← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 118

Sashe 73

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Washegari Sunday tana gida through out saboda ita kaɗai ce ranar hutunta a week, tunda ta fara siwes Monday to Saturday take zuwa gurin aiki. Tunda ta tashi da safe bata huta ba tana ta aikin gida. Mama sun fita gidan wata Freind ɗinta ita da su Dije tun wajen 11, daga nan kuma za su wuce kasuwa su siyo kayan girki. Suma su Hameedah tun safe suka wuce Abuja, saboda gobe Monday Hameedan zata je gurin aiki. Bayan Sallar la'asar tana kitchen tana girki ta ji ƙarar doorbeil. Ta fito tana kwab'e fuska saboda gajiyar da ta yi, a tunaninta su Mama ne suka dawo, amma tana buɗe ƙofar sai ta ga wanda bata taɓa tsammanin ganin sa a wannan lokacin ba. Cikin matuƙar mamaki ta tsaya tana kallonsa. Ya sakar mata murmushinsa wanda ya kasa bacewa idanunta tun ranar da ya tafi har kawo yau. Ta yi ƙasa da kanta tare da faɗin "Sannu da zuwa." Ta ƙarashe zancen tana matsawa baya dan ta ba shi hanya. Ya ce "Yawwa Aunty." Tare da shigowa cikin falon bakinsa ɗauke da Sallama. Ta koma kitchen zuciyarta cike fal da mamakin zuwansa. Plate ta ɗauko ta ɗora masa drinks akai ta dawo falon, ya bita da kallo still fuskarta d'auke da murmushi. Ta ajiye plate ɗin a gabansa ba tare da ta ce komai ba. Ya ce "Mama bata nan ne?" Ta ce "Eh, ta je unguwa, amma na san yanzu tana hanyar dawowa, ina su Afrah?" Ya ce "Suna gida, ba su ma san zan zo ba dan kar su mun rigima." Neehal ta ce "Ai da ka zo mun da su, ya su Ummi?" Ya ce "Suna nan k'alau." Ta mik'e tare da faɗin "Ga ruwa ka sha, bari na ƙarasa girki." Ya ce "Okay thank you." Tare bin ta da kallo har ta shige kitchen ɗin, ya lumshe idonsa yana jin k'aunarta na ƙara mamaye dukkan wani gurbi dake cikin zuciyarsa. Ba jimawa da shigar ta kitchen ɗin ya ji shigowar su Mama falon ita da su Dije tare da wasu ma'aikatan gidan maza guda biyu hannunsu ɗauke da manya_manyan ledodi. Mama ta ƙaraso cikin falon da mamaki take duban Ahmad, cikin fara'a ta ce. "Doctor! Kai ne a gidan namu?" Cikin girmamawa ya ce "Nine Mama, sannu da zuwa." Mama tana ƙoƙarin zama ta ce "Yawwa, sannunka kai ma." Ya sauko daga kan kujerar da yake ya ce "Ina yini." Mama ta ce "Lafiya k'alau, ina ƴan tagwayena da su Ummi?" Ahmad ya ce "Suna nan k'alau." Mama ta ce "Masha Allah, ina Neehal ɗin ne ta bar ka kai kaɗai a zaune." Yana sosa kai ya ce "Ai babu komai Mama.,'" Mama ta miƙe ta nufi kitchen jin k'amshin girki ta gane Neehal ɗin tana can. "Oyoyo, Sannunku da zuwa." Neehal ta faɗa lokacin da Mama ta shiga kitchen ɗin. Mama ta ce "Yawwa, Sannunki da aiki." Ta shagwab'e fuska ta ce "Yawwa Mama, yau na sha aiki na gaji, jikina har ya fara mun ciwo." Mama ta ce "Allah ya baki lada kin ji ƴar albarka." Neehal ta ce "Ameen." Mama ta ce "Ki je gurin Doctor, bari na ƙarasa girkin. Babu daɗi a bar mutum shi kaɗai a zaune." Neehal ta ce "Na ma gama girkin, saukewa kawai zan yi, da kitchen ɗin zan gyara." Mama ta ce "Barshi, idan su Zulai sun huta sai su zo su gyara, ki zuba abincin ki kai masa." Neehal ta ce "Toh." Mama ta juya ta fita, ita kuma ta shiga zuba masa abincin kamar yadda Mama ta umarce ta. Sai da ta hau sama ta sako hijabi tare da ɗauko wayarta sannan ta dawo downstairs ɗin.

Yana zaune yana latsa waya ta yi Sallama ta ajiye masa abincin a gabansa, ganin bai sha drinks ɗin data ajiye masa ba. Ta ce "Ya baka sha ruwan ba." Ya d'ago yana kallon fuskarta da murmushinsa na gado ya ce "Zan sha yanzu." Ba ta ce komai ba ta buɗe ruwan ta tsiyaya masa a cikin glass cup ta miƙa masa. Ya karɓa tare da faɗin "Thank you." Neehal ta koma kujerar gefensa ta zauna ta shiga wasa da yatsun hannunta. Bayan ya gama shan ruwa ya fuskance ta a hankali ya ce "Gurinki na zo Neehal." Ta dube shi da sauri amma bata yi magana ba. Ya gyaɗa mata kai alamar tabbatarwa. Ya miƙe tsam daga kujerar da yake ya koma wadda take zaune ya zauna a gefenta. Ta lumshe ido da sauri saboda shaƙar sassayan k'amshinsa da ta yi. Muryar Ahmad da ta ji yana magana yasa ta buɗe idanunta. Wayar hannunsa yake miƙo mata, ta karɓa da alamar tambaya akan fuskarta. Hoton da ta gani akan screen ɗin wayar yasa ta waro Idanunta waje cikin tsananin mamaki. Hotonta ne tana ƙarama wanda bata san a inda ya same shi ba. Kafin ta yi magana ya riga ta da faɗin "Ki wuce ki ga na gaba." Ba tare da ta yi magana ba ta wuce kamar yadda ya ce zuciyarta cike da al'ajabi, Wannan karon ɗan zabura ta yi tana ƙara kallon hoton, hotonta ne ita da shi, tana murmushi shi kuma yana kallon fuskarta da murmushi ɗauke akan fuskarsa...........✍️
[7/21, 9:31 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*

_By_
_Zeey Kumurya_

*4️⃣3️⃣*

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*
Chapter 73 · 0% Book details