Sashe 45
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Aunty Fauziyya kamar kullum tana jiyo hayaniyar yaranta ta shigo ɗakin da sauri, dan kullum da hakan take gane tashinsu, Neehal na rakub'e jikin kayanta tana ta rawar sanyi, cikin muryar marasa lafiya ta ce "Ina kwana Aunty." Wani mugun kallo Aunty Fauziyya ta watsa mata, a harzuk'e tana zazzaro ido kamar sabuwar kamu ta ce "Yana gidan Ubanki shi kwanan." Neehal bata kuma cewa komai ba, ita kuma Fauziyya ta ja ƴaƴanta sukai toilet, wanka ta musu ta shirya su cikin uniform ɗinsu, sannan suka fita falo dan karyawa. Uncle Umar ya ce wa Fauziyya "Ina Neehal ɗin, itama ta fito ta karya mana." A fusace Aunty Fauziyya ta ce masa "Ka san yar gold ce bata tashi ba har yanzu." Sai wajen ƙarfe tara Aunty Fauziyya ta ƙwalawa Neehal kira lokacin Uncle Umar ya fita, cikin hanzari Neehal ta taso dan wani bala'in tsoron matar take ji, k'osan Talatin ta bata da wani ɗan bread da ruwan bunu rabin ƙaramin cup a matsayin breakfast. Neehal ta bi abun da aka bata da kallo sannan ta fara ci tana yamutsa fuska saboda bakinta babu daɗi, yunwa ce kawai ta sa take ci, ga shi ita k'osai ba mutuminta ba ne, gara ma bread ɗin. Ruwan bunun kuwa ko kurb'a ba ta yi ba, dan tasan baza ta iya sha ba. Bayan ta gama cikin faɗa Aunty Fauziyya ta ce "Tunda ciki ya ɗauka, sai ki tashi ki haɗa kayan nan, ki kai tsakar gida ki wanke, sannan ki dawo ki share mun falo ki yi mopping, ɗakin da kika kwana ma haka." Cikin sanyi Neehal ta ce "Aunty ban da lafiya, kuma ban iya b......." "Ai ko cutar mutuwa kike yau sai kin mun aikin nan, dan Ubanki Jakar uwarki ce ni zan dafa miki ki ci kina daga kwance, zaki tashi ko sai na miki dukan mutuwa a gidan nan." Jiki na b'ari Neehal ta tashi ta fara haɗa kayan, duk da zazzaɓin dake damunta, amma saboda tsoron Fauziyya da take ji dole ta yi. Ba ta taɓa wanke_wanke ba a rayuwarta, sai a gidan Mama ne ma idan ta ci abinci Mama take sata ta dauraye flate ɗin da taci abincin. Ai kuwa Fauziyya ta sha asarar omo, gashi kafin ta gama ta jik'a jikinta jagab da ruwa, a haka ta yi share_sharen da mopping, Fauziyya kuwa tuni ta fice yawon mak'ota. Tana gama aikin ta yi daki ta kwanta akan tiles, zazzaɓi mai zafi ne ya rufe ta. Da Fauziyya ta dawo ta ga b'arnar Omon da Neehal ta mata, ta dinga surfa mata ashariya da masifa, da dukanta ma zata yi wata makociyarta data shigo ta hanata, ganin yanda Neehal ɗin take rawar sanyi. Da rana ma kiranta Aunty Fauziyya ta yi ta bata wata shinkafa da wake ƴar kaɗan a roba, ko man kirki babu a ciki. Lauma ɗaya Neehal ta yi ta ture ta koma ɗaki ta kwanta, Fauziyya ranar wuni ta yi tana zagin Neehal. Da daddare Uncle Umar ya lek'a ɗakin da Neehal take ganin Shiru_shiru bai ji motsinta ba tunda ya dawo, ganin ba ta da lafiya ya bata panadol da Paracetamol ta sha, ya kuma kawo mata lemo da ayaban daya shigo gidan da su har ɗaki, ta kuwa ci ayabar ba laifi dan tana sonta sosai. Fauziyya tayta kumbure_kumbure tana huci kamar zata naushi iska ganin abun da Uncle Umar ya yi wa Neehal. Washegari ma Neehal ce ta yi wanke_wanke da shara, jikin nata ya yi sauƙi tunda ta sha magani, sai dai bata warke sumul ba, ranar kam sai da Fauziyya ta mare ta akan ta'adin omon data mata. A daren Ranar Uncle Usman ya zo gidan yi musu sallama dan zai koma garin da yake aiki ne. Tsaraba sosai yayo wa Neehal da su Aiman ta sweet da chocolate, da zai tafi Neehal tai ta Kuka, Aunty Fauziyya ta tab'e baki a ranta ta ce 'Munafurcin banza.'
Tun daga ranar Neehal ce take wanke_wanke da shara da mopping da aiken gidan, yanda ka san baiwa haka Fauziyya ta mayar da ita, ga masifa da tsawa da bala'i. Wani matsifaffen tsoronta Neehal take ji, gashi idan Uncle Umar ya dawo ta haÉ—a wa Neehal sharri a gurinsa wai ta zage ta, haka zai zo yay mata masifa shi ma kamar zai dake ta. Kullum Neehal sai ta ci kuka ta gode Allah, kuma duk wani abu na amfani da Aunty A'isha ta sako mata acikin kayanta Fauziyya ta k'wace, kama daga toothpaste, sabulan Wanka hatta bargonta duk ta k'wace. Yau kwanan Neehal goma sha biyu a gidan Uncle Umar, amma gaba-d'aya ta rame ta yi duhu saboda wahala, baza ka taÉ“a cewa itace yar gatan Ummanta da Abbanta ba. Kitson dake kanta ya tsufa ya dugurguje, ga farcenta ya fara taruwa, ta saba duk ran Friday Aunty'nta tana yanke mata, haka ma Mama idan tana gidanta, nan kuwa wanka ma ba kullum ake barinta ta yi ba. Ga rashin ishashshen abinci, abincin da yaro É—an shekara biyar zai ci shi ake bata, shima kuma mara daÉ—i. Kullum da safe tana jin k'amshi ana soya k'wai da dankali amma ita ko ganin shi bata yi, haka ma naman miya ba'a bata ko gutsire. Misalin Æ™arfe Uku na yamma Neehal ce tafe tana ta zuba sauri saboda gargadi'n da Aunty Fauziyya na mata akan kar ta daÉ—e, kayan miya zata siyo mata a can bakin titi, kuma daga gida zuwa bakin titi da Æ´ar tafiya, gaba-d'aya a gajiye take saboda aikin da tasha yau har da wankin kayanta ta yi, ga rana da ake k'walla wa a garin, gashi ba ta ci abincin rana ba kuma tana jin yunwa sosai gami da Æ™ishirwa, Aunty Fauziyya ta ce sai ta siyo mata kayan miyar sannan zata ci abincin. Ta shiga wani layi wanda daga shi sai titi, ta ga wani k'aton gida mai kyau, wani kyakkyawan matashi da ba zai wuce shekaru 25 ba ne ya fito daga Æ™aramar Æ™ofar gidan hannunsa É—auke da robar ruwan faro mai sanyi. Tsayawa Neehal ta yi ta Æ™ura wa ruwan hannunsa ido tana maida Numfashi saboda gajiya, sau É—aya matashin ya kalle ta ya É—auke kai ya nufi Motar dake fake a gaban gidan, Neehal ganin haka yasa ta Æ™arasa kusa da shi da sauri ta ce...........âœï¸
[7/21, 9:02 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*2ï¸âƒ£9ï¸âƒ£*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*