta tallama ya bani ƴarsa in cika shi da ƴaƴan banki, idan kuma ya yi taurin kai kawar da shi a doran ƙasa ba wahala zai mun. Ya ƙara yin shiru na wasu sakanni sannan cikin dariya ya ce, Ah, to dan yana mutumina ai bai kai ya biyan buƙata ta ba a gurina. Ni fa dama dan na yi mu'amalar jin daɗi da shi na shiga cikin rayuwarsa, to kuma na fuskanci ba zai taɓa amincewa da buƙata ta ba, wai shi mai tsoron Allah, dan haka kawai zan huta da ƴarsa ma ya wadatar." Wani irin juyawa na ji kaina yana mun, na yi baya da sauri na fice daga falon cikin tsananin tashin hankalin jin abun da mahaifina yake aikawa. Da ƙyar na iya ƙarasawa part ɗina na zube a kan kujera. Tun daga wannan ranar na fara bibiyar al'amuransa ba tare da ya sani ba. Anan na gane mahaifina cikakken ɗan luwaɗi ne sannan kuma k'wararre a rapping ƙananan yara mata, duk a saboda neman duniya da mulki. Lokacin dana samu labarin rasuwar Alhaji Muhammad Gabasawa da matarsa ko tantama ban yi ba na san aikin mahaifina ne, amma ban sanar da kowa ba saboda yanda idonsa ya rufe a neman duniya nima zai iya sawa a kashe ni matuƙar na faɗa. Sai dai cikin ikon Allah bayan rasuwar Alhaji Muhammad Gabasawa da wasu kwanaki shima Dad Allah ya saukar masa da ciwo wanda aka rasa gane kansa da gindinsa. Ciwo kullum ƙara tsanani yake ana magani amma kamar ba'ayi. Ya shafe fiye da shekara biyu yana jinya kafin ya mutu, mutuwar da bana fatan duk wani wanda na sani a duniya ya yi irin ta. Domin kuwa babu alamar dacewa a tafiyar." Sai kuma ya yi shiru na wasu sakanni sannan ya cigaba da magana cikin raunin murya. "Ganin ya rasu sai na bar abun a raina ban sanar da kowa ba, sai a cikin satin nan muka haɗu da Barrister Murtala ta sanadin wani abokina wanda shi ma Barrister ne, a nan ya ji yana bashi labarin case ɗin dake gabansa. Gabana ya faɗi amma ban sanar da shi komai ba a lokacin har muka rabu, sai daga baya dana koma gida na kasa zaune na kasa tsaye, na rasa abun da yake mun daɗi. A jiya ne na yanke shawarar na nemi Barrister Murtala na faɗa masa gaskiyar cewa mahaifina ne ya saka a yi wannan kisan, ko iyalan mamacin za su yafe masa dan ya samu sassauci daga azabtar Ubangiji. Da taimakon abokina kuma abokin Barrister Murtala na gano inda Barrister Murtala yake da zama na je na ba shi wannan labarin, shine ya buk'aci dana zo kotu yau na faɗa a gaban Alk'ali."