← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 118

Sashe 6

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan Magriba Neehal na zaune a gaban madubin ɗakinta ta na d'aura ɗankwalin atamfar da ke jikinta, dawowarta kenan daga gidansu Haneefah ta sauya kaya ta fara shiryawa kafin Anwar ya ƙaraso. Wayarta dake kan mudubinne ta fara ringing cikin amon sautin wak'a mai daɗi irin ta masoya, murmusawa ta yi ta kai hannu ta ɗauki wayar dan tasan Anwar ne ya ƙaraso tun da shi kaɗai ta sawa wannan ringing ɗin, ta ɗaga kiran tare yin sallama cikin siririyar muryarta, Anwar ya amsa tare da faɗin "Gimbiyata na ƙaraso" ta yi murmushin jin daɗi mai sauti ta ce "Welcome Sir" shima murmushin ya yi tare da katse wayar, Neehal ta ƙarasa daurinta ta feshe jikinta da da daɗaɗan turarukanta masu sanyin ƙamshi, wanda idan mutum ba matsowa kusa da ita ya yi ba, ba zai ji k'amshin ba. Ɗakin Mama ta lek'a ta sanar mata Anwar ya zo ta fita, Mama ta ce sai ta dawo, ta kuma gaishe da Anwar ɗin, a falon ƙasa ta tarar da su Dije su na kallo, ta dube su ta ce "Aunty Dije dan Allah idan babu damuwa ki ɗan biyo ni da cake ɗin can, zan ɗau drinks ne" Dije ta je "Haba uwar ɗakina babu damuwar komai" Neehal ta yi murmushi ta ce "Toh Nagode" Zulai ta ce "Kawai ki wuce zamu kawo miki har ruwanma, kar yay ta jiranki" Neehal ta ce "Toh Nagode sosai"

Ya na zaune a kan fararen kujerun da suke zama koyaushe dan yin zancen, ya na latsa wayarsa, ya na sanye cikin wata shadda light blue, da ta haska choculate colour ɗin fatarsa wadda ta nuna zallar jin daɗin da yake ciki, Anwar Kyakkyawane a jin farko a sahun kyawawa, dogo ne amma bashi da jiki sosai. Neehal ta ƙaraso gurin tare da yin sallama, Anwar ya d'ago ya na bin ta da wani kallo k'auna, wadda ya sata saurin sunkuyar da kanta ƙasa cikin jin kunya, ya amsa mata sallamar ya na ƙara k'ura mata ido, Neehal ta turo baki gaba cikin shagwab'arta ta ce "Ina yini" ya yi murmushi ganin yanda ta yi, kasancewar gidansu Neehal akwai wadatuwar haske sosai ko mun dare, shiyasa ya ke kallonta tar" ya ce "Lafiya k'alau, ya Mama" ta ce "Tananan k'alau ta na gaisheka" ya ce "Ina amsawa tare da ajiye wayarsa a kan ɗan table ɗin robar da ke gabansu, cike da soyayya da kulawa ya ce "Me ya faru ne, na ga kamar Queen na fushi da Ni" Neehal ta ƙara shagwab'e fuska ta ce "Nothing, kawai kai ne na ga ka na ta kallo na" murmushi Anwar ya yi me sauti ya ce "Dan mutum ya kalli matarsa laifine, ni fa gaskiya kunyar nan ta ki ta na cutata, dan ma kwanaki kaɗan suka rage ki zama mallakina na cire miki ita gabad'aya" Neehal ta ƙara sunkuyar da kanta ƙasa ba ta ce komai ba, saboda fad'uwar da gabanta ya yi, a dalilin zancen auransu da Anwar ya yi, ta rasa me ya sa tun da auransu ya matso take jin hakan a tattare da ita, a da kuma farkon soyayyarsu ba ta jin komai, burinta kawai a lokacin a ce sun mallaki juna, saboda tarin k'aunar da take masa, amma yanzu duk sai ta ji jikinta ya yi sanyi da auran. Anwar bai yi tunanin wani abu a shirun da Neehal ta yi masa ba, dan ya riga ya saba da halinta na jin kunya idan suna tare, saɓanin idan suna waya ko chat da take zagewa ta na rattabo masa kalaman soyayya, amma idan ya zo gurinta sai dai ya yi ta hirarsa shi kaɗai, ita daga um sai um'um, in kuma ta so wani lokacin ta zage su sha hirarsu. Anwar ya ƙara cewa "Yau ko um ɗinma ba zan samu ba Queen, sai dai shiru?" Neehal ta yi murmushi a ƙoƙarin ta na ganin Anwar din kar ya yi tunanin wani abu ta d'ago kanta tana kallonshi amma ba ido cikin ido ba ta ce "Za ka samu mana, harma fiye da haka" ƙarasowar su Dije gurin ya hana Anwar maganar da yake son yi, su ka yi sallama Neehal da Anwar suka amsa musu a tare, gaishesa suka yi tare da ajiye kayan hannunsu a gaban Anwar din, Anwar ya amsa musu tare musu godiya suka juya suka tafi. Neehal ta mik'e ta tsiyaya masa ruwa da lemo a glass cup, sannan ta koma ta zauna suka cigaba da hirarsu ya na shan drink d'in kaɗan_kaɗan. Can Anwar ya dubeta ya ce "Queen ni fa yau na zo miki da babbar tsaraba" Neehal ta ce "Ta me kenan?" Bai ba ta amsa ba sai hannunsa da ya zira a aljihun rigarsa ya ɗakko wani abu da Neehal ba ta gane mene ba, buɗe ɗan ƙaramin case ɗin ya yi wani zobe mai kyau ya bayyana, Neehal ta waro manyan idanunta ta ce "Wow ya Anwar ring ɗin nan ya yi kyau sosai fa" ya ce "Sai ma kin san a wannan kyakkyawan finger ɗin naki, na san sai ya ƙarawa zoben kyau" Neehal ta yi murmushi, Anwar ya ɗakko zoben dake ta k'yalk'yali ya ce "Kawo Hannunki in saka miki, na ki ne na kawo miki" Neehal ta ce "Nagode sosai Ya Anwar, amma Ni dai ka ba ni in saka da kaina" Anwar ya ce "A'a my Queen ni dai ki barni na sa miki" Neehal ta yi shiru ba ta ce komai ba, domin ba za ta iya musu da Anwar ɗin ba, hannun damanta ta kalla, a hankali ta sa hannun hagunta ta cire zoben dake babban ɗanyatsanta ta ajiye, sannan ta miƙa masa ɗanyatsan, murmushi Anwar ya yi ya matso ya zira mata zoben, hakan ya yi dai_dai da fitowar Ameen daga part ɗinsa domin tafiya Masallaci dan anfara kiran sallar isha'i, karaf a idanunsa Anwar ya zira wa Neehal zobe...........✍️
[7/21, 9:00 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*

_By_
_Zeey Kumurya_

*0️⃣5️⃣*

Tab'e ɗan ƙaramin bakinsa ya yi tare da ɗauke kansa daga inda suke. Neehal ta janye hannunta tana sauke Numfashi ba ta ce komai ba, saboda abun ya mata wani banbarakwai, duk da Anwar ko hannunta bai taɓa riƙe wa ba amma sai ta ji wata irin kunyarsa ta rufe ta. A hankali ta daure ta ce "Nagode sosai Ya Anwar" Anwar ya yi murmushi ya ce "Kin ga yanda hannunki ya yi wa zoben kyau kuwa?" Neehal ta yi ɗan murmushi idanunta na kan hannunta da zoben yake sanye dass kamar an gwada ta ce "Hannun nawa ne ma ya yi wa zoben kyau, ba ma zobenne ya yi wa hannuna kyau ba?" Anwar ya ce "Eh mana, ai ke ko kwalliya ki kai ke ki ke wa kwalliyar kyau ba ita take miki ba" kafin Neehal ta ce wani abu Ameen ya ƙaraso kusa da su, Anwar ya yi sauri ya ce masa "Yayanmu Barka da dare" Ameen ya ɗan saki fuskarsa ya na mik'owa Anwar hannu ya ce "Yawwa barkan mu" suka yi musabaha Anwar ya gaisheshi ya amsa sannan ya wuce ba tare da ya kalli ko inda Neehal take ba, saɓanin ita kuma da ta zira masa na mujiya. Anwar ya kalle ta ganin ta bi Ameen da ido ya ce "Ya dai Queen?" Neehal ta sauke ajiyar zuciya, zuciyarta babu daɗi ganin yanda Ameen ya shareta, ya ƙi kulata, Alhalin yau ba su haɗu ba kwata_kwata, ta rasa me yasa kwana biyunnan yake mata haka, duk da ma can shi mutum ne ba mai sakewa ba kuma ga miskilanci, amma ya na nuna mata kulawa sosai a matsayinta na k'anwarshi tilo guda ɗaya...... Anwar ya katse mata tunaninta ta hanyar faɗin "Wai me yake farune na ga kamar kina cikin damuwa Neehal?" Neehal ta sauke ajiyar zuciya a karo na biyu ta ce "Bakomai Ya Anwar" ya ce "Sure?" Ta gyaɗa masa kai kawai tare da ƙoƙarin boye damuwarta dan kar ya fuskanci wani abu. Anwar ya duba tsadadden agogon hannunsa ya ce "Shikenan Queen bari na je gida na ga time ɗin Sallah ya yi" Neehal ta ce "Ba ka ci cake din ba kuma?" Ya ce "Na k'oshi ne" Neehal ta bata fuska ta ce "Please ya Anwar ka ci mana" ba tare da ya ce komai ba ya buɗe Plate d'in da'aka rufe cake d'in ya d'au 1 ya gutsira ya ajiye, ya na kallonta ya ce "Thank you" Neehal ta ce "Ka ƙara Mana, wannan ai baka ci ba" ya ce "I'm sorry dear, ciki na ya cika ne" Neehal ba ta kuma cewa komai ba, Anwar ya Mik'e ya ce "Bye sai mun yi waya?" Neehal ta mik'e ta na faɗin "Mu je in raka ka" Suka jera su na tafiya har inda ya yi parking Motarsa ta raka shi, tsayawa su ka yi ta dubeshi ta ce "Thank you so much ya Anwar for your time, da kuma kyautar da ka ba ni, Allah ya sa ka da Alkhairi ya ƙara buɗi" Anwar ya ce "Ni ma Nagode sosai dear, kuma na ji daɗi, Allah ya barmu tare" Neehal ta ce "Amin, Allah ya kiyaye hanya ya tsare, ka gaida Ammi" ya ce "Amin, za ta ji Insha Allah bye" Neehal ta ɗaga masa hannu ta na murmushi, shima d'aga mata hannun ya yi ya buɗe motar sa ya shige" Neehal ta juya ta koma cikin gida. Su Dije ta faɗa wa su je su ɗauko cake ɗin su cinye, Mama da Hajiya duk suna ɗaki tasan jiran Sallah su ke yi, itama ɗakinta ta shiga ta faɗa toilet ta dauro alwala ta fito ta bi jam'i.
Chapter 6 · 0% Book details