Sashe 102
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
A falo Neehal ta zauna bayan ta fito, ba ta koma bedroom ba. Tana zaune a nan Ameen ya fito daga ɗakin. Ta kalli agogon dake falon ta ga goma na safe ta wuce, ta ce masa "Yaya me za'a girka for lunch?" Ya zauna a kujerar dake fuskantar ta, ya ce. "Tun yanzu?" Ta ce "12 za ni gurin aiki ne, shi yasa." Ya ce "Ki dafa ko me kike so." Ta ce "Ka faɗa dai, kar in dafa abin da baka ci, ko kuma wanda Aunty Hafsah bata ci." Ya ce "Ita ai bata iya cin abinci, for me kuma ko me kika dafa i will eat." Ta ce "Ko tuwo ne?" Ya harare ta. Ta tashi tana dariya ta sauka ƙasa, ya bi ta da kallo. A falon ƙasa ta samu ƴan'mata guda biyu masu aikin gidan, ta shiga kitchen ba tare data musu magana ba. Kamar yadda ta tsokani Ameen tuwon ta ɗaura, duk da itama bata wani ci sosai amma kawai sai ta ji shi take son yi. Tuwon semo ta yi, miyar zogale tare da taimakon ƴan'mata nan, wanda bayan shigowar ta kitchen ba jimawa suka biyo ta wai za su taya ta aikin, ta ce musu to bismillah. Suna aikin suna mata hira, dan surutu ne da su ba kaɗan ba, farkon hirar kyawunta suka fara yabawa, har suna cewa sun kasa gano waya fi kyau tsakanin ita da Ameen. Yanda suke acting a hirar sai suke bata nishad'i, ta dinga murmushi, wani abun kuwa idan sukay dole sai ta dara, because they are so commedians. Sai ta ji daɗi a ranta ta samu masu ɗebe mata kewa a gidan, kuma ga su yara ne ba za su wuce 18 years ba. Ta tambaye su sunayensu suka sanar mata, Harira da Saude. Ba ta gama girkin ba sai kusan 12, saboda da ɗan yawa ta yi saboda ta san za'a iya yin baƙi ƴan zuwa dubiya, ta kwasawa Ameen nasa daban a cikin ƙaramar warmer, ta ce wa su Saude idan ya zo neman abincinsa gashi nan. Ta ɗibi kaɗan ta ci saboda saurin da take yi ta tafi gurin aiki dan ta yi late, bayan ta gama ci ta hau sama ta shirya cikin sauri ta fito ta shiga ɗakin Hafsah ta sanar mata zata tafi, kamar an mata dole ta ce ta je driver ya kai ta. Direban gidan ne ya kai ta gurin aiki kamar yadda Hafsan ta faɗa, ba ta ga Ameen ba kuma bata ga Motarsa a parking space ba, hakan ya tabbatar mata da baya gidan kenan.
Ƙarfe Shida na yamma ta tashi daga aiki, tun kafin ta fito daga office aka aiko an zo ɗaukarta. Bayan ta fito ta ga direban gidan Ameen ne, dama da ya kawo ta ya tambaye ta ƙarfe nawa zata ta tashi ta sanar masa. Bayan ta koma gidan ta shige ɗaki bata fito ba har akay Magriba, saboda baƙin da ta ga an yi. Tana zaune akan sallaya suna chat da Sadik aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, ta d'ago tana dubansa tare da amsa masa sallmar da ya yi. Ta ajiye wayar ta ce "Sannu da zuwa Yaya." Bai amsa mata ba ya zauna a kusa da ita. Ta ɗan lumshe ido ta buɗe saboda k'amshinsa da ya cika mata hanci. Ta yi ƙasa da kanta saboda yanda ta ga yana kallon ta, lokuta da dama tana mamakin yanda yake yawan kallon ta, ta kan tambayi kanta ko kallon na mene ne? Ganin ba shi da niyyar magana ta ce "Mun yi waya da Mama ta ce, idan tana free za su zo anjima ita da Daddy." Ya ce "Allah ya kai mu." Sai kuma ya ɓata fuska ya ce "Dama zuwa kika yi dan kina bari na da yunwa?" Ta masa kallon mamaki ta ce "Yunwa kuma Yaya?" Ya ce "Eh." Ta yi murmushi dan gano bakin zaren, ta ce. "Amma dai ka ci wani abun?" Ya girgiza mata kai, ta ɓata fuska cikin rashin jin daɗi ta ce, "Da ka ci tuwon Yaya ko kaɗan ne, ya yi daɗi fa, nima na ci, amma shine ka zauna da yunwa." Ya ce "Ai baki so in ci ba dama." Ta ce "To yanzu bari in tashi in dafa maka wani abun ka ci, me kake so in dafa maka Yayana?" Ya ce "No ki huta I know you are tied." Ta ce "Zan iya fa Yaya, ai na huta." Ya ce "No ki bar shi, mu je dai ki raka ni unguwa." Ta ce "Toh Yaya."