← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 118

Sashe 7

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Misalin ƙarfe tara na dare Hajiya ce zaune a falon sama ita da Ameen, Hajiya sai washe baki take tana zubawa Ameen hira, da alama dai ya cika mata aljihunta da kuɗi, Neehal ce ta fito daga ɗakinta, ganin Ameen ta ɓata fuska tare da turo baki gaba, Hajiya ta bi ta da kallo ta ce "Har Auwar ɗin ya tafi?" Neehal ta gyad'a mata kai kawai, Hajiya ta ƙara faɗin "To kuma mene ki ke ta ɓata rai, kamar za ki kai duka?" Neehal ba ta kula ta ba ta zauna a kasan kujerar da suke. Ameen ya d'ago ya na kallonta a hankali ya ce "Na ga missed call ɗinki tun ɗazu?" Neehal ta ce "Uhm" kawai, ya ce "What Happened?" muryarta na rawa ta ce "Nothing" ƙoƙarin maida kwallar da ta cika mata ido ta yi, wadda batasan dalilin ta ba. Ameen ya maida hankalinshi kan wayarsa bai ƙara cewa komai ba, Neehal ta tashi ta koma ɗakinta.

Ta na shiga ta hango wayarta na haske alamun a na kira, ɗauka ta yi ta duba ta ga Anwar ne, ɗaga wa ta yi ta kara a kunnenta ya yi sallama ta amsa masa ta ƙara da faɗin "Ka je gida lafiya?" Ya ce "Lafiya ƙalau" Ta ce "Nagode fa ya Anwar sosai" Ya ce "Kin san fa ban san yawan godiyar nan, kin kai na miki komai Neehal a rayuwarnan, kuma kin san wani abu?" Neehal ta ce "A'a" Ya ce "Wannan ring d'in kyautar da na ajiye zan miki ce ranar aurenmu, kuma kawai sai na canza shawara na ce bari na kawo miki kawai" Neehal ta ce "Aiko na ji daɗi sosai Ya Anwar ɗina, Allah ya bar k'aunah." Ya ce "Ameen My Queen." Hirarsu suka cigaba da yi cikin nishaɗi, duk da Neehal ba ta wani jin daɗi a ranta kawai daurewa ta ke yi.

Washegari gari Uncle Mahmud k'anin Mama ya zo da sassafe ɗaukar Hajiya za su wuce Gombe, Neehal kafin ta wuce School suka yi Sallama dan lecture din safe gareta. Kwanaki na ta tafiya Rayuwa ta na wucewa, sai gashi har satika huɗu sun shud'e, a wannan week ɗinne kuma su Neehal za su gama exam ɗinsu ta second semester Level two (2), sosai Neehal ta zama silent saboda kusantowar bikinta, Tsakaninta da Ya Ameen kuwa ba ta sauya zani ba, tsakaninta da shi gaisuwa ce kawai sai kuma kyauta da tsarabar da yake yo mata a duk satin duniya idan ya dawo gida weekend bai fasa mata ba, amma kwata_kwata ba ya sakewa da ita, ita kuwa Neehal hakan ba ƙaramin damunta ya ke ba.

Yau Laraba ƙarfe 12 Neehal ta fito daga exam, ta na cikin tafiya ta ji a na kiranta da faɗin *"Fateema Tafeedah*" juyawa ta yi ta ga best freind ɗin ta ce a school ɗin Zee, tsayawa ta yi har Zee ta ƙaraso inda take, Zee ta ce "Fateemah tafiya za ki yi" Neehal ta ce "Ehh" Zee ta ce "Tun yanzu, yau ba shiga Library kenan?" Neehal ta ce "Na gaji ne, bacci ma nake ji, da daddare kawai na yi karatun" Zee ta ce "Ok sai mun yi waya tunda gobe bamu da exam" Neehal ta ce "Ba za ki zo ke da su Meesha ku karb'i Ankonku ba?, gobe fa Aunty Sadiya za ta kawo duka" Zee ta ce "Allah ya kai mu goben, za mu shigo da yamma mu karb'a insha Allah" Suka yi sallama Neehal ta tafi. Ta na zuwa gida ta wuce sama ta shiga ɗakinta ta kwanta ta na tunanin rayuwarsu tun daga k'uruciya, haka kawai ta ji kuka ya kufce mata ta shiga rera shi, sai da ta gaji dan kanta ta yi shiru, dan babu mai rarrashin ta a kusa, Toilet ta shiga ta dauro alwala ta dawo ta zauna kanta na mata wani irin ciwo, ga yunwa dake nuk'urk'usar cikinta dan bata karya ba ta tafi school. Da k'yar ta daure ta yi Sallar sannan ta sakko ƙasa, tea ta haɗa mai kauri tasha, duk da tasha tea d'in amma ba ta dena jin ba daɗi a jikinta ba, haka dai ta daure ta shiga kiciniyar ɗora girki kar Mama ta dawo ta tarar ba ta yi ba. Washegari ta tashi ba ta jin daɗin jikinta ko kaɗan, amma ta ta'allak'a hakan da period ɗinta da ya kusa, dan ta na cin wahala ba kaɗan ba idan za ta yi. Ta na kwance a kan gadonta lullub'e da duvet Mama ta shigo ɗakin, Janye duvet d'in Mama ta yi ta na faɗin "Neehal wanne irin bacci ki ke haka har 10 ta wuce ba ki tashi ba?" Neehal ta buɗe idonta a hankali ta ce "Ba na jin daɗi ne Mama" Mama ta ce "Ayya sorry Daughter, Month ɗinki ya yi ko, ki tashi ki lallaɓa ki yi wanka ki sha ko tea ne, sai kisha magani" Neehal ta ce "Ai bai zo ba,ciwon kawai na ke ji" Mama ta ce "Ki dai tashi ki sha" Neehal ta yunk'ura ta tashi zaune tana taune lips d'inta.

Ƙarfe 12 Aunty Sadiya ta ƙaraso gidan da atamfofi da leshuka da yadin bridal shower na k'awayen amarya, aka zube su a falo. Neehal ta na kwance a kan doguwar kujera ba ta ko motsa ba duk da ta na jin duk budurin zuwan Aunty Sadiyan, sai ma runtse idanunta da ta ƙara yi zuciyarta na bugawa. Aunty Sadiya ta kalli sashen da take ta ce "Neehal lafiya kuwa take bacci da ranar nan?" Mama ta ce "Ba ta jin daɗi ne, ciwon mararta ne ya tashi, amma na bata magani tasha, shine bacci ya ɗauketa" Aunty Sadiya cike da tausayawa ta ce "Ayya Allah ya ba ta lafiya, Amarya ba lafiya ai babu kanta, dan ma insha Allahu ta na yin Aure za ta dena ciwon marar" Mama ta ce "Allah ya sa, kin san ta da shegen shan zak'i kamar me, na hanata na hanata amma ta ƙi denawa" Aunty Sadiya ta ce "Allah ya sauwak'e, bari na kira Haneefah ta zo ta ɗibi na freinds ɗinsu" Mama ta ce "Ya kamata kam, tunda bikin ya matso su kai ɗinkuna, nima bari na ɗibi na mutanena." Su na duba kayan su na cigaba da tattaunawa akan bikin, Mama ta na sanar da Aunty Sadiya Abubuwan da za'ayi, ba wani jan bikin za'ayi ba, Events uku kawai za'ayi, daga Kamu/Mother's day, sai Dinner da Yini, sai bridal shower na k'awayen Amarya. Gabad'aya sun riga da sun yi bucking na events din da za'ayi, duk wata siyayya ta Amarya itama sun kammala ta, yanzu lefe kawai suke jira sai a sanya satittikan bikin. Sai da Haneefah ta zo sannan ta tashi Neehal daga baccin gasken da ya d'auketa, ta tashi zaune ta na taune lips ɗinta, ka na ganinta ka ga mai cuta, Aunty Sadiya da Haneefah suka shiga yi mata sannu. Mama ta kawo mata abinci ta ɗan tsakura ta ci ta ƙara shan magani, ranar dai haka ta wuni ba ta jin daɗi, Anwar da su ka yi waya hankalinshi ya tashi da ya ji ba ta da lafiya, sai da ya zo ya duba ta da daddare hankalinsa ya ɗan kwanta, tun da ya ga jikinta ba rijib take a kwance ba. Washegari, ta tashi jikin nata da sauƙi, dan period d'in nata bai zo ba har yau, yau ma exam d'in safe ce da su, amma ba ta dawo ba gida da wuri ba, saboda sun tsaya ɗaukar pics da friends ɗinta, tunda sun gama exam d'in sai dai fatan samun result mai kyau, suka yi sallama da freinds ɗinta su na faɗin sai sun zo bikinta, ita dai Neehal yaƙe kawai take yi dan zuciyarta babu daɗi ko kaɗan. Ta na dawowa gida Mama ta sanar mata da zuwan wadda za ta mata gyaran jiki daga Maiduguri gobe Insha Allah, Hajiya ma goben za ta zo tunda ran Lahadi za'akawo lefe amma maza ne za su kawo.
Chapter 7 · 0% Book details