← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 118

Sashe 54

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Wajen ƙarfe goma na safe sai ga Uncle Umar a asibitin, Uncle Usman ya je ya shigo da shi. Tun kafin su shigo ɗakin ya fara masifa, Uncle Usman dai bai tanka masa ba. Har lokacin Neehal bacci take abunta. Uncle Usman ya zauna yana yi wa Uncle Umar wani kallo ya ce "Wallahi Ya Umar ka matuƙar ba ni mamaki ka kuma ba ni kunya da har kake kallo ana azabtar da Neehal amma baza ka hana ba sai ma tayawa da ka yi. To idan ka manta bari in tuna maka, mahaifin yarinyar nan shi ya fito da mu daga cikin duhun rayuwa zuwa mai haske, cinmu, shanmu, suturarmu, iliminmu, bai taɓa nuna gazawar sa ba ko a fuska balle a aikace, alhalin kuma mu ba dolensa ba ne kyautatawa ce kawai irin tasa. Mutumin da yay maka duk waɗannan  abubuwan sannan ya ɗora da samar maka aiki ya baka muhallin zama, hidimar bikinka rabi da kwata shi ya yi ta, dan ba ya raye ɗiyarsa guda ɗaya tak a duniya ta cancanci azabtarwa daga gare ka? A tunani na ko wani ka ga yana mata haka sai inda ƙarfin ka ya ƙare a ɗaukar mata mataki." Uncle Umar ya yi shiru kawai yana kallon Uncle Usman amma ya rasa bakin magana. Uncle Usman ya Tab'e baki ya ce "Abu na ƙarshe daga rana irin ta yau Neehal ta bar hannunka da zama, zata koma inda ake sonta da k'aunarta saboda Allah, tun da dama kai dan dukiyarta ka karb'i riqon ta, to ka riƙe dukiyar amma ita dai baza ta ƙara kwana a gidanka ba." Cikin fusata Uncle Umar ya ce "Ni kake faɗa wa waɗan nan maganganun Usman? Uban wa ya faɗa maka dan dukiyarta na karb'i riqon ta, wato an zugo ka zaka mun rashin kunya ko?" Uncle Usman ya yi murmushi ya ce "Calm down bro, abun duk bai kai haka ba, karɓe Neehal daga hannunka ba ya nufin za a karɓe dukiyarta daga hannunka ba ne, za'a bar maka kacigaba da juya ta domin wadda zata ɗauki Neehal bata buƙatar dukiyarta dan a gurinta ba komai ba ce." Uncle Umar ya mike tsaye ya ce "Wai me kake nufi da nine Usman eye? Wato kana so ka ce son cinye dukiyar Neehal nake son yi ko? To wallahi babu inda zata a hannuna zata cigaba da zama har auranta." Uncle Usman ya ce "Hmmm sai ku ji daɗin kashe ta kenan kai da matarka da duka ko? Yaya Umar, Yaya Fateemah bata cancanci haka daga gare ka ba, ka ji tsoron Allah ka tuna kai ma zaka mutu kuma kai ma ka haifi ƴaƴan nan. Yarinyar nan mai ta sani a rayuwa me ta tsare muku da kuka mayar da ita baiwa a gidanku, kuma wallahi bana ganin lefin Fauziyya sosai na fi ganin naka dan da ka tsawatar mata ba ta isa ta yi wa Neehal haka ba, amma babu komai rayuwa ce Duk *abin da mutum ya shuka shi zai girba* ." Uncle Umar cikin borin kunya ya ja tsaki ya fice daga ɗakin. Sai wajen 12 Neehal ta tashi daga baccin, bayan ta wanke baki Uncle Usman ya bata abincin da ya siyo mata ta ci sannan ta sha maganinta. Wayar Aunty A'isha ya kira ya haɗa su, Neehal ta dinga murna jin Muryar Aunty'nta, ta dinga tambayarta ina Maman Abuja. Bayan sun gama wayar ya kira Ummi ya haɗa su itama. Da kansa ya je har gidan Uncle Umar ya tattaro duk wani abu na Neehal ya haɗa a trolley ɗinta ya baro su daga gidan. Aunty Fauziyya ta tab'e baki ta ce "Umma ta gai da Ashsha, ala raka taki gona." A yammacin ranar aka sallame su daga asibitin tun da Neehal ɗin ta warware sosai, sai dai zata cigaba da shan magungunanta. Gidansu Haleemah suka je ya kai mata kayayyakin da ta ba shi tare da yi mata godiya sannan suka wuce Gabasawa. Ummi ta yi kuka sosai ganin yanda Neehal ta lalace ga shatin duka b'aro_b'aro ajikinta. Kwanan su ɗaya suka wuce Gombe, nan ma Su Aunty A'isha sun sha kuka da ganin yanda Neehal ta koma. Hajiya ta dinga ja wa su Aunty Fauziyya alkaba'i. Lokacin da Neehal ta koma Gombe Mama ba sa garin ta je Saudiyya Umara daga nan ta wuce London, sai daf da bikin Aunty Sadiya ta dawo. Lokacin Neehal ta fara dawo wa hayyacinta saboda kulawar da take samu a gurin Aunty A'isha da Hajiya, har an saka ta a makaranta boko da islamiyya. Mama ta yi murna sosai da ta ga Neehal ta dawo gurin Aunty A'isha da zama. Bayan bikin Aunty Sadiya Neehal ta mak'ale wa Mama ta bita Abuja, wannan zuwan shine sanadiyyar komawarta hannun Mama gaba-d'aya da zama. Dama zuwa Kano siyayya da su Aunty A'isha suka yi ta haɗu da wani Alhaji da Allah ya yi wa matarsa rasuwa shekarar da ta wuce, shima bai taɓa haihuwa ba ya ce yana son ta kuma baya son a ja bikinsu da nisa tun da su ba yara ba ne. Cikin wata biyu bayan fahimtar juna da sukai da kuma duk wani binkicen da ya kamata aka ɗaura Auran Aunty A'isha da mutumin ta tare a nan Kano. Neehal tana jin daɗin zama a gurin Mama sosai dan babu abun da suka rage ta da shi na jin daɗin rayuwa ita da Daddy. Makaranta mai tsada Daddy ya saka ta. Cikin lokaci kaɗan Neehal ta koma Neehal ɗinta ta ainihi mai rawar kai da surutun tsiya, hakan ya sa ba sa shiri ko kaɗan da Ameen, a duk lokacin da ya zo gida to ba ta da sukuni ta dinga kumbure_kumbure a ɗaki tare da Allah Allah ya yi ya tafi. Tun Neehal tana tunawa da Ahmad a ranta har ta fara mantawa shi.
Chapter 54 · 0% Book details