Sashe 79
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Washegari ma fitar safe ta yi zuwa gurin aiki, data dawo kamar time ɗin jiya ta shirya ta tafi gidan Aunty A'isha, sai bayan Magriba ta dawo gida. Tana cikin yin Sallar isha'i ta ji wayarta na ringing, bayan ta idar ta yi lazimi ta ɗauko wayar domin ta duba mai kiran nata. Wani kiran ne ya ƙara shigowa, 'Uncle Ahmad' sunan data gani yana yawo akan screen ɗin kenan. Ta d'aga tare karawa wayar a kunne, muryar su Afrah ta ji kowa na rige_rigen kiran sunan ta, "Aunty! Aunty!" Cikin farinciki ta ce "Na'am my kids ya kuke?" Suka haɗa baki gurin faɗin "Lafiya k'alau." Neehal ta ce "Ya school da Islamiyya? Kuna dai karatu sosai ko yaran kirki?" Afrah ta ce "Eh Aunty, exam ma zamu fara next week." Ta ce "Allah ya ba da sa'a Daughter, ina Ummi da Aunty Zahra?" Ta ce "Suna gida." Neehal ta ce "Ki ce ina gaishe su." Amrah ta zo ta karɓe wayar daga hannun Afrah tana faɗin "Aunty ki yi hirar da ni nima, ai kin gama da ita ko?" Neehal ta ce "Toh Daughter ina Daddy?" Amrah ta kalli Ahmad dake zaune yana sauraren hirar da suke, da yake a handsfree ya saka wayar. Ya gyaɗa mata kai, Amrah ta ce "Gashi nan." Ahmad ya ɗauki wayar ya ce musu su je su cigaba da Assignment ɗinsu. Ya kara wayar a kunnensa bai ce komai ba. Neehal ta ce "Ina yini." Ya ce "Bana amsawa." Tun ma kafin ya faɗa mata abun da ta masa ta san laifinta, dan haka ta ce "I'm sorry bazan kuma Uncle, ya ka je gida?" Ya ce "Lafiya k'alau, ya Mama da Daddy?" Ta ce "Suna nan k'alau." Ya ce "Masha Allah." Tare da kwanciya akan gadon da yake kai, murya ƙasa_ƙasa ya ce "Princess ki bani labari mai daɗi mana." Ta ce "Uhm, kasan me Uncle?" Ya ce "A'a." Ta yi shiru, ya ce "Uhm? ina jin ki?" Ta ce "Ka fasa kawo mun su Afrah, ka bar su a gurin Ummi ta cigaba da riƙe su kawai." Ya ce "Why?" Ta ce "Mama ta ce, kun fi mu buƙatar su a kusa da ku." Ta faɗa masa duk yanda suka yi da Maman. Ya yi murmushi ya ce "Allah sarki Mama, ta hango abun da mu ba mu hango ba, kuma ta fi mu gaskiya." Neehal ta ce "Amma idan sun yi hutu zaka na kawo mun su." Ya ce "Insha Allah Princess, kafin kuma mu yi aurenmu su dawo hannunki da zama gaba-ɗaya." Ta yi shiru tana maimaita kalmar Auren daya ambata a cikin ranta, gabanta na fad'uwa. Ya ce "Hello Princess!" Ta sauke numfashi ta ce "Na'am Uncle." Ya ce "Kin yi shiru." Ta ce "Ba komai." Sun ɗan taɓa hira sannan suka yi sallama.....
*SAFEENAH*
Tun ranar da su Afrah suka koma gida anata murnar ganin su yan'uwa da abokan arziki, yayin da a ɓangaren Safeenah kuwa akasin haka ne. Dan wani irin tashin hankali mara misaltuwa ta tsinci kanta a ciki, lokacin ɗaya cikinta ya kaɗa ta tsure sai toilet. Da yake sai a washegarin ranar da su Ahmad suka koma da safe sannan suka samu labarin bayyanar su Afran. Ranar wuni ta yi a ɗaki cikin zullumi da fargaba, lokacin ɗaya ta zabge ta rame ta fita daga cikin hayyacinta. Gashi tana ta kiran wayar ƙawarta Saudart bata shiga wayar a kashe. Ranar da su Afrah suka zo gidan ta ja su ɗaki ta tambaye su cikin bugar ciki, yanda aka ɗauke su. Afrah data fi surutu ta ce mata "Suna falo suna kallo, wasu suka zo fuskokinsu a rufe suka ɗauke su." Tashin hankalin ta ne ya ƙaru, tunda gashi yaran za su iya bayanin yadda aka sace su idan an tambaye su, hakan yasa a washegarin ranar ta yi sammako ta tafi Zariya bayan ta yiwa mahaifiyarta ƙaryar Saudat ɗin ce bata da lafiya zata je duba ta. Tana zuwa Zariya ta ƙara tarar da wani tashin hankalin, domin kuwa kwance a gadon asibiti ta tarar da Saudat cikin mummunan yanayi, bata ma san waye a kanta ba. Ƙanwar Saudat ɗin ce take sanar mata wasu ƴan_daba ne suka mata duka ba tare da an san me ta yi musu ba. Amma ana ta bincike ana ce ƙoƙarin gano ko su waye. Cikin fitar hayyaci Safeenah ta dawo gida da daddare, tana zuwa ta kwanta zazzaɓi rigijib ya rufe ta saboda tsananin tashin hankali. Tana tsoron kar ta yi biyu babu, ita bata samu soyayyar Ahmad da take bala'in son sa ba gashi kuma Ƴaƴansa sun dawo gare sa cikin k'oshin lafiya. Ta yi da na sani da nadama mara amfani data biyewa rud'in shaid'an da zugar ƙawa har ta kaita ta baro ta, yau gashi ta barta a ciki, duk da itama gata can kwance cikin mawuyacin hali, amma ita ta san idan asirinta ya tonu kashe ta za'a yi. Tunda kwangilar kisan kai ta bayar a yi. Ta kira Gaye wanda yasa yaransa suka masa aikin ɗauke su Afrah amma wayar ta shiga bai ɗauka ba. Sai bayan kwana biyu ta ga text ɗinsa ya turo mata, inda yake sanar mata. Shine yasa yaransa suka yiwa Saudat dukan mutuwa, saboda ta yi masa barazanar zata tona masa asiri tunda ya ci amanar su a aikin da suka ba shi. Itama matuƙar ta yi ƙoƙarin aikata gangancin da Saudat ta aikata sai ya mata abun da ya fi wanda ya yiwa Saudat. Ƙarshen tashin hankali da damuwa Safeenah ta shiga da ganin wannan text ɗin, amma ta yiwa Allah godiya da ba'a kashe su Afrah ba, may be in an tashi yi mata hukunci a yi mata da sassauci. Jinya sosai ta kwanta har sai da ta kaita ga kwanciya a gadon asibiti saboda razani.......