← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 118

Sashe 4

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wayarta da sim ɗinta da ba kowa ke da shi ba yake ciki ake kira, missed call ɗin Mama ta gani da na Anwar, Layin Mama ta fara kira, ringing daya Mama ta d'aga, Neehal ta ce "Hello Mama" Mama ta ce "Wato Neehal har yanzu ba ki koyi sallama a waya ba ko?" Neehal ta ce "Sorry Mamanah" Mama ta ce "Sorry for your self, kin dawo gida ne?" Neehal ta ce "Eh tun ɗazu" Mama ta ce "Dad fa?" Neehal ta ce "Shima na ga car ɗinsa a parking space, amma ban je part d'in shi ba, na tsaya Sallah ne" Mama ta ce "Ok, kin ci abinci dai ko? Dannasan halinki da zama da yunwa" Neehal ta ce "Na ci snaks" Mama ta ce "Haka dai ki ka iya, Ina Hajiya?" Neehal ta ce "Ta na ɗakinta, Yaushe za ki dawo Mama?" Mama ta ce "Sai 10, dama kira na yi in ji ko kin dawo, zan yi abu yanzu ki kula sosai" Neehal ta ce "Toh Mama sai kin dawo" daga haka ta katse wayar. Number'n Anwar ta dannawa kira, sai da ta kusan katsewa ya ɗauka, Neehal ta ce "Amincin Allah ya tabbata ga farin cikin zuciyata, dafatan ka wuni lafiya, kaina bisa wuya na, yau nasan Queen ta yi lefi" Anwar ya lumshe idansa cikin jin daɗin kalamanta da tsananin farin cikin jin muryarta ya ce "Tare da ke tauraruwar da ke haskaka birnin zuciyata, amma tabbas yau kam Queen ta mini laifi babba ma" Neehal ta waro kyawawan idanunta waje tana murmushin jin daɗin kasancewarta da masoyinnata ta ce "Haba my Habibi, a yi haƙuri mana insha Allahu Queen ba za ta kuma ba" Yanda ta yi maganar cike da shagwab'a ya sa sai da tsigar jikin Anwar ta tashi, ya ɗan sauke numfashi ya ce "Shikenan ai Queen ɗita ta wuce gaban komai a gurina, amma dai yau ta mini k'wauron jin muryarta wanda hakan ya sa na rasa nutsuwata gabad'aya" Neehal ta ce "Am so sorry mijin, missed call ɗin farko da ka mun ina bacci ne, da na tashi kuma na kira ka ba kai picking ba, har na je gurin aiki na dawo ba ka kira ba, sai yanzu" Anwar ya ce "Sarkin bacci, to ya kike?" Neehal ta ce "Alhamdulillah sai kewarka da ta cikamun zuciya da gangar jikina" Anwar ya ce "Missed You too my love, ya Mamana da Yayanah da Dad ɗinmu?" Neehal ta ce "Duk sunanan lafiya k'alau, ya Amminah?" Anwar ya ce "Masha Allah, Ammi tananan klu" Neehal ta ce "Ka gaidata Please da sauran 'yan gidan" Anwar ya ce "Za su ji Insha Allah, yaushe zan zo in ganki ne na yi missing kyakkyawar fuskarnan taki" Neehal ta ce "Gobe mana" Anwar ya ce "Allah ya kai mu amaryata" Hira suka ci gaba da yi irin ta masoya mai cike da nishad'i da farin ciki, ba su wani jima ba su ka yi sallama Neehal ta ce za ta je part d'in Dad ne.

Da sallama ta shiga falon Dad, Dad na zaune akan kujera ya na karatun jarida time ɗin Ameen ya fita, Dad ya d'ago tare da amsa sallamar Neehal ɗin fuskarsa ɗauke da murmushi, Neehal ma murmushin ta ke yi ta ƙaraso cikin falon tana faɗin, "My Dad yau na yi missing ɗinka over" Dad ya ce "Nima haka my daughter, ya aikin" Neehal ta ce "Alhamdulillah" tare da zama a gefen Dad d'in, Dad ya ce "Ɗazu bayan mun fito daga meeting na kunna TV na ce bari in ga daughter nah, time ɗin ki na labaran yamma" Neehal ta yi murmushi "Dad ya ce, yanzu nake shirin kiranki na ce ki kawo mini fruits" Neehal ta Mik'e tana faɗin "Bari na had'o maka to" Dad ya ce "Yawwa ɗiyar albarka" Neehal ba ta wani jima ba, ta dawo ɗauke da vowl wanda ta yayyanka fruits d'in a ciki, ta ajiye akan Centre table ɗin dake gaban Dad, Dad yana dubanta da murmushi a kan fuskarsa ya ce "Thank you Amarya" Neehal ta rufe fuskarta cikin jin kunya. Tare su ka sha fruits d'in da Dad, ya na ta zolayarta da yake Dad mutum ne mai barkwanci, hirar su suke irin ta ɗa da mahaifin da ya ja ƴaƴansa a jiki, har sai da Mama ta dawo sannan Neehal ta koma part ɗinsu. Sai da ta biya ɗakin Hajiya ta yi mata sai da safe sannan ta wuce nata ɗakin, wanka ta fara yi sannan ta ɗauki wayoyinta ta kwanta akan lumtsumeman gadonta bayan ta kashe light d'in ɗakin, data ta kunna ta shiga yanar gizo, sai wajen 1pm ta kashe datar bayan ta gama shan hira da masoyinta Anwar da besty'nta Haneefah da sauran freinds ɗinta da 'yan'uwa da abokan aiki. Misalin ƙarfe uku da ƴan mintuna na daren Mama ta kirata, ɗagawa ta yi muryarta cike da bacci ta yi sallama, Mama ta amsa mata tare da faɗin "Ki tashi ki yi Sallah toh" Neehal kamar za ta yi kuka ta ce "Mama dan Allah ki bar ni na yi bacci na, gobe fa da safe za ni aiki, kuma ban daɗe da kwanciya ba" Mama ta ce "Ni na hanaki kwanciya da wuri, ai kin san da sallar ki ka tsaya chat" Neehal ta ce "Ba fa chat na yi ba, karatu na yi, kin san 2 weeks ya rage mu fara exam" Mama ta ce "Na ji, ki tashi ki yi Sallar dai, ko raka'a biyu ce, kin ga auren ki ya kusa, ki roƙi Allah ya kawar muku da fitintunu a zama auranku, yanda auren yanzu ya zama na zamani, dole sai mun dage da addu'a" Neehal ta ce "To Mama" Mama ta ce "Yawwa my daughter, ki yi addu'a sosai, sharrin mutum da Aljan Allah ya kare mu" Neehal ta ce "Ameen, bye" Mama ta katse wayar, Neehal ta yunk'ura ta tashi ta shiga toilet dan d'auro alwala.

Washegari, bayan ta idar da sallar asuba ta yi karatun Alkur'ani mai girma izifi biyu, sannan ta ɗauko materials ɗinta na school ta ɗan dudduba, gari na fara haske ta tashi ta gyara ɗakinta, sannan ta faɗa toilet ta yi wanka. 7:30 ta sakko ƙasa cikin shirinta na zuwa gurin aiki, ta na sanye da hijabinta wanda ya zo mata har ƙasa, Mama ta na kitchen ta na haɗa breakfast, ƙarasawa kitchen d'in ta yi ta ce "Morning Mum" Mama ta ce "Morning dear, har kin fito" Neehal ta ce "Ehh, kin san yau Sunday za mu haɗa labaran week d'in gabad'aya dole sai na je da wuri" Mama ta ce "Amma dai za ki tsaya ki yi break ko" Neehal ta ce "Idan na je can zan ci, bari na ɗiba cake" Mama ta ce "A'a ki dai tsaya ki ci abincin ko kaɗanne nasan halinki ba ci za ki yi ba" Neehal ba ta musa ba, ta haɗa tea a ƙaramin cup ta d'ebi irish d'in da Mama ta soya kaɗan, ta koma falo ta ci. Kayan ta dawo kitchen ta ajiye bayan ta gama ci, ta yi wa Mama sallama, Maman ta mata addu'a ta fice. Sai da ta biya part d'in Dad sharp_sharp ta gaishesa sannan ta fito ta tafi........✍️
[7/21, 8:59 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*

_By_
_Zeey Kumurya_

*0️⃣4️⃣*

Bayan Mama ta gama haɗa breakfast din ta ɗibi na Dad ta haɗa masa a cikin tire, tana ƙoƙarin fita Dije mai aiki ta shigo kitchen d'in, ta risina ta ce "Ina kwana Hajiya, dafatan kin tashi lafiya" Mama ta ce "Lafiya kalau Dije, yawwa dama na gama sai ki haɗa wanke_wanke ki yi ki gyara kitchen d'in" cikin girmamawa Dije ta ce "Toh Hajiya" Mama ta fita daga kitchen d'in, Zulai mai aiki ta na mopping a falon, ganin Mama ya sa ta ajiye mopper ɗin hannunta ta taho da sauri ta na faɗin "Sannu da fitowa Hajiya" Mama ta ce "Yawwa mun tashi Lafiya" Zulai ta ce "Lafiya ƙalau Hajiya" tana ƙoƙarin karɓar kayan hannun Mama, Mama ta ce "Ki barshi ki je ki ci gaba da aikin ki kawai, idan kun gama sai ku ɗibi abinci a kitchen ku karya" Zulai ta ce "Toh Hajiya" ta koma ta cigaba da aikinta, Mama kuma ta nufi part din Dad.
Chapter 4 · 0% Book details