Sashe 101
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tana Kuka ta janyo ƙaramar trolley ta zuba kayanta da bata ma tsaya zab'a ba kawai buɗe wardrobe ta yi ta kwaso. Ta saka hijabai guda biyu a ciki ta zuge. Ta ɗauki wani ta zira a jikinta, ta koma bakin gado ta zauna tana cigaba da kukan ta. A haka Mama ta shigo ta same ta. Cikin takaici Mama ta ce "Neehal kukan ne har yanzu kamar wadda akaiwa wani mugun abun, haka zaki je gidan mutane kina musu kuka?" Ta yi shiru tare da daina kukan. Mama ta tab'e baki ta ce "Ki fito yana falo yana jiran ki, kuma ki cigaba da kukan kin san halinsa dai." Ta goge hawayen fuskarta ta ce "Ki yi haquri Mama na daina." Mama ta ce "Allah ya shirya mun ke, ya nuna mun ranar da zaki girma ki daina wannan kukan, ko jariri haka ya gan ki ya bari a kuka Neehal." Ta turo baki ba ta ce komai ba, ta miƙe ta kwashi wayoyinta ta zuba a small handbag. Mama ta kama hannunta ta ce "Ki saki ranki mana Daughter, ko kuma kin fi so idan kewarki ta dame ni in dinga tuno fuskarki a cukule." Ta yi murmushi saboda yanda Maman ta yi magana. Itama murmushin ta yi ta shafa kuncinta ta ce, "Je ki wanke fuskarki maza ƴar albarka ta." Ta gyaɗa mata kai tare da tashi ta shige toilet. Mama ta miƙe ta fita, a falo ta tarar da Ameen zaune inda ta bar shi. Ta zauna a kusa da shi ta ce "Gata nan zuwa, saura kuma a dinga ci mun zalin yarinya idan an je." Ya yi murmushi ya ce "Ƴar taki ce bata ji ai ba daga ni ba ne." Mama ta ce "Ni dai na faɗa maka, idan na ji ba dai-dai ba da kaina zan zo in ɗauke ƴata." Ya ce "Baza ma ki ji ba Insha Allah." Dai-dai nan Neehal ta fito daga ɗaki tana jan trolley, Ameen ya bi ta da kallo. Ba tare data kalle shi ba ta ce "Ina kwana." Ya ce "Lafiya." Tare da miƙewa ya karb'i trolley'n hannunta ya fice daga falon. Ta dubi Mama ta ce "Daddy ya fita ba mu yi sallama ba." Mama ta ce "Sauri yake ne, amma ya ce idan ya dawo da daddare zai zo har gidan Ameen ɗin ya gan ki." Ta shagwab'e fuska ta ce "Please Mama ku zo tare." Mama ta ce "To Allah ya kai mu, make sure dai kin ɗauki komai na zuwa gurin aikin ki?" Ta girgiza kai tare da faɗin. "Mama wai kwana nawa zan yi ne?" Mama ta ce "Just 2 days." Ta gyaɗa mata kai sannan ta juya ta koma ɗakinta, ta ɗauko laptop ɗinta da duk wani abu da zata buƙata a gurin aiki, sannan ta fito. Mama ta bata kuɗi ko zata buƙata, ta ce mata a'a ta ɗauki ATM ɗinta, idan tana buƙata zata ciro. Har waje Mama ta raka ta, amma iyakacin ta bakin part ɗinta ta koma. Gabanta na fad'uwa ta nufi parking space inda ta san yana jiran ta, a hankali take tafiya har ta ƙarasa. Kafin ta ƙarasa gurin Motarsa ya buɗe ya fito ya buɗe mata baya, ba tare da ya ce komai ba ya karb'i laptop ɗin hannunta ya saka a bayan Motar, ya mayar ya rufe sannan ya buɗe mata gaban Motar. Cikin mamaki take kallon sa zuciyarta cike da tsoro, gani take kamar wani abun yake shirya mata na punishment ɗin da ya ce zai mata, sai ta kasa shiga Motar. Ya haɗe rai amma cikin sanyin murya ya ce "Ko sai na ɗauke ki na saka ki ne?" Ta kalle shi ta turo baki sannan ta shiga Idanunta cike da k'walla. Ya zagaya ya shiga mazaunin driver, ya yi looked Motar sannan ya kunna ta ya yi reverse suka fice daga gidan. Ta lumshe idonta tare da kwantar da kanta a jikin kujera. Ji take kamar garin zata bari saboda damuwa, dan ita bata taɓa yin tafiyar kwanaki ba tare da Mama ba, and kuma tana tunanin yadda zata yi kwanaki a gidan matar da bata k'aunarta ko kaɗan, Matar dake mata fuska biyu a gurin Yayanta da Mamanta. Har suka je gidan babu wadda ya yi magana a cikinsu, sai karatun Alkur'ani ne yake tashi a cikin Motar. Ta buɗe idonta jin Motar ta tsaya, idanunta suka sauka a cikin nasa saboda juyowa ya yi sosai yana kallonta, harara ta yi tsammanin samu daga gare shi amma sai ta ga saɓanin haka, wani tattausan murmushi ya sakar mata, murmushin da tun tana yarinya yake matuƙar burge ta, kuma bata tunanin akwai na biyun shi a kyau a idonta ba. Ta mayar da idonta ta lumshe cikin jin bugun zuciyarta na sauyawa, gaba-ɗaya ya juye mata ya koma Mamanta data baro a gida, kamar Ameen da Mama ta ɓaci, babu abun da ya baro nata, hatta yanayin kallon su iri ɗaya ne, the only difference is shi Namiji ne ita kuma mace ce. A hankali ya ce "Cry cry girl, kukan ne dai?" Ta buɗe ido tare da turo baki gaba ta ce "I start missing my Mum." Ya ce "Sorry, ai taimakon mu zaki yi Mummy's girl." Ta ɓata fuska ba ta ce komai ba, shi ma bai kuma magana ba ya buɗe Motar ya fita, itama bin bayan shi ta yi ta fito hannunta riƙe da handbag ɗinta. Ya buɗe bayan Motar ya ɗauki laptop ɗin sannan ya fara tafiya ta bi bayan sa. Babu kowa a falon ƙasan da suka shiga, amma fess yake a gyare sai tashin k'amshi yake, sama ta ga ya hau hakan yasa itama ta bi bayan sa. Bedroom ɗin Hafsah ya shiga ita kuma ta zauna a falo, ba jimawa ya fito ya ce ta shiga ɗakin. Ta tashi ta shiga a tunaninta Hafsan tana ciki, amma sai ta ga babu kowa, ga laptop ɗinta ya ajiye mata akan bedside locker. Ta zauna a bakin gado tana bin ɗakin da kallo, dan bata taɓa shigar sa ba sai yau. Knocking ƙofar da akai yasa ta tashi ta je ta buɗe, ɗaya daga cikin masu aikin gidan ce, cikin girmamawa ta gaishe da Neehal sannan ta bata trolley ɗinta tana faɗin. "Gashi mai gidan ya ce akawo miki." Ta karɓa tare yin murmushi ta ce "Na gode." A ɗakin Hafsat zata zauna kenan? A fili ta ce "Lallai ma Yaya." Sai kuma ta tab'e baki da ta yi tunanin wani abu. Tana ajiye trolley'n ya turo ƙofa ya shigo da sallama, ta amsa masa, ya dube ta ya ce "Ki zo ku gaisa." Ba ta ce komai ba, dan ta gane wadda yake nufi, ta fito ta biyo bayan sa suka shiga ɗakinsa, Hajiya Hafsat na kwance akan gado idanunta akan ƙofa. Already ta san da zuwan Neehal gidan dan Ameen ɗin ya sanar mata tun jiya, kuma ko kaɗan bata ji daɗin hakan ba, babu yanda zata yi ne kawai. Neehal ta ƙarasa bakin gadon ta ce "Ina kwana Aunty Hafsah, ya jikin?" Cikin fake smiling Hafsah ta ce "Lafiya k'alau sisina, ai na yi fushi tunda sai yau zaki zo duba ni, da haihuwa na yi ma sai Babyn ya kwana sannan zaki zo ki gan shi ko?" Neehal ta saci kallon Ameen da ya zauna a kusa da matarsa ta ce "A yi mun afuwa Aunty, na je gurin aiki ne, sai bayan da Mama ta dawo take faɗa mun abun da ya faru, I hope dai jikin naki da sauƙi." Hafsah ta ce "Jiki da sauƙi, Welcome, Yaya ya ɗauko ki zai wahalar wa da Mama ke da aiki ko?" Ta ƙarashe zancen da kallon Ameen, yay mata wani kallo bai ce komai ba. Neehal ta yi murmushi ta ce "Babu komai Aunty, mene abun wahala a aikin gida?" Hafsah ta ja tsaki a ranta cikin tsanar Neehal ɗin, maganar nan da suke yi ma daure zuciyarta kawai take yi, tsanar yarinyar kullum ƙaruwa take a ranta, ko dan yanda Ameen yake nuna caring a kanta ne? Gashi duk ganin da zatay mata sai ta ga kamar ƙara kyau take, ga iyayi idan tana magana, ita a dole mai class. Ta ja ɗan ƙaramin tsaki ba tare da ta san a fili ta yi ba tare da yamutsa fuska, kallon da Ameen yay mata ne ya fargar da ita, ta taune lip ɗinta tare da dafe cikinta dan ya yi tunanin ciwon cikin ne ya sata tsakin. Ya ɗauke idonsa daga kanta a kallon da yake mata data rasa yaren da zata fassara shi, shi ba kallon tuhuma ba shi ba na gargadi' ba. Neehal ta ce "Sannu Aunty, ko kina buƙatar wani abun ne?" Hafsah ta girgiza mata kai alamar a'a. Ta ce "Allah ya sauwaqe." Sannan ta da juyawa ta fice daga ɗakin. Hafsah ta bi ta da kallon tsana, tana juyowa suka haɗa ido da Ameen yana mata irin kallon d'azu. Sai ta hau borin kunya ta fara yamutsa fuska tana faɗin. "Baby cikina na damuna da ciwo." Ameen ya janyo ta jikinsa ya ce "Sorry, bari na kira Mama ko akwai maganin da za'a baki ya daina ciwon." Ta gyaɗa masa kai, tare ƙara shigewa jikinsa.