← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 118

Sashe 113

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Ahmad ya ce "Princess!" Ta ce "Na'am my uncle." Ya ce "Kina waya da my in-law shine kika katse kika daga kira na?" Ta yi murmushi ta ce. "To ai kai Uncle ɗina ne, dole ya yi haquri in yi waya da kai, tunda cikin biyayya yake karka fasa ba shi auren ƴarka." Ya yi murmushi mai sauti ya ce. "Yaranki ne suka ce na kira ki suna so su taya ki murna." Neehal ta ce. "Allah sarki ƴaƴan albarka, amma fa sun so su yi late." Ahmad ya ce, "Lefin Daddy ne bai kira musu Aunty da wuri ba, yau kuma a gidan Ammi suka wuni babu mai Numbern ki a gidan." Neehal ta ce. "To a basu wayar in ji muryoyinsu ko hankalina zai kwanta, in ji sa'idar kewarsu dake cike a raina." Ahmad ya cire wayar daga kunnensa ya saka a speaker, ya ajiye a gaban su Afrah da suka zuba masa ido amma babu damar su yi magana, dan ya ce duk wanda ya yi masa surutu yana waya ba zai yi magana da Aunty ba, kuma ba zai ci cake ɗin celebration ɗinta ba. Cikin rige_rigen Magana suka ce. "Aunty congratulation." Neehal ta yi murmushi ta ce, "Thank you so much my kids, Allah yay muku albarka, yaushe zaku zo Aunty ta gan ku, dan na yi kewar ku sosai." Afrah ta yi saurin fara magana da faɗin. "Aunty Daddy ya ce sai bikin ki zamu zo, wai kin kusa zama amarya." Neehal ta murmusa ta ce. "Toh Shikenan Daughter, ya school?" Amrah ta ce. "Aunty now we are in primary one." Neehal ta ce "Masha Allah, yarana sun girma har sun shiga primary, what about islamiyya?" Afrah ta ce. "Muna suratul Jin." Ta ce, "Masha Allah, ku dage da karatu kun ji yaran kirki, ban da wasa sosai, idan kuna karatu sosai I will give you something special." Suka ce. "Toh Aunty, Daddy ya ce zaki yanka Cake, ki kawo mana mu ci." Ta ce. "Insha Allah, zan kawo muku." Ahmad ya ɗauke wayar jin za su kuma wata maganar ya ce. "Ya'isa haka kar a ƙarar mun da credit." Neehal ta ɓata fuska kamar yana ganin ta, cikin shagwab'a ta ce. "Kai Uncle, muna hirar mu mai daɗi zaka katse mana?" Ya ce. "Sorry Aunty, zan mayar da su gidan Ummi ne, idan na bar su kuma surutunsu ba ya ƙarewa sai mu yi dare, sannan kuma ina son na yi wata magana da ke." Neehal ta ce. "Tom ina sauraren ka." Ya lumshe ido ya buɗe ya ce. "Na kai kuɗin aure yau." Cikin razana ta waro Idanunta waje tare da dafe saitin zuciyarta da hannunta, saboda wani abu da ta ji mai zafi ya soki zuciyarta. A hankali ta shiga sauke numfashi amma ba ta ce komai ba. Ahmad ya cigaba da magana. "Neehal! Zuwa yanzu na riga na fitar da ran samun ki a rayuwata, duba da yadda bikin ki ya rage bai fi saura 1 month ba. Amma kuma zuciyata ta kasa daina tunanin ki, ta kasa rage sonki ko da kaɗan ne. Neehal! Ina tsoron ki yi Aure na dinga tunanin ki ina kwasar zunubi, hakan yasa na yanke shawarar yin aure nima nan da watanni kaɗan, na san idan ina da mata zata ɗauke mun hankalin tunanin ki." Ta lumshe idonta hawaye ya biyo ta ƙasan idon, ta sani ita mace ce mai kishi, yanzu ma kuma ta san kishin Uncle ɗin nata ne yake damun zuciyarta. Ta daure sosai dan ganin bai fuskanci halin da take ciki ba, ta ce. "Masha Allah My Uncle, Allah ya sanya Albarka, Allah yasa matar rufin asirinka ce, Allah ya kau da duk wata fitina dake cikin auren ku. Allah ya bata ikon riƙe ka da amana kai da twins." Cikin jin daɗi ya ce. "Amin, Amin Princess, na gode sosai. Amma Princess, Twins naki ne, babu matar da zan iya bawa ta riƙe mun su matuƙar kina raye. Dan haka bayan aurenki idan kun gama cin amarcin ku, Indai mijinki ya amince zan kawo miki su, ki riƙe ƴaƴanki har auransu idan Allah ya nufa." Ta buɗe idonta hawaye na cigaba da zuba daga idanun, bata jin zata samu wanda zai so ta kamar Uncle ɗinta, tana son twins sosai, amma ta san duk k'aunar da take musu ya fi ta son su, amma ya sadaukar da nasa son saboda ita, saboda ta yi farin ciki a rayuwarta. "Me yasa baza mu yi aure mu mori soyayyar da muke wa juna ba?" Ta yi maganar da a tunaninta a zuci ta yi, sai da ta ji Ahmad cikin raunin murya ya ce. "Allah ne bai yi ba Princess." Sannan ta yi realising ashe a fili ta yi maganar. Ta ja gwauron numfashi tana hasaso irin kulawar da zata samu a gurin Ahmad data aure shi. A hankali ta ce. "Thank you so much Uncle, Allah ya biya ka da Aljannah." Ya ce "Amin Princess, ke ma haka." Ta kawar da damuwar dake cin ranta ta ce. "Ya sunan Auntin tawa?" Ya ce, "Kina so ki sani?" Ta ce. "Eh mana, idan da hali ma har da pics ɗinta domin in ga ko ta dace da kyakkyawan Uncle ɗina, one in the millions." Ya yi murmushi ya ce. "Yanzu kuwa Princess, dan idan ba tay miki ba dole a canza ta, a samo duk kalar wadda kike so." Ta yi ɗan murmushi mai ciwo, a ranta ta ce. 'Da son samu ne ni nake so ka aura Uncle.' amma a fili sai ta ce masa. "Na san ma ta yi, Uncle ɗina ba zai yi zaɓen da zai bani kunya ba." Ya murmusa ya ce, "Sai dai kin gani zaki tabbatar, zan tura miki pics ɗinta yanzu ta WhatsApp." Ta ce. "Toh Uncle." Ya ce, "Good night, ki je ki cigaba da waya da in-law kar ya yi fushi, ga yaranki har sun fara bacci." Ta ce, "Ka shafa mun kansu, and my regard to Ummi, Abba, Zahra da my Aunty please." Ya ce "Duk za su ji Insha Allah, ki gaishe da Mama." Ta ce, "Zata ji Insha Allah." Daga haka suka yi sallama ya kashe wayar. Ta zare wayar daga kunnenta tare da zuba mata ido, tana jin zuciyarta babu daɗi sosai akan auren da Ahmad zai yi. Kenan duk soyayyar da yake cewa zai nuna mata idan sun yi Aure yanzu wadda zai aura zai yiwa ita. Sai ta ji wani kishi ya ƙara cika mata zuciya, a ganinta kamar ya yi sauri, ai da ya bari ya ga an ɗaura mata Aure sannan sai ya fara tunanin yi shi ma. Ta ɓata fuska tare da kunna data ta shiga WhatsApp dan ganin pics ɗin da ya ce zai tura mata. Ya turo kuwa kamar yadda ya faɗa, da sauri ta buɗe ta kalla, wata Black beauty ce, amma daga gani ta girme mata. Tana ta zuba murmushi a hoton, tana da kyawunta dai-dai gwargwado. Ta yi back, ta karanta gajeran bayanin da yay mata akan yarinyar, Nurse ce a asibitin da yake aiki, a nan suka haɗu sunanta Khadijah. Neehal ta masa reply da Allah ya tabbatar da Alkhairi. Sannan fita daga WhatsApp ɗin ta kira Sadik suka ci-gaba da hirar su. Washegari Sadik ya kawo mata prame mai ɗauke da hotonta, tare da banner mai ɗan girma, da turaruka as her graduation gift. Ranar Sunday wanda ya kama kwana biyu da yin graduation ɗinsu, ranar za su yi Graduation dinner da suka haɗa iya ƴan class ɗinsu, a wani hadadden hall ƙarami. Ƙarfe biyar da mintuna na yamma ta sakko cikin shirinta na tafiya. Tana sanye cikin wani lace kalar black and red. Ɗinkin riga da skirt akai mata wanda ya zauna dass a jikinta. Ta kafa kwatancen dauri mai V a kanta. Ta yi kyau sosai kayan ya ƙara haska farar fatarta. Turus ta tsaya a falon ganin Ameen zaune shi da Mama, dan ɓata tunanin ganin shi at this time ba, tunda ba ya zuwa gidan sai dare. Mama ta dube ta, ya ce. "Me ya faru na ga kin tsaya? ke da tun d'azu kike ce mun sauri kike." Ta ƙaraso cikin falon tana kallon shi wanda sai a lokacin ya d'ago ya dube ta. Kamar mara gaskiya ta ce. "Yaya Ina yini." Bai amsa ba sai cewa ya yi. "Where are you going?" Ta kalli Mama ba ta ce komai ba, Mama ta ce. "Party suke yi yau na graduation ɗinsu." Ya dubi Neehal yana ɗan haɗa rai ya ce. "Party kuma na me?" Mama ta ce. "Na ƴan class ɗinsu mana." Ya kafe ta da ido bai ce komai ba, tay saurin yin ƙasa da kanta cikin tsoron kar ya hana ta zuwa, dan ta san kaɗan daga aikinsa ne ya hana tan." A hankali ta ce. "Mama zan tafi." Mama ta ce, "Allah ya kiyaye hanya, ki kula fa sosai kuma karki yi dare." Ta miƙe tana faɗin. "Insha Allah Mama, sai na dawo." Ameen ya haɗe rai sosai yana kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya ce. "Wai wanne irin party ne da ba'a yi shi tun rana ba sai daf da Magriba za'a tafi? A dawo yaushe kenan?" Neehal ta yi raurau da ido kamar zata yi kuka, dan ta saddaqar hana ta kawai zai yi." Mama ta ce, "Bayan Magriba za ta dawo." Sannan ta mayar da kallonta ga Neehal ta ce. "Wuce ki tafi Daughter, saura ki bari hawayen idonki su zubo ki ɓata kwalliyar ki." Ta gyaɗa mata kai. Ameen ya miƙe yana faɗin, "Mu je in kai ki." Ta kalle shi ta ce, "To Yaya wa zai dawo da ni?" Ya mata wani kallo ya ce. "Ban sani ba." Mama ta ce, "Ku je Daughter, zan zo in ɗauko ki da kaina, kafin ku tashi ki kira ni." Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fice daga falon. Mama ta dube shi tana taɓa baki ta ce. "Yarinya tana cikin farincikinta zaka canza mata mood, ta kusa dai hutawa da takurar ka, tunda in ta yi aure ba za ka bi ta gidan mijinta ka nuna mata iko ba." Bai ce Komai ba, ya fice daga falon. A bakin Motarsa ya tarar da ita tsaye tana jiran shi. Bai mata magana ba ya buɗe Motar ya shiga, itama buɗewa ta yi ta shiga tana tutturo baki gaba. Ya kalle ta sau ɗaya ya ɗauke kai sannan ya kunna Motar suka tafi. Sai da suka hau kan titi ya tambaye ta gurin da za su, ta faɗa masa. Suna cikin tafiya ta ce, "Yaya." Ya ce. "Uhm." Sai kuma ta yi shiru, ya ce. "Mene ne?" Jin yanda ya yi magana cikin sanyin murya sai ya bata k'warin gwiwar tambayarsa abun da yake damunta a rai. "Yaya wai dan Allah me nake maka sometimes sai in ga kana ta shashshare ni." Ta yi maganar kamar zata yi kuka. Ya juyo ya kalle ta, sannan ya yi ɗan murmushi ya ce. "Kina son in daina miki hakan ne?" Da sauri ta ce. "Eh." Ya mayar da duban sa ga titi sannan ya ce. "Why?" Ta ce. "Saboda kai kaɗai ne Yayana, ina son na ga muna rayuwa kamar kowanne Yaya da ƙanwarsa." Ya yi shiru na tsawon mintuna biyu, kamar ba zai tanka ba sai kuma ya ce. "Yanzu kamar yaya muke rayuwar? Ai kamar kowa ne dama." Ta ce. "Ni dai bana son yanda muke, sai nake ganin kamar wani laifin nake maka." Ya juyo ya mata wani kallo da lumshashshun idanunsa, cikin wata irin cool voice wadda tasa Neehal lumshe ido ba tare data shirya ba, ya ce. "Yes akwai abun da kikai mun." Ta buɗe ido da sauri tare da waro su cikin mamaki ta ce. "Mene Yaya, ka faɗa mun ba zan kuma yi maka ba, Insha Allah." Ya murmusa ganin yanda ta ruɗe ya ce. "Zan faɗa miki amma ba yanzu ba, kuma kar ki ƙara tambaya ta, idan lokacin da ya dace ki sani ya yi zan sanar miki da kaina ba tare da kin kuma tambaya ta ba." Ta shagwab'e fuska ta ce. "Please Yaya ka faɗa mun yanzu." Ya ɓata rai ya ce, "Ba ki ji mene na ce ba ne?" Bata kuma magana ba, a ranta tana jinjina halinsa, yanzu zaka gan shi faran_faran take kuma sai ya canza. Ta kwantar da kanta a jikin kujera tana tunaninta ita kuwa wanne irin abu tay masa da yake mata haka? Har suka ƙarasa gurin babu wanda ya kuma yin magana. Sai bayan ya yi parking ne ta ce masa. "Thank you." Ya ce, "Saura kuma ki je ki ta rawa." Ta turo baki a ranta tana faɗin. 'Ko yaushe ya taɓa ganin ta tana rawa ma da zai ce kar ta yi." Ta buɗe ƙofar ta fita, ta kalle shi ta d'aga masa hannu. Ya gyaɗa mata kai kawai tare da bin ta da kallo harta shige gurin. Sai bayan isha'i sannan aka tashi, partyn ya yi musu daɗi da armashi yanda suke so. Ga mamakin Neehal Ameen ne ya dawo ya ɗauke ta, sai ta yi tunanin ko Mama ce ta tilasta masa ya zo, dan ta san halinta zata iya cewa tunda shi ya kai ta sai ya koma ya ɗauko ta........
Chapter 113 · 0% Book details