← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 118

Sashe 14

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Misalin ƙarfe 11 na safe Ameen ya shigo gidan, kamar yadda ya saba part d'in Mama ya nufa direct, da key d'in hannunsa ya yi amfani ya buɗe kofar, da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga. Hameedah ce kwance a kan kujera ta na latsa waya, Mahaifiyarta kuwa ta fice gidan k'awayenta. Da sauri ta tashi zaune jin sallamarsa tare da faɗaɗa fara'arta wadda tun da ta zo gidan ba ta yi kamarta ba. Ameen ya kalle ta sau ɗaya ya kau da kansa, har ya ƙaraso cikin falon kallon sa take kamar za ta lashe shi bakin ta ya ƙi rufuwa dan farin ciki. Cikin kaud'i da iyayi ta ce "Sannu da zuwa Ya Ameen." Ta ƙarashe zancen tare da mik'ewa ta koma kusa da shi. Ya kalle ta ba yabo ba fallasa ya d'aga mata kai. Hameedah ba ta damu ba ta ce "Yayanah I missed you so much, na manta when last da na ganka, last zuwan da na yi ba mu haɗu ba, gashi kai kuma ba ka zuwa gidanmu." Ameen ya banzatar da zancen nata ya ce "Yaushe kika zo?" Cike da jin daɗin ya biye mata da ya yi suna hira ta ce "Yesterday, ni da Mommy mun zo gaisuwa ne?" Ameen ya ce "Tun yaushe aka yi rasuwar amma sai yanzu za ku zo?" Hameedah ta ɗan shagwab'e ta ce "To ai Yaya ka ga ina zuwa aiki, sai weekend nake da time." Ameen ya yi shiru kamar ba zai yi magana ba, sai kuma can ya ce "Neehal tana matsayin cousin sis ɗinki, amma a mata rasuwa ki ce sai kin samu time za ki zo mata gaisuwa?"  Hameedah ta tab'e baki tare da ɓata fuska ba ta ce komai ba, sai kuma can ta ce "Kasan Mommy ma ba ta jin dad'i ba time ɗin shi ya sa ba mu zo ba, kuma na ga ita gaisuwa ai ba ta tsufa, tun da mun masa addu'a ai is ok." Ameen bai kuma ce mata komai ba ya mik'e ya nufi sama gurin Mahaifiyarsa. Mama ta na operating system ya  yi knocking k'ofar ɗakin, ta ba da umarnin a shigo. A hankali ya buɗe k'ofar bakin sa ɗauke da sallama. Mama ta d'ago ta na duban sa ta amsa masa, ya ƙaraso ya zauna a gefen ta ya ce "Gud Morning Mum, how are you?." Mama ta ce "Lafiya, ka zo lafiya? Ya aiki?" Ya ce "Alhamdulillah, ina Neehal fa?" Mama ta ce "Ta je aiki." Ya gyad'a kai kawai tare da ƙoƙarin mik'ewa. "Koma ka zauna ina son magana da kai." Muryar Mama ta katse masa hanzarinsa. Ya gyara zama tare da bata duka hankalinsa. Mama ta ture laptop d'in gabanta ta na dubansa da kyau ta ce "Ameen me kake tunani a kan al'amarin Neehal? Ba ka ganin kamar wasu ne suke bibiyar rayuwarta? Duba da a baya an kashe Jameel ma" Shiru ya yi alamun nazari kafin ya sauke Numfashi ya ce "Mum, babu irin tunanin da ban yi ba a kan wannan al'amarin, tun lokacin na ci karo da labarin mutuwar Anwar dake ta yawo a media, amma kuma da na yi wani nazari da lissafi sai na ga kamar kisan Anwar da Jameel ba shi da alaƙa da Neehal." "Saboda me ka ce haka?" Cewar Mama ta na kallon sa. Ameen ya ce "Idan ba ki manta ba Mum, shi Jameel dama can ya na da 'yan adawa a rayuwarsa duba da yanayin aikinsa." Mama ta ce "Hakane, domin kuwa tun a wancan lokacin da aka kashe Jameel ko kaɗan ban yi tunanin kisan ya na da alaƙa da Neehal ba, dan sometimes Idan ya zo gaishe ni ya na yawan cewa a taya su da addu'a saboda magauta da mahassada, amma kuma kashe Anwar da aka yi ya birgita mun duk wani lissafi na Ameen." Ameen ya ce "Duk da an kashe Anwar amma ba na tunanin kisan Anwar ya na da alaƙa da na Jameel" Mama ta yi shiru ta na jin dama furucin Ameen zai tabbata da sai tafi kowa farinciki, za ta so a ce ba dan Neehal ake kisan ba, amma kuma abun da kamar wuya musamman idan ta yi duba da....... "Kar ki sa wa ranki damuwa Please Mom, kuma ki cire tunanin wai ko dan Neehal aka kashe Anwar" Ameen ya katsewa Mama tunaninta da faɗin haka. Mama cikin damuwa ta ce "Ameen! Ka na so ka kwantar mini da hankali ne kawai kamar yadda ka saba a kodayaushe idan ka ga ina cikin damuwa, amma ba ni kaɗai ba ma, ko A'isha da Sadiya mun yi maganar da su kuma suma duk tunanin su haka ne." "To ai dama tunanin ku duk ɗaya ne ku mata." Cewar Ameen ya na murmushi. Mama ta ɗan harara shi ta ce "Su kuma sauran mazan da muka yi maganar da su fa?" Kamar a ɗan rud'e ya ce "Su wa kenan?" Mama ta masa wani kallo ta ce "To mene na yin hakan kuma, kamar wanda aka zabura?" Ameen ya ɗan lumshe idonsa ya ce "Nothing, kawai ban so ki ka yi maganar da wasu ba" Mama ta ce "Ahmad ɗin Sadiya ne fa sai Mahmud, su kuma ka ga ai duk na gida ne." Ameen ya ce "Hakane, Insha Allahu ko ma yaya ne Allah zai warware mana, kuma Insha Allahu problem ɗin ba daga wurin Neehal ta ke ba." Mama ta ce "Ameen ya Allah."  Ameen ya mik'e ya na faɗin "Ina Hajiya fa?" Mama ta ce "Tun safe driver ya kaita gidan Sadiya yau can za ta wuni." Ya ce "Ok" har ya juya Mama ta ce "Ka ga Hameedah kuwa" ya gyad'a mata kai alamar Eh ba tare daya juyo ba, Mama ta yi murmushi kawai dan tasan tun da ya yi haka ba ya son zancen Hameedan ne.
Chapter 14 · 0% Book details