Sashe 31
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Had'ad'd'en asibiti ne wanda daga gani babu tambaya na masu hannu da shuni ne, wata mata ce tsaye a Emergency ward tana kaiwa da komo wa tare da karanto duk addu'ar da ta zo bakinta cikin kuka, kallo É—aya za kai mata ka fuskanci tana cikin tashin hankali ba kaÉ—an ba. A gefe guda kuma wata yarinya ce zaune akan kujerun dake gurin wadda ba za ta wuce shekara 15 ba, tana rufzar kuka da dukkan Æ™arfinta. Wani Babban Mutum ne ya Æ™araso gurin tare da wasu mutane biye a bayansa, matar na ganinsa ta Æ™ara fashewa da kuka tana faÉ—in, "Alhaji ba a gansu ba ko? Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, ya ALLAH ka bayyana mana yaran nan a raye ko a mace, Allah ka kare su da kariyarka a duk inda suke, Allah kasa suna hannu na gari, Allah ka dubi maraicinsu." Sai kuma ta fashe da kuka abun gwanin ban tausayi. Ta Æ™arasa inda mutumin yake ta riÆ™e hannunsa tana faÉ—in "Alhaji dan Allah ka taimake ni kasa a nemo yaran nan, ko dan mummunan halin da mahaifinsu yake ciki sanadiyyar É“atansu, dan Allah Alhaji kar na rasa É—anaa." Mutumin wanda ga dukkan alamu mijinta ne cikin lallami ya ce, "Police suna can suna iya bakin Æ™oÆ™arin su wajen ganin sun nemo yaran, kuma insha Allahu muna saran za a gansu, ki kwantar hankalinki kin ji." D'ago da jajayen idanunta da suka ci kuka suka koshi ta yi tana duban sa ta ce "Ta yaya hankalina zai kwanta Abbansu, alhalin ga yarona can kwance rai a hannun Allah, jikokina kuma an neme su an rasa ka faÉ—a mun ta yaya hankalina zai kwanta!" Ta Æ™arashe maganar cikin tsananin kuka. Mutumin ya sauke numfashi cikin Æ™oÆ™arin É“oye tasa damuwar ya ce "Allah yana sane da mu Fatima, kuma insha Allahu shi zai kawo mana mafita, ke dai kawai ki dage da addu'a." Ta gyaÉ—a masa kai tare da sakin hannunsa ta zauna saboda jirin dake neman yar da ita, mutumin ya nufi gurin da yarinyar dake ta kuka take ya zauna tare da janyo ta jikinsa ya fara rarrashinta. Mutanen da suka zo tare da mutumin suka jinjina kai zuciyoyinsu cike da tausayin wannan ahali. Matar ta d'aga hannunta sama a fili take faÉ—in, "Ya Ubangiji na roÆ™e ka ka tashi kafaÉ—un *AHMAD* É—ina, ka bayyana masa yaransa da gaggawa a duk inda suke, Allah duk wanda yake da hannu a É“atan yaran nan Allah ka tona asirinsa." Gaba-d'aya mutanen wurin suka amsa da "Amin ya Allah.".........âœï¸
[7/21, 9:01 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*2ï¸âƒ£0ï¸âƒ£*
Bayan wasu mintuna wani likita ya fito daga ɗakin da Ahmad yake yana goge fuskarsa da handkerchief, Matar ta riga kowa mik'ewa tana faɗin "Doctor, ya ya jikin nasa?" Likitan ya sauke numfashi yana dubanta ya ce "I'm sorry to say Hajiya, Amma jikinsa da sauƙi Alhamdulillah, ki ta yi masa addu'a kawai." Bai jira amsarta ba ya juya ga Alhajin ya ce "Ka biyo ni office Alhaji." Matar tana sheshshek'a ta ce "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, likita me kake nufi? Har yanzu kenan Ahmad be farfaɗo ba?" Alhaji ya dube ta ya ce "Ki zauna ki yi addu'a kamar yadda Doctor ya ce, zan je inji bayaninsa." Matar ta gyaɗa kai tana salati ta koma ta zauna jagwab, yarinyarta ta matso kusa da ita tana sauke numfashi ta ce "Ummi, tunda har yanzu ba'a gansu ba ki kira gidan su Ammi ki sanar musu, ya kamata zuwa yanzu su ma su san halin da ake ciki." Ummi ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Tun d'azu naso kiran su Zahra, Abbanku ne ya hana ya ce kar a tayar musu da hankali a bari aga abun da hali zai yi, amma yanzu tunda ba a gansu bari na kira Yaseer na faɗa masa, kin san Ammin tana da hawan jini yanzu in ta ji sai ya tashi, amma shi Yaseer ɗin ya san ta yanda zai faɗa mata hankalinta ba zai tashi sosai ba." Zahra ta gyaɗa mata kai kawai cikin sanyin jiki.
â–ªï¸â–ªï¸â–ªï¸â–ªï¸â–ªï¸â–ªï¸â–ªï¸â–ªï¸â–ªï¸â–ªï¸â–ªï¸
           *KANO*

Jiki a sanyaye su Mama suka kwantar da yaran a wani spare room dake part ɗin Daddy, sosai al'amarin yaran ya girgiza kwanyar Mama, tafi 5 minutes tana kallon su kafin ta sauke numfashi ta juya ta fita bayan ta lullub'a musu bargo, Haneefah dama suna kwantar da su ta fice. A falo suka ci karo da Aunty Sadiya da Aunty A'isha. Aunty Sadiya ta dubi Mama ta ce "Yaya Fatima kin ga Neehal ɗin?" Mama ta ce "Eh, ashe gida ta dawo wai kanta na ciwo." Aunty A'isha ta ce "Ayya, hayaniya ce Allah ya sauwaaqe." Aunty Sadiya dake kallon Mama ta ce "Lafiya kuwa na ganki wani iri?" Mama ta sauke numfashi ta ce "Ina fa lafiya Sadiya." A rude Aunty Sadiya ta ce "Me ya faru?" Mama ta ce "Ku zauna maganar ba ta tsaye ba ce." Sosai Aunty A'isha da Aunty Sadiya suka jimanta al'amarin, zargika kala_kala suka yi akan yar da yaran da akay, Mama ta ce "Sanin gaibu sai Allah." Ɗakin da yaran suke suka shiga suka gan su, Amma Mama ta roƙe su a kan kar su sanar da kowa hatta da Hajiya kuwa. Bayan Neehal ta idar da Sallah ta ɗauko wayarta ta kira Sadik, rejected yay kamar ko da yaushe sannan ya kira ta. Tana d'agawa ta ce "I'm sorry Ya Sadik Please." Sadik ya kwaikwayi yanda take magana ya ce "Um um, ba zan yi sorry'n ba." Neehal ta yi murmushi me sauti jin yanda ya yi ta ce "Haba Yayanah na kaina, idan baka hakura ba kuka fa zan yi." Ta ƙarashe maganar cikin shagwab'a. Sadik ya sauke numfashi ya ce "Shikenan komai ya wuce dear, amma ina kika shiga?" Neehal ta ce "Kaina ke ciwo shi yasa." Cikin tausayawa Sadik ya ce "Subhallah, sannu Allah ya sauqaqe, amma dai kin sha magani ko?" Neehal ta ce "Yanzu dai zan sha." Sun taɓa hira kaɗan suka yi sallama, saboda ta samu ta sha magani ta kwanta ta huta.
Hameedah ce zaune ta ɗora kanta akan cinyar mahaifiyarta tana kuka ƙasa_ƙasa, ganin tabbas ta rasa Ameen tunda gobe zai angonce da wata. Mumy wadda ta gaji da rarrashi tun a gurin bikin ta ce "Wai Hameedah meke damunki ne? so kike har sai mutane sun fuskanci halin da kike ciki, masu dariya su yi miki suna Allah ya ƙara, na ce miki daure zuciyarki za ki yi ki nuna kamar baki damu ba, a yi bikin nan a gama." Hameedah ta d'ago kanta cikin sheshshek'a ta ce "Mumy na yi iya yina nayi ƙoƙarin hakan amma na kasa, wallahi Mumy ba ki ji yanda nake ji a cikin zuciyata ba kamar ana rura mun garwashin wuta." Mumy ta ce "Na san abun da ciwo, kuma nima ina jin yanda kike ji, amma ki daure dai, na faɗa miki ko mai daren daɗe wa sai kin auri Ameen in dai da bokaye a cikin duniyar nan, yanzu dai ki share hawayenki in faɗa miki wani abu kin ji My daughter." Hameedah ta gayd'a mata kai ta fara share hawayen nata.
Misalin ƙarfe 12:30 na dare Ameen ne zaune a falon Daddy shi da Mama da ta kira shi, ya tattara duka hankalinsa yana sauraren abun da zata faɗa masa. Mama ta ce "Dama d'azu kai ka tsayar da Neehal?" Ya ce "Eh." Mama ta ce "Akan wanne dalili?" Ya yi shiru, Mama ta ce "Ka yi shiru ina maka mgn." Ya ce "Babu komai Mama." Mama ta girgiza kai ta ce "To me ne dalilin da yasa ka bata kayan data saka? bayan ga wanda suka ɗinka za su saka ita ƴan'uwanta." Ameen ya ce "Mama wai dama wannan shine kiran da kika mun? wallahi na ɗauka wani babban abunne ya faru." Mama ta harare shi ta ce "Ban sani ba." Shigowar Neehal falon ya hana Ameen faɗar abun da zai faɗa. "Ke kuma daga ina?" Mama ta tambayi Neehal tana kallonta, Neehal ta turo baki gaba ta ce "Bacci zan yi a nan saboda ina son na kwana tare da yaran." Mama ta nuna mata dakin da suke da hannu tana faɗin "Suna nan, zaki wani kwaso jiki a daren nan ki taho kamar da tare da su kike kwana." Neehal ba ta ce komai ba ta shige, Ameen da ya bita da kallo har ta shige dakin sannan ya dubi Mama ya ce "Wanne Yara ne kuke magana akansu." Mama kamar ta share ta ƙi faɗa masa sai kuma dai ta sanar masa, don abokin kuka shi ake fadawa mutuwa. Shima ya girgiza da lamarin, amma dai ya ce wa Mama da safe sai akai yaran gidan Radios da Televisions a bada cikiyarsu ko za a dace a samu iyayensu. Mama ta yi na'am da shawarar shi. Neehal ta daɗe kafin bacci ya ɗauke ta, tana ta aikin kallon yaran, tana jin ƙaunar su na mamaye mata zuciya.