Sashe 64
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Turus ta yi tare da tsayawa a bakin ƙofar cikin shock, wani abu mai tsananin ɗaci ya tsaya mata a mak'oshi, dama a fusace ta taho saboda Fadeelah ta sanar mata Neehal ta zo tana cikin ɗakin, sai da ta mata masifar me yasa zata bar wata ta shigar mata ɗakin miji sannan ta taho ɗakin. Neehal ta yi ƙoƙarin zame hannunta daga cikin na Ameen jin ƙarar buɗe ƙofar ɗakin, kuma ko tantama ba ta yi Hafsat ce, amma ya ƙi bata damar hakan, sai ma ƙara matse hannunta yake a cikin nasa duk da shim ya ji shigowar Hafsan. Sai da ya goge mata hawayen fuskarta tass sannan ya saki hannunta yana murmushi ya ce "Mommy's girl, rigimammiya kawai." Neehal ta koma kan bedside locker ta zauna ta turo ɗan bakinta gaba. Duk yanda Hafsah taso daurewa kasawa ta yi, sosai fuskarta ta nuna ɓacin ranta. Ta janyo ƙafarta data ji ta mata wani iri tana bankawa Neehal harara ta ƙaraso cikin ɗakin, ji take kamar ta janyo ta ta shak'e ta dan tsananin ƙiyayyarta da take ji a ranta. Neehal ta dube ta da murmushi akan fuskarta ta ce "Ina yini Aunty Hafsah." Kamar an mata dole ta amsa da faɗin "Lafiya." Neehal ta ce "Ya mai jiki?" A ranta ta ce ''Gashi nan a gabanki ai, kin ga jikin nasa munafuka' Amma a fili sai ta ce "Da sauqi." Daga haka Neehal ta ja bakinta ta tsuke sai ma ƙoƙarin tashi da ta yi dan ta ba su guri. Hafsah ta ɗan saki fuska ta zauna a kan gadon ta kai hannunta jikin Ameen wanda idanunsa ke lumshe ta ce "Baby ya jikin naka?" Ameen ya buɗe idanunsa ya kalli Neehal ba tare da ya amsa mata ba, ya ce "Ki bata abinci, daga school take." Neehal ta miƙe ta ce "No Yaya am full." Wani kallo ya wurga mata wanda yasa ta yin ƙasa da kanta. Hafsah ta had'iye wani malolon baƙin cikin da ya tsaya mata a mak'oshi, 'wato ba ma zai amsa mata magana ba, sai ma bata umarnin da bawa wata banzar yarinya abinci. Amma da yake makira ce sai ta dake kamar ba ta ji komai ba. Cikin kissarta ta ce "Ayya, ai ban sani ba sisina, mu je na baki abinci ki ci" Neehal zata yi magana wayarta dake hannunta ta hau vibrate, ta duba tare da d'agawa ganin Mama ce. Mama ta ce "Kin je gidan Ameen ɗin." Neehal ta ce "Ehh." Mama ta ce "Ya jikin nasa." Ta ce "Da sauqi." Mama ta ce "Bacci yake?" Neehal ta ce "A'a, idonsa biyu yana ma zaune." Mama ta ce "Okay, bashi wayar." Neehal ta miƙa masa ba tare da ta yi magana ba, ya karb'a tare da kara wayar a kunnensa, ko da ba'a faɗa masa ba ya san Mama ce. Gaisawa suka yi, Mama ya masa ya jiki? Sannan ya bawa Neehal wayar. Ameen ya dubi Hafsah wadda ke kallonsa ya ce "Ina kika ajiye mun my phones? Mum said ta kira ni ban yi picking ba." Hafsah ta ce ,"Suna Bedroom dina, bari na ɗauko maka." Sai kuma ta marairaice fuska ta dafa kafaɗunsa tare da faɗin "Babyna duk ka rame, ciwon nan yana wahalar mun da kai, nice mai cikin amma kai ne da laulayin." Neehal ta ɗan tab'e baki tare da fita daga ɗakin. Ameen bai cewa Hafsah komai ba, sai idanunsa da ya mayar ya lumshe. Neehal ta fito falo ta zauna ta ɗauko wayarta ta shiga latsawa, su Fadeelah kuwa sai hirarsu suke. Hafsah ta fito ta shiga bedroom ɗinta ta ɗauko wayoyin Ameen ta kai masa, sannan ta fito ta zauna kusa da k'awayenta ba ta ko kalli inda Neehal take ba. Fadeelah ce ma take ɗan sako ta a cikin hirar tasu, ita kuma sai dai ta yi murmushi kawai. Ganin Magriba ta kusa ta miƙe ta dube su ta ce "Aunty Hafsah zan wuce Allah ya ƙara sauƙi." Bata jira amsarta ba ta mai da dubanta ga su Fadeelah tana murmushi ta ce "Sai anjimanku." Fadeelah ta ce "Har zaki tafi Neehal? To ki gai da gida da Mama." Neehal ta ce "Mama zata ji." Sannan ta juya ta fice daga falon. Hafsah ta bita da harara tare da jan dogon tsaki bayan ta fita. Fadeelah ta kalle ta ba ta ce komai ba, a ranta tana mamakin wannan hali na ƙawartata. Neehal tana koma wa gida Mama ta kalle ta, ta ce "Kuka kika yi ko Neehal?" Neehal ta yi shiru, Mama ta ce "Allah ya shirye ki, ya jikin nasa?" Kamar zata kuma wani kukan ta ce "Da sauqi, amma Mama daga gani Yaya yana jin jiki sosai, duk ya rame." Mama ta ce "Ki masa addu'a, ba kuka ba." Ganin idanunta har sun fara ƙyallin k'walla. Da daddare Sadik ya zo suka sha zancensu, sun daɗe suna hira wanda kusan gaba-ɗaya hirar a kan bikin Haneefah suka yi ta. Lokacin da Sadik ya koma gida kamar kodayaushe idan mahaifinsu yana gari, iyayensa duka suna zaune a main Parlour, sai dai yau babu k'annensa. Ya shigo da sallama kan sa a ƙasa, suka amsa masa baki ɗaya. Umma ta ce "Um su Sadik yanzu kullum sai an je zancen ne?" Ran Maamah ya ɓaci amma ba ta ce komai ba. Abbansa ya ce "Idan ya je zance laifi ne?" Cikin kissarta da son ɓata Sadik ɗin a idon mahaifinsa ta ce "Ba laifi ba ne Abbansu, kawai dai na ga ya kamata a san inda yake zuwa zancen ne, domin a tabbatar da tarbiyyar yarinyar." Abba ya kalli Sadik dake tsugunne ya ce "A ina gidansu yarinyar da kake zuwa yake?" Cikin ladabi Sadik ya ce "A Nasarawa gidansu yake, sunan mahaifinta Alh. Muhammad Tafida." Abba ya maimaita sunan kamar mai son tuno wani abu "Alh. Muhammad TAFIDA? kamar na san sunan nan, amma dai zan bincika, dan kamar Yadda Ummanku ta faɗa ya kamata mu san inda kake zuwa ɗin, idan gidansu yarinyar gidan tarbiyya ne sai ka cigaba da zuwa, idan kuma akasin haka ne kasan sauran." Ya ƙarashe zancen yana kallon Sadik. Sadik ya gyaɗa masa kai zuciyarsa babu fargabar komai, dan yasan babu wani abu bad da za a samu a gurin Neehal ko iyayenta Insha Allahu.
Washegari da safe sai ga Hajiya ta zo wai ta zo duba Ameen ne. Neehal tana bacci ta ji Maganar Hajiya a kanta. A hankali ta buɗe idanunta dake cike da bacci, cikin muryar bacci ta ce "Kai tsohuwar nan baza ki bar mutum ya yi ƙiba ba, daga zuwanki ina baccina mai daɗi kin katse mini." Hajiya ta ce "Wanne irin baccin asara ne wannan har tsakar rana? Yaushe Faɗiman ta lalace har ta barki kike irin wannan baccin? Haka zaki je gidan mijin kina sakin baki kina sharar bacci." Neehal ta tashi zaune tana ƴar miƙa tare da yin salati. Hajiya ta ce "Ni ki yi ki tashi ki shirya ki raka ni gidan Aminu yaron kirki irin albarka in dubo sa, duk da ma sai jiya Uwartasa ta faɗa mun rashin lafiyar tasa, ban da haka da tuni ban zo ba." Neehal ta kalli agogon dake bangon ɗakin ta ce "Taɓ, sai dai direban Mama ya kai ki, ni school zan tafi yanzu ina da exam 12." Bata bi takan mitar Hajiya ba ta tashi ta shige toilet. Tana fitowa ta ga wayarta dake kan gado tana haske, ta ɗauka ta ga Ameen ne yake kiranta. Ta d'aga da sallama a bakinta, Al'ameen ya amsa mata. Ta ce "Ina kwana Yaya, ya jikin naka?" Ya ce "Da sauqi, me yasa jiya kika taho baki mun sallama ba?" Ta ce "I thought ka yi bacci ne lokacin." Ya ce "Ko dai kina sauri ki tafi saboda saurayinki zai zo?" Neehal ta ce "Allah ba haka ba ne Yaya" ya ce "Amma ai yazo ɗin ko?" Neehal ta yi shiru tana murmushi ƙasa ƙasa, ya ce "Uhm, to me yasa yau baki kira ni kin ji lafiyata ba?" Sai ta ji abun wani iri, ita da tun yana gida ma basa wata waya balle yanzu da ya yi aure, ko yana nufin dan bashi da lafiya ne bata kira ta ji jikin nashi ba? ta ce "Yanzu na tashi daga barci ne I'm sorry" Ya ce "Alright, i will call you later" Daga haka ya kashe wayar. Ta bi wayar da kallo kamar zata gan shi a ciki, daga baya kuma ta ajiye ta cigaba da sabgarta.
Hajiya tana duban Mama bayan ta gama rattabo mata yanda suka yi da Neehal ta ce "Wai niko Faɗima har yanzu yaran nan shiru babu labarin wani nasu?" Mama ta ce "Babu Hajiya har yanzu, tun muna zuba idon ganin kira har mun gaji." Hajiya ta ce "Ikon Allah, to ko dai ba ƴan ƙasar nan ba ne?" Mama ta ce "Waya sani ne, sai Allah." Hajiya ta ce "Allah ya kyauta, suna inane ma ban gansu ba." Mama ta ce "Suna makaranta, sai yamma suke dawowa." Hajiya ta ce "Allah sarki Janar, Allah ya saka masa da Alkhairi, shi da ba ya gajiya da aikin Allah, har ya saka su a makaranta."