Sashe 23
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Neehal ce zaune a office d'inta ta na operating system, sai sauke numfashi take akai_akai alamun wani abu na damunta. Haneefah dake zaune a kujerar da take fuskantar ta tana latsa waya, lokaci zuwa lokaci ta na d'agowa ta na kallon ta. Ajiye wayar ta yi a kan table ɗin gabanta cikin kulawa ta ce "Wai Neehal meke damun ki ne.?" Ba tare da Neehal ta d'ago ba ta ce "Babu komai, me ki ka gani.?" Haneefah ta ce "Yanayinki ya nuna kamar wani abu na damun ki." Neehal ta ce "Babu gaskiya, idan ma da akwai ba zai wuce Rashin jin Ya Sadik ba ne da banyi ba yau." Haneefah ta ce "Kamarya rashin Ya Sadik.?" Neehal ta sauke numfashi ta ce "Tun jiya da yamma da muka yi waya har yanzu bai ƙara kira na ba, gashi last seen ɗinsa a WhatsApp tun 6:44 pm na jiya" Haneefah ta yi wani munafukin murmushi ganin haƙansu ya kusa cimma ruwa ita da Sadik, domin ita ta bashi shawarar ka da ya nunawa Neehal ya na sonta a yanzu, ya bari sai ta shak'u da shi sosai sai ya sanar mata. Ita kuwa Neehal baiwar Allah, maganarta take bil hak'k'i ba tare da tunanin komai ba. "To ki kira shi mana ki ji ko lafiya." Cewar Haneefah cikin nazartar ta. Neehal ta ce "Kuma fa hakane, bari mu koma gida zan kira shi." Haneefah ta ce "To, Allah ya sa lafiya dai." Neehal ta ce "Amin." Bayan sun koma gida da yamma wanka kawai Neehal ta yi ta kira layukan Sadik amma duka ba sa tafiya. Zama ta yi a bakin gado tare da dafe kanta cikin damuwa, can kuma ta ja ɗan ƙaramin tsaki ganin damurwar na neman hana ta sukuni. A fili ta ce "To mene ma na damuwar haka akan shi.?" "Sadik ya cancanci ki damu dashi fiye da haka ma, duba da tarin kyautatawarsa a gare ki, gami da kulawar da yake nuna miki." Wata zuciyar ta ba ta amsa da faɗin haka. Mik'ewa tsaye ta yi zumbur kamar an tsikareta ta na sauke ajiyar zuciya, saboda wani tunani da ya ɗarsu a ranta. Wata doguwar rigar abaya purple color ta ɗakko ta zira a jikinta, turarukanta ta mutstsika ta yane kanta da ɗankwalin abayar, wayoyinta kawai ta kwasa a hannunta ta fice daga d'akin. A falon ƙasa ta tarar da Mama. "Ke ina zaki haka ki ke sauri kamar za ki tashi sama.?" Mama dake kallon Neehal tunda ta fara sakkowa daga kan steps ta fad'i haka." Neehal ta tattaro nutsuwarta ta na ɗan sosa kanta ta ce "Gidan Aunty za ni, kuma sauri nake saboda in yi in dawo da wuri." Cikin mamaki Mama ta ce "Gidan Aisha kuma da wannan sakaliyar yammar? Daga dawowarki daga aiki ko abinci ba ki ci ba.?" Neehal ta yi shiru tare da sunkuyar da kanta ƙasa. Mama ta ce "Me ma za ki yi a gidan A'ishan?" Neehal ta ce "Gaishe ta zan yi, na dad'e ban je ba." Mama ta mata kallon tsaf ta ce "Ki bari gobe kya je." Neehal ta ce "Gobe fa sai six zan dawo daga school." Mama ta ce "To kya je wani time ɗin." Neehal ta marairaice ta ce "Please Mama." Mama ta ce "Ba fa za ki fita ba Neehal a yamman nan, idan Dad ɗinki ya dawo me zan ce masa?" Neehal ta turo baki gaba ta juya za ta koma sama. Mama ta katse ta ta hanyar faɗin. "Ki shiga kitchen ki zubo abinci ki ci." Neehal ta yi hanyar kitchen ba tare da ta ce komai ba, abincin ta ɗebo kaɗan ta koma sama. Ta na shiga ɗakinta ta ajiye shi a kan bedside ta hau gado ta kwanta, sosai ta ji takaicin hana ta zuwa da Mama ta yi har da 'yar k'wallarta, kiran Sallar Magriba ne ya tada ta. Bayan ta idar da Sallah ta ɗakko abincin ta fara ci, sai kuma yanzu take jin haushin kanta na damuwar da ta yi akan kawai yau rana ɗaya dan ba su yi waya da Sadik ba, tambayar kanta ma ta yi inda ta je unguwar su Aunty A'ishan gidansu Sadik ɗin za ta je neman sa ko kuma yaya? Sakin ranta ta yi ta cigaba da sabgarta duk da kewar Sadik ɗin na nuk'urk'usar ranta.
Neehal tsna kitchen ta na yiwa Dad farfesu Mama dake falon a zaune ta na kallon labarai ta shigo kitchen ɗin ta na faɗin. "Neehal kin kusa gamawa.?" Neehal ta ce "Ehh na kusa." Mama ta ce "Kawo in ƙarasa ki je falo Sadik ya zo." Neehal ta juyo da sauri ta na duban Mama cikin fad'uwar gaban da ba ta san dalilin ta ba." Mama ta ƙaraso cikin kitchen, Neehal ta na Ƙoƙarin fita Mama ta ce "Ki zuba masa abinci mana." Neehal ta ce "Toh, hijab zan ɗauko." Jiki a sanyaye ta ƙaraso ta zauna a kujerar kusa da shi bayan ta ajiye masa abinci a gabansa. Kanta a ƙasa ta ce "Ina yini." Sadik da yake ta binta da kallo ya ce "Lafiya k'alau ya aiki." Neehal ta ce "Alhamdulillah." Sadik ya gyara zama cikin kulawa ya ce "Ba ki da lafiya ne na ganki wani iri.?" Neehal ta ce "Lafiya ta k'alau." Sadik ya ce "Uhm, ko ki tambaye ni yau ina shiga.?" Neehal ta ce "Ai zan tambaye ka, dafatan dai Lafiya.?" Sadik ya ce "Lafiya lau, sha'anin aiki ne ya kawo haka." Neehal ta turo baki gaba ba ta ce komai ba. Sadik ya yi murmushi cikin tsokana ya ce "Fushin me ki ke yi to.?" A shagwab'e ta ce "Ni ba fushi nake ba."
"Uhm rigimar autanci ce ta motsa kenan."
Neehal ta yi murmushi saboda yanda yay maganar ya bata dariya. Hirar su suka cigaba da yi cikin nishad'i, wani irin daɗi take ji saboda ganin Sadik, cikin lokaci kaɗan ta ware suka shiga hirarsu. Sadiƙ mutum ne da ya san takan bi da duk wanda yake mu'amala da shi, mutum ne mai tsananin kirki da hak'uri, gashi da sanyi kamar ba barrister ba, sai dai akwai kaifin tunani da saurin fahimtar abu, ga uwa uba nutsuwa da addini. Abun da yake ƙara burge Neehal da shi nasiha da faɗin gaskiya a kodayaushe, ko yaya kuka ɗan zauna da shi sai ya tunatar da kai wani abu na addini da mu'amalar rayuwa. Mama ma yaron ya na burgeta, ta yaba da hankalinsa da nutsuwarsa, shi yasa ba ta hana mu'amalar su da Neehal ba.
Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah, yau gashi bikin Ameen ya matso saura satittika, shirye-shiryen biki ake ba kama ƙafar yaro, ɓangaren gidan amarya da gidan Ango, ba yama kamar gidan su Amarya, dan su yanda suke tsara bikin ma sai anfi sati ana shagali, ango ne yake neman ba su cikas dan shi ya ce bashi da lokacin ɓatawa a yawon zuwa events, amarya dai ta na ta lallab'ashi a kan ya amince amma ya ƙi. Su Mama shirin su suke sosai ita da 'yan'uwanta, Ameen ya saki kuɗi an haɗa lefe na gani na faɗa, Aunty Sadiya da Aunty A'isha ne suka haɗo masa. Ƴan'uwan Dad ma masu murna da auren ba a barsu a baya ba gurin nasu shirin.
Yau Saturday Misalin ƙarfe goma na safe Neehal ta na kwance a kan gadonta ta na bacci ta ji ana tashin ta, a hankali ta buɗe idanunta dake cike da barci ta na karanta addu'ar tashi daga bacci a zuciyarta. Ameerah 'yar gidan Uncle Mahmud ta gani tsaye a kanta, yunk'urawa ta yi ta tashi zaune ta na mutsitstsika ido, Ameerah ta na murmushi ta zauna a bakin gadon ta na faɗin. "Bacci har wannan ranar Yaya Neehal." Cikin murya mai cike da bacci Neehal ta ce "Kin san jiya muka gama exam, baccin da ban yi ba ne kwana 2 saboda karatu nake ramawa, yaushe ku ka zo?." Ameerah ta ce "Yanzun nan, Mama ta ce in shigo in tashe ki." Neehal ta ce "Welcome, ke da Ammi ku ka zo.?" Ameerah ta ce "Ehh, suna falo suna kallon lefe." Neehal ta sauka daga kan gadon ta na faɗin, "Kin san nima har yau ban samu nutsuwar ganin lefen nan ba, saboda exams d'in da muke, gashi har za a kai gobe." Ameerah ta ce "Ai dama exam akwai caza wa mutum kai, Allah dai ya ba da sa'a." Neehal ta amsa da "Amin" tare da shigewa toilet.