Sashe 86
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan Alk'ali ya zauna a mazauninsa aka miƙo masa wani ɗan abun rubutu da pen. Bayan 2 minutes wani mutum ya miƙe ya ɗan rankwafawa ya yi gaisuwa ga Alk'ali sannan ya fara karanto takardar dake hannunsa kamar haka "Zamu saurari shari'a ta gaba akan gisan gillan da wasu mutane suka aikata wa marigayi Alhaji Muhammad Gabasawa tare da mai ɗakinsa, shekara goma sha ɗaya da watanni da suka wuce." Sannan ya koma ya zauna. Neehal ta lumshe idonta bayan ta gama ƙarewa wadanda suka yi kisan kallo, zuciyarta na mata k'una. Barrister Murtala Gaya (Lauyan Alhaji Ali) ya miƙe ya kai gaisuwa ga Alk'ali sannan ya fara magana. "Sunana Barrister Murtala Gaya, Ni ne lauyan masu ƙara, ina roƙon wannan kotu mai adalci da ta yankewa waɗan nan azzaluman mutanen da suka yiwa Alhaji Muhammad Gabasawa da mai ɗakinsa gisan gilla hukunci dai_dai da abun da suka aikata." Ya rank'wafawa ya ce "Na gode ya mai girma mai shari'a." Alk'ali ya ɗan yi rubuce_rubuce sannan ya d'ago ya dubi mutane ya ce "Ko akwai lauyan da yake kare masu ƙara?" Wani Barrister ne ya miƙe cikin girmamawa ya ce "Eh akwai ya mai girma mai shari'a. Sunana Barrister Garba Dan_ladi, nine lauyan dake kare waɗanda ake ƙara." Sannan shi ma ya ɗan rank'wafawa ya ce "Na gode ya mai girma mai shari'a." Sannan ya koma ya zauna. Barrister Murtala Gaya ya miƙe a karo na biyu yana duban Alk'ali ya ce "Ya mai girma mai shari'a ina son zan yi magana da waɗanda ake ƙara." Alk'ali ya ce "Kotu ta baka dama." Ya rank'wafawa ya ce "Na gode ya mai girma mai shari'a." Sannan ya yi fito daga gurin da yake ya ƙarasa inda masu laifin suke ya ɗan kare musu kallo na wasu sakanni sannan ya ce. "Kotu tana son sanin sunayenku da kuma yanda kuka gudanar da kisan kai ga Alhaji Muhammad Gabasawa da iyalinsa, tare kuma da son sanin wanda ya turo ku aikata hakan." Da sauri Barrister Garba ɗan ladi ya miƙe ya ce "Ina da ja ya mai shari'a, bai kamata Barrister Murtala ya dinga tambayar waɗanda ake ƙara wanda ya turo su aikata laifin da sukay ba, saboda ba don haka ake zaman wannan kotun ba." (Da alama dai wanda ya turo a kashe su Abba shine ya ɗauki Barrister Garba.) Barrister Murtala ya tari numfashinsa da faɗin "Dole ne in musu wannan tambayar ya mai girma mai shari'a, saboda waɗanda ake ƙara sun sanar da jami'an tsaro cewar turo su akay, amma sun ƙi faɗar ko waye ne, da alama an musu babban gargadi' ko barazana mai tsoratarwa. Mu kuma muna so mu sani saboda shi ma a nemo shi a duk inda yake a hukunta shi." Alk'ali ya dubi Barrister Garba ya ce "K'orafi bai karbu ba Barrister Garba." Ya mayar da dubansa ga Barrister Murtala ya ce "Barrister Murtala cigaba da tambayarka kotu na sauraren ka." Ya yi murmushi ya ce "Na gode ya mai girma mai shari'a." Sannan ya ƙara maimaita tambayar da ya yi wa waɗanda ake ƙara. Ɗaya daga cikinsu ya ce "Sunana Hakim ilyasu." Sai babban nasu shi ma ya ce "Sunana Bilyaminu saminu." Na ƙarshen kuma ya ce "Sunana Zakari Mu'azu." Barrister Murtala ya jinjina kai ya ce "Kotu tana sauraren ku, Malam Zakari da Bilyaminu da Hakim." Wanda ya fara faɗar sunansa wato Hakim ya ce "Watarana muna zaune da yamma ni da abokina Zakari......ya nuna Bilyaminu sannan ya cigaba da magana. Bilyaminu ya zo ya same mu a kan yana so zamu yi wani aiki tare da shi, ya tabbatar mana da za mu samu kuɗi mai tarin yawa a wannan aikin, cikin zumud'i muka ce masa za mu yi ko wanne irin aiki ne. Da farko da ya sanar mana aikin kisan kai ne mun tsorata, muka ce gaskiya baza mu iya ba, domin ba mu taɓa aikata hakan ba, iyakacinmu k'wace da haurawa gidan mutane, ko kuma raka irin su Bilyaminu fashi da makami. Amma Bilyaminu ya nuna mana ruwan kuɗi ya ce, mutumin da zamu yiwa aiki hamshaqin mai kuɗi ne, zai ninka mana kuɗin da muka gani a gurin Bilyaminu sau goma. Nan fa muka ruɗe mun ji zamu kuɗi, muka je mun amince amma fa muna tsoron kar a samu matsala. Bilyaminu ya ce babu matsalar da za'a samu, koma da an samu wanda ya samu aikin zai tsaya mana dan Babba ne a ƙasar nan, dan haka mu kwantar da hankulanmu babu abun da zai faru. Da jin wannan batu sai muka amince." Hakim ya ɗan numfasa, Barrister Murtala ya ce "Dama already kum san shi Bilyaminun ne kuna da alaƙa dashi?" Hakim ya ce "Ehh, babba ne shi a daba kuma kamar oga yake a gurin mu." Barrister Murtala ya jinjina kai ya ce "Cigaba kotu na saurarenka ka sanar mata yanda kuka gudanar da kisan." Hakim ya cigaba da magana. "Tun a ranar Bilyaminu ya fara ba mu kuɗaɗe masu kauri, ya ce sauran kuma sai aiki ya kammala zai ba mu. Muka amince cike da k'warin gwiwa da murnar za mu samu kuɗaɗe. Bayan kwana biyu da daddare Bilyaminu ya zo ya ɗauke mu a wata Mota shida wasu mutane guda biyu, gaba-ɗayansu fuskokinsu a rufe da baƙin k'yalle. Wani ɗan gida ya kai mu ya ba mu wasu kaya bak'ak'e muka saka a jikinmu tare da baƙin k'yallen muma muka ɗaure fuskokinmu. Sannan ya bamu bindigu muka zira a aljihun wandunanmu. Bayan dare ya tsala muka fita a wannan Motar zuwa gidan mutumin da muka kashe, ta bayan gidan Bilyaminu ya yi parking motar muka fito ya buɗe ƙofar dake bayan gidan muka shige, shi ya yi mana jagora har cikin ɗakin baccinsu. Dama Bilyaminu ya sanar mana za su yi magana da mutanen, idan sun amince da buƙatarsa wadda ba mu san ta mene ba kar mu yi musu komai, idan kuma mun ji sun yi gardama mu sakar musu harbi. Bayan ya gama rad'a musu maganar da zai faɗa musu muka ji mai gidan cikin ƙaraji yana cewa ba zai taɓa amincewa da buƙatar su ba, da ido Bilyaminu yay mana inkiya. Babu jira ni da Zakari muka sakar musu bullet bibbiyu a ƙirjinsu, Bilyaminu ya ƙara musu ɗai_ɗai. Sauran mutum biyun da su zo ɗaukar mu tare da Bilyaminu waɗanda ba mu san su ba, su ba su yi harbin ba. Suna dai tsaye riƙe da bindigu a hannunsu. Mu ukun nan mu kai kisan." Ya yi shiru yana jan numfashi. Neehal ta runtse idanta hawaye mai zafi na zuba daga cikinsu. Aunty A'isha ma runtse idanunta tay tana tuno sanda ta ji ƙarar harbin a cikin kunnenta. Hajiya kuwa tsinuwar Allah take ja musu a cikin zuciyarta. Barrister Murtala ya jinjina kai cikin k'warewar aiki ya dubi Zakari ya ce "Ka ji duk abun da ɗan'uwanka ya faɗa, gaskiya ne?" Zakari ya ce "Eh haka ne." Barrister Murtala ya mayar da dubansa ga Bilyaminu wanda ko cikin duhu mutum yay gamo da shi zai tabbatar da rikak'k'en ɗan ta'adda ne. Saboda zubinsa da yanke yake muzurai da ido da kuma tabo_tabon yanka dake jikinsa. Ya ce "Malam Bilyaminu ka ji duk abun da Hakim ya faɗa haka ne?" Cikin shakak'k'iyar murya ya ce "Eh Haka ne." Barrister ya jinjina kai ya ce "Kotu tana san sanin wanda ya turo ku ku kay wannan ɗanyen aikin da kuma sanin ina sauran mutum biyun da ku kay aikin tare?" Bilyaminu ya ce "Sauran mutum biyun da mukay aiki tare ɗaya ya shek'a barzahu a cikinsu, ɗayan kuma yana kurkuku a halin yanzu sakamakon wani kisan da yay aka kama su, an yanke masa hukuncin d'aurin rai da rai. Batun wanda ya samu wannan aikin kuma wani babban mutum ne kuma sananne a ƙasar nan. Shi ya bani address ɗin gidan da za mu yi kisan, har yanda tsarin gidan yake da hanyoyin da zamu bi har zuwa ɗakin baccinsu, kuma shi ya ba ni mukullin da na yi amfani da shi na buɗe ƙofar gidan ta baya. Ban san dalilin da yasa ya ce mu je mu kashe mutumin da matarsa ba, ya dai faɗa mun kawai idan na je na nuna musu hotonsa, na ce masa za su amince da buƙatar da yake da ita a kan ƴarsu ko a'a? Idan sun je za su amince kar mu yi musu komai, idan kuma sun ƙi amince mu kai su k'iyama, dan za su iya tona masa asiri. A halin yanzu mutumin ba ya numfashi a doron ƙasa ya mutu shi ma. Kuma na riga na yi masa alƙawari bisa wani sharad'i namu na sirri ba zan taɓa faɗar sunansa ba a cikin wannan aikin ko me za'a mun kuwa." Barrister Murtala ya jinjina kai cikin gamsuwa ya ce "Ko zaka iya faɗawa kotu alaƙar dake tsananinka da mutumin da ya saka ku aikin." Ya ce "Eh, alaƙa ce kawai irin ta mai kuɗi da ƴan hark'alla irin mu, idan suna buƙatar aiki irin wannan su saka mu su biya mu da ƴan silalla." Barrister Murtala ya juyo ya kalli Alk'ali ya ce "Ya mai girma mai shari'a, ina son wannan kotu ta bani dama in gayyato wani bawan Allah wanda yake da masaniyar komai akan wanda yasa su Bilyaminu kashe su Alhaji Muhammad Gabasawa da matarsa. Tunda shi Bilyaminu ya ƙi faɗa" Alk'ali ya ɗan yi rubuce-rubuce ya d'ago ya ce "Kotu ta baka dama Barrister Murtala." Ya rank'wafawa ya ce "Na gode ya mai girma mai shari'a." Sannan ya ce "Ina son gayyato *Hashim Isma'il na_kowa* ." Alk'ali ya dubi mutane ya ce "Kotu na san ganin Hashim Isma'il na_kowa a gabanta." Alhaji Ali ya maimaita sunan a cikin zuciyarsa "Hashim Isma'il na_kowa?" Mamaki bai gama kashe shi ba sai da wani magidancin mutum da aƙalla zai yi shekaru arba'in a duniya ya fito gaban kotu, domin kuwa ɗan amininsa ne Alhaji Isma'il na_kowa, tsohon sanatan Kano ta tsakiya, kuma mutumin da yake matuƙar son Alhaji Muhammad Gabasawa. Aunty A'isha ma mamakin ne ya kusa kashewa domin ta san mutumin a gurin Abban Neehal, mutuminsa ne sosai. Ba iya Aunty A'isha da Alhaji Ali kawai ambatar sunan Isma'il na kowa ya bawa mamaki ba, mafi yawan mutanen gurin sun