Sashe 107
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da suka yi Sallar isha'i sannan Mama ta zaunar da Neehal a ɗakinta akan maganar da ta ce zasu yi. Tana duban ta seriously ta ce "Neehal ɗazu kawunki Malam Musa ya zo, yaso ya zauna ya jira ki dawo ku gaisa amma akai masa kiran gaggawa a gurin aikin su. Kuma dalilin zuwan nasa ya zo ne akan ya kamata idan kina da tsayayye ya fito a yi maganar auran ku." Ta d'ago ta dubi Mama da sauri amma batai magana ba. Mama ta cigaba da magana da faɗin, "Na ce masa akwai wanda yake zuwa gurin ki, dan kun ma daɗe kun kusa shekara tare, amma mu da muna jiran ki kammala karatun ki ne sai mu yi masa magana idan da gaske yake sai ya fito a yi maganar biki." Neehal ta sauke numfashi tare da yin ƙasa da kanta, Mama ta ce. "Ya ce duk wannan ba matsala ba ce, idan gasken yake ya turo a yi maganar auran naku, bayan kin kammala karatun naki sai a yi bikin." Neehal ta d'ago ta dubi Mama gabanta na fad'uwa ta ce "Mama duk yanda kuka yanke dai-dai ne, kuma duk abun da kuka ce shi zan bi." Mama ta ce "Haka ne Daughter, Allah yay miki albarka, yanzu idan Daddy ya dawo zamu tattauna ni da shi, yanda muka yi zan sanar miki sai ki faɗawa Sadik ɗin." Neehal ta gyaɗa mata kai, tana son tay mata maganar Ahmad amma kuma ta rasa ta ina zata fara. Mama dake nazartar ta, ta ce "Neehal me kike son cewa? Ko baki son Sadik ɗin ne?" Ta girgiza mata kai cikin sanyin jiki. Mama ta ce "To ya na ga gaba-ɗaya yanayinki ya sauya, kamar ba ki yi farinciki ba, kin ga Daughter idan da akwai wata matsalar ki faɗa mun." Ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce "Uncle Ahmad." Mama ta yi murmushi ta ce "Me ya faru da shi?" Ta buɗe baki kamar zata yi magana sai ta fasa. Mama ta ce "Na san soyayya kuke yi da shi ai, na zuba miki ido ne kawai in ga iya gudun ruwanki." Ta rufe fuskarta da hannunta cikin jin kunya. Mama ta ce "Amma Neehal me yasa kina tare da Sadik kike kula Ahmad da sunan soyayya? Hakan ba dai-dai ba ne fa." Ta sauke numfashi ta ce "Mama ba zan iya ƙin kula shi ba, saboda shi ma ya taimake ni a lokacin da nake buƙatar taimako." Mama ta ce "You are right, amma kin yi babban mistake." Ta ce "Mama na sani, amma ban san yaya zan yi ba ne a time ɗin." Mama ta ce "Shikenan, yanzu shi kike so ko Sadik ɗin. Ta yi shiru ba ta ce komai ba. Mama ta ce "Uhm? Ke nake sauraro." Ta ce "Mama na rasa wanda zan zab'a a cikin su, kowanne a cikin su yana da good qualities, amma Mama ki zaɓar mun ɗaya a cikin su Please, duk wanda kika zaɓar mun i will accept him." Mama ta girgiza kai tare da dafa ƙafaɗarta ta ce. "Neehal miji fa, abokin rayuwarki wanda zaku yi rayuwar da baku taɓa yin irinta da kowa ba a duniyar nan. Dan haka ke ya kamata ki zab'arwa kanki wanda hankalin ki ya fi kwanciya da shi. Wanda kika yaba nagartar shi kuma kuka fahimci juna, wanda kike ganin zai baki farinciki ya kuma riƙe ki amana. Duk da mazan yanzu sai addu'a, amma ba duka aka haɗu aka zama ɗaya ba, akwai nagari wanda muke fatan Allah ya haɗa ku da su. Dan haka ki je ki nutsu ki yi shawara ki tantance wanda kike ganin hankalinki ya fi kwanciya da shi, kafin mu gama magana da Dad sai ki sanar mun wanda kika fitar, sai na faɗa musu a san abun yi. Sannan kuma ki dage da addu'a da neman zaɓin Allah." Neehal ta sauke numfashi cikin rashin sanin abun yi ta gyaɗawa Mama kai. Mama ta tashi tana faɗin. "Bari na je part ɗin Daddy." Ta gyaɗa mata kai kawai still bata yi magana ba. Bayan fitar Mama ta kwanta akan gado ta faɗa duniyar tunani. Ta fara tuno farkon haɗuwar su da Sadik da irin mutuncin da yay mata, ta kuma tuno irin tarin soyayyar da yake mata, da kuma damuwar da yake shiga a sanadin ta, domin ta san komai da ya faru a gidansu ya sanar mata babu abun da ya ɓoye mata. Ta tuna alkawarin da tay masa lokacin da ta je asibiti dubo shi da ba shi da lafiya, bayan ya kama hannunta ya ce mata. "Neehal dan Allah duk runtsi karki bari a raba mu, Wlh idan na rasa ki mutuwa zan yi." Tana hawaye ta ce masa "Baza ka mutu ba Ya Sadik ɗina Insha Allahu kai ne mijina, na maka alƙawarin indai kana raye ba zan taɓa aurar wanin ka ba. Daga nan ta komar da tunanin nata kan Ahmad, mutumin da yay ta dakon soyayyarta tsawon shekaru, kuma ya taimaka mata a lokacin da take da buƙatar taimako, ga kuma Ƴaƴansa wanda suke k'aunarta take k'aunar su, zata so ta auri Ahmad ko dan ta kula da twins, ta maye musu gurbin mahaifiya da suka rasa. Ta gyara kwanciyarta tana son ta tantance wa tafi so a tsakanin su amma ƙwaƙwalwarta ta kasa yi mata wannan aikin. Ganin ta kasa samun mafita sai ta yanke shawarar zata tunkari ƴar'uwa kuma Aminiyarta wadda bata da kamar ta wato Haneefah da wannan maganar, domin ta bata shawara. Da wannan tunanin ta miƙe ta koma ɗakinta.
Mama kuwa sai da ta zubawa Daddy abinci ya ci sannan ta sanar masa da zuwan Kawu Musa da kuma yanda suka yi da shi. Daddy ya numfasa ya ce "Haka ne, kuma abun da ya faɗa gaskiya ne, nima da na so na ce ta turo mun shi yaron mu yi magana, amma sai na ce mu bari ta gama karatun ta, ta ɗan huta tukunna. Ko dan damuwar da ta shiga kwanaki akan rasuwar sauran samarinta." Mama ta ce "Haka ne, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi ya kawar da duk wata fitina a wannan karon a yi lafiya a gama lafiya." Daddy ya ce "Amin, yanzu ta fara turo mun shi yaron mu yi magana da shi, kafin akai ga maganar turo magabatansa." Mama ta ce "To ai ita yanzu wai ta rasa wa zata zaɓa, ka san baban Twins shi ma son ta yake." Mama ta kwashe duk yanda suka yi da Neehal ta sanar masa. Daddy ya yi murmushi ya ce "Daughter mai farin jini." Mama ta ce "Hmm, Allah ya kyauta, amma ni nafi mata sha'awar Ahmad ɗin, tunda shi babba ne, ga kuma yaransa suna buƙatar kulawar uwa, amma kuma idan ta zaɓe shi ta bar Sadik shi kuma bata kyauta masa ba, tunda ya riga Ahmad ɗin zuwa." Daddy ya ce. "Allah ya zaɓa mafi Alkhairi kawai." Mama ta ce "Amin Amin." Dad ya ce "Ɗazu Saratu ta kira ni, tana mun shirmen ku na mata." Mama ta ce "Shirmen me kuma?" Dad ya ce "Ita fa har yanzu bata haqura da batun Ameen da Hameedah ba, na ce mata ban da abunta Ameen fa ko shekara bai rufa da yin aure ba, idan ma auran zai ƙara ai ba yanzu ba, ballantana ma na san halin Ameen da ƙyar zai yarda ya ƙara aure." Mama ta ce "Allah ya kawo mata miji nagari ta yi auranta, amma Ameen a farko ma ya ƙi auren ta balle kuma yanzu." Daddy ya ce "Nima shi na gani dai Doctor." Mama ta ce "Allah ya kyauta."
Washegari ta kama Friday lecture ɗin safe gare ta 8_12. Kafin ɗaya ta dawo gida, bayan ta yi Sallah ta ci abinci ta shirya tay wa Mama Sallama ta tafi gidan Haneefah kamar yadda ta k'udurta. Haneefah tana kitchen tana suyar wainar fulawa ta ji ana knocking ƙofar falo, bata fita ta falo ba ta buɗe ƙofar kitchen ta baya ta lek'a dan ganin waye. Hango Neehal da ta yi yasa ta waro ido da ƙarfi ta ce, "Kan uban nan, zuwa babu sanarwa." Neehal ta yi murmushi tare da ƙarasowa ƙofar kitchen ɗin ta juya ido ta ce. "Ko in koma ne?" Haneefah ta rungume ta cikin murnar ganin ta ta ce, "Wa ya isa ke da gidan ki." Neehal ta ce "Shi na gani dai." Haneefah ta jata suka shiga kitchen jin wainar data bari akan wuta tana kamawa. Neehal ta riƙe hab'a ta ce "Unborn me cin wainar fulawa ne kenan?" Haneefah ta ce "Rufa mun asiri da wani batun unborn, ina da sauran shekara biyu da watanni kafin na kammala school, a hakan ma idan ba'a tafi strike ɗin ƙasar nan na gado ba. Wannan wainar fulawar ta Ya Faruq ce ya saka ni in yi masa, kin san masoyiyarsa ce." Neehal ta ce "Faɗi gaskiya dai, wannan murjewar da kyawun da kika yi duk na mene ne?" Haneefah ta ce "Auran kenan Yarinya." Neehal ta waro Ido ta ce "Hmm, ya kk ya gida da school?" Haneefah ta ce "Lafiya k'alau, Alhamdulillah ya Mamana? Duk da fushi nake da Mama ta ƙi zuwa gidana." Neehal ta ce "Kin san Mama, ita fita wahala take mata." Haneefah ta ce "Daga gida kike ko school?" Ta ce "Daga gida mana, takanas na zo dan na gan ki." Haneefah ta yi murmushi ta ce "Kin kyauta kuwa, ki shiga falo ki huta kafin na ƙarasa." Neehal ta ce "Toh, Ya Faruq yana nan ne?" Haneefah ta ce. "Eh yana ɗaki, da na ji shigowar mota ma na ɗauka abokansa ne, ashe my Besty ce ta mun surprise." Neehal ta yi murmushi ta wuce ciki. Bayan Haneefah ta kammala wainar ta kaiwa Ya Faruq ɗaki tare da sanar masa zuwan Neehal, ya fito suka gaisa cikin fara'a. Haneefah ta kawowa Neehal abinci da drinks da wainar data toya, tana ci suna hira. Sai da suka yi Sallar la'asar lokacin Faruq ya fita sannan Neehal ta zayyanowa Haneefah problem ɗinta.