← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 118

Sashe 32

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari da safe Neehal tana tattare ɗaki Yarinya ɗaya ta tashi tana kiran sunan Daddy, Neehal ta ajiye tsintsiyar hannunta ta ƙarasa gadon ta d'ago ta tana faɗin "Kin tashi, mu je ki yi fitsari to." Yarinyar dake bin ta da kallo ta gyaɗa mata kai. Bayan ta yi fitsarin Neehal ta wanke mata baki da fuska suka fito, suna fitowa ta ga itama ɗayar ta tashi zaune tana ta mutsitsika ido, Neehal ta kama ta itama ta kaita toilet, Bayan sun fito ta kalle su ta ce "What is your name?" Wadda tafi surutu ta ce "Afrah, amma Daddy yana ce mun Princess, a lesson da islamiyya kuma *FATIMA AHMAD*." Neehal ta jinjina kai ta ce "Nice name Darling." Sannan ta juya ta kalli Ɗayar ta ce "Ke fa." Yarinyar ta ce "Amrah, amma Daddy yana ce mun Jewel a lesson da islamiyya kuma *AISHA AHMAD*." Neehal ta Jinjina kai tana murmushi ta ce "Nice name sweetheart." Afrah ta ce "Aunty safiyar ta yi zaki kai mu gurin Daddy ko?" Neehal ta gyaɗa mata kai zuciyarta cike da k'aunar yaran. Mama ce ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da tea flaks da ƙananun cups, yaran suka bita da kallo kafin su haɗa baki a tare su ce "Ina kwana." Mama ta ajiye kayan hannunta tare da amsa musu, ta ƙaraso ta shafa kansu da cike da kaunarsu, dan yaran sun matuƙar burge ta ba kaɗan ba, musamman da suka gaishe ta, ga dukkan alamu daga gidan tarbiyya suke. Mama ta dubi Neehal ta ce "Ɗauko musu kayansu a saka musu, bari na haɗa musu breakfast su yi." Neehal ta amsa mata tare da ficewa daga ɗakin, yaran suka bita da kallo kamar za su bita. Bayan sun yi breakfast Neehal ta musu wanka ta shirya su cikin rigunansu na jiya. Kasancewar yau ne d'aurin Aure yasa gidan ya ƙara cika da baƙi mata da maza, duk inda Neehal ta ɗora k'afarta su Afrah na biye da ita a baya, duk wanda ya tambaye ta yaran waye sai ta ce na wata Friend ɗinta ne. Ɗaya daga cikin sojojin gidan ta bawa kuɗi ya siyo wa musu kayan sakawa da takalma da panties, kafin Azhar ya kawo mata ta shirya su tsaf suka yi kyau sosai. kowa so yake ya ɗauke su ko ya musu hoto, amma yaran sun ƙi yarda da kowa sai Neehal, saboda ganin taron jama'a, ita kuwa ta cika su da kayan zaƙi dangin su chocolate da sweet suna ta sha. Mama kanta ya ɗau caji tana da hidima da mutane, hakan ya sa ba ta bi takan zancen yaran ba, dama kuma da taywa Daddy maganar su ya ce a bari bayan biki sai a san abun yi. Ƙarfe biyu na rana aka ɗaura Auren AL'AMIN MUHAMMAD TAFIDA da amaryarsa HAFSAT AHMAD ƊAN GASKE. Anan babban masallacin Juma'a dake cikin Narasawa G.R.A. Yau ma Neehal ta yi kyau sosai, shadda ta saka da safe Wadda aka mata akai mai kyawun gaske, ta kafa ɗaurinta. Su Afrah sai faɗin "Kin yi kyau Aunty." suke, Murmushi Neehal take idan suka faɗi haka. Ta ce musu "Thank you Dear." Wajen ƙarfe uku Sadik ya ƙaraso gidan. Neehal ta fito tare da twins ɗinta, tunda ta fito ya ƙura mata ganin irin kyawun da ta yi. Neehal ta gaishe shi ya amsa yana kallon yaran, Neehal ta ce "Ya su Maamah da Abba?"  Sadik ya ce "Suna Lafiya, Ya taro?" Neehal ta ce "Alhamdulillah." Ya ce "Allah ya sanya Alkhairi ya ba su zaman lafiya, saura naki kuma." Neehal ta yi murmushi ta ce "Yau har na gaji da jin wannan furucin, kowa muka haɗu sai ya ce sai mun zo naki kuma." Sadik ya ce "To ai gaskiya ne, gwara Mama ta aurar dake ta huta da rigimarki." Neehal ta ce "hmmm." Kawai, Sadik yace "Wannan cute babies ɗin fa?" Neehal ta ce "Yaran wata Friend ɗina ne." Sadik ya ce "Masha Allah, Allah ya raya su." Neehal ta ce "Ameen." Tare da dubansu ta ce "Ba ku gaida Uncle ba." Amrah ce ta fara gaishe shi da faɗin "Ina kwana." Sannan itama Afrah ta gaishe shi, ya kama hannunsu tare da amsa musu. Bai wani jima ba ya tafi saboda Ameerah data zo kiran Neehal. Suna tafiya Ameerah ta ce "Amma Yaa Neehal wannan saurayinki ne?" Neehal ta girgiza kai tare da faɗin "Ko ɗaya, he is just my Friend." Ameerah ta yi shiru amma ba dan ta yarda ba. Ƙarfe huɗu aka tafi gurin da za ai Mother's Day, sai bayan magriba aka tashi. Yau kam amarya ba ta zo ba, tana gida suna nasu suma, shima Ameen ɗin bai je ba, hakan yasa yau kwata_kwata ba su haɗu da Neehal ba. Twins kam ganin hada_hadar mutane yasa ba su ƙara takurawa Neehal akan ta kai su gurin Daddy'nsu ba, sai da suka zo bacci nema suka so yi mata rigima ta lallaɓawa su da faɗin sai an gama biki zata kai su. Washegari ma anyi taro a gida inda akai kidan ƙwarya manyan mata suka cashe, tun kafin Azhar aka fara har bayan la'asar ana yi. Yau za a miƙa Amarya gidan angonta, misalin ƙarfe biyar na yamma Neehal dake jin duk jikinta a sanyaye ba tare da tasan dalili ba ta bar wa Haneefah twins ta nufi part ɗin Ameen............✍️
[7/21, 9:01 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*

_By_
_Zeey Kumurya_

*2️⃣1️⃣*

A hankali ta buɗe ƙofar falonsa ta shiga bakinta ɗauke da Sallama, kanta na ƙasa ba ta yarda ta d'ago ba saboda falon cike yake da abokanansa. Suka amsa mata suna binta da kallo, Salman ganin yanda ta takure a tsaye ya dube ta ya ce "Shiga mana Neehal, yana ciki ai." Neehal ta ce "Toh." Tare da gaishe su a lokaci ɗaya, ba ta jira amsarsu ba ta wuce. Wani a cikinsu da ya bita da kallo ya ce "Salman, wannan kamar ƴar jaridar nan ta ASTV?" Salman ya ce ba kama ba ce ita ce." Ya ce "Wow yarinyar me kyau tana burge ni wlh." Kafin ya ce wani abu ya ji wani a cikinsu yana faɗin "Ita ce wadda suka zo tare da Al'ameen ranar dinner ai, dama ƙanwarsa ce?" Salman ya ce "Yeah." Wanda ya fara magana da farko ya ce "To ai ni ranar na ɗauka ita ce ma Amaryar saboda ta yi kyau sosai har ma tafi Amarya....." Haka dai sukaita magana akan Neehal.

A hankali take knocking ƙofar bedroom ɗinsa kamar me tsaron wani abu, Ameen dake shiryawa a gaban mudubi don bai jima da fitowa daga wanka ba ya ɗan yamutsa fuska ya ce "Waye?" Neehal tay shiru yanayin da take jin jikinta da zuciyarta na ƙara tsananta, Ameen ya taho ya buɗe ƙofar zuciyarsa cike da masifa, a tunaninsa a cikin abokansa ne wani ya zo zai ƙara masa ciwon kai akan wanda suka sa masa d'azu. Cike da mamaki yake kallonta, kanta na ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, ya koma ciki yana faɗin "Come in." Neehal ta shiga kamar munafuka ta zauna a gefen gado, yana fesa turare ya ce "What happened?" Ganin ta ƙi cewa komai tunda ta shigo. A hankali ta d'ago ta kalle shi amma yanda ba za su haɗa ido ba ta ce "Yaya..." Sai kuma ta yi shiru hawaye ya fara zuba daga idonta, Ameen ya sauke numfashi sannan ya dawo kusa da ita ya zauna ya kama hannunta murya ƙasa_ƙasa ya ce "Tell me what happened?" Neehal ta share hawayenta ba ta ce komai ba, Ameen ya ƙura mata ido domin yasan dalilin kukan nata a hankali ya ce "Kin fara missing Yayanki ne?" Ta d'aga masa kai da sauri sannan ta ce "Shikenan Yaya na dena ganin ka every weekend?" Ameen ya girgiza mata kai tare da faɗin "Wa ya faɗa miki? Zan dinga zuwa kodayaushe mana."  ta ce "Na san baza ka zo ba tunda ka yi aure." Ameen ya ce "Dolena ma inzo inga my Mum da little sis ɗina." Neehal ta ce "Dagaske?" Ya d'ago kanta ya saka idanunsa a cikin nata yana mata wani kallo ya gyaɗa mata kai, Neehal ta lumshe idanta da sauri gabanta na fad'uwa. Ameen ya sakar mata fuska yana sauke numfashi, tashi ya yi ya ɗauko wayarsa ya shiga gallery ya miƙa mata, ta karb'a tana dubawa. Waro idanta ta yi tana murmushi t ce "Wow Yaya pics ɗin sun yi kyau sosai." Ya yi murmushi kawai yana kallonta, ita kuma ta cigaba da kallon hotunan. Pictures ɗinsu ne wanda aka musu ranar dinner ita da shi, wani suna zaune wani kuma a tsaye lokacin da ta je yi musu lik'i, sosai hotunan sukai kyau, kuma babu ta yanda za'ai ka gani ka ce ba ita ce amaryar ba. Ta ajiye masa wayar bayan ta gama gani tare da mik'ewa ta ce "Yaya Bari in koma." Ameen ya mata wani kallo ya ce "Ba za ki raka ni gidan Amaryata ba?" ta waro Ido ta ce "Ni kuma Yaya? ga Freinds ɗinka nan." Ya kau da zancen da faɗin "Ina new kids ɗinki?" Neehal ta ce "Suwa?" Ya ce "Twins." Neehal ta ce "Oh, suna gurin Haneefah." Ya ce "Me yasa ba ki zo mun da su ba?" Ta ce "Na ga baka son hayaniya ne kar su dame ka." Ameen ya ce "Ok, me kike so in baki a ɗakin nan?" Neehal ta hau juya ido a ɗakin  ganin babu abun da zata buƙata a ɗakin, ta ce "Nothing." Ya ce "Sure?" Ta gyaɗa masa kai, sai kuma ta kalli kan mudubi ta ɗan shagwab'e fuska ta ce "Na tuno, your perfumes." Ya ce "Ai na maza ne kawai." Ta turo baki gaba ta ce "Ai ba ajikina zan dinga sawa ba, kawai zan dinga jin k'amshin ina tunawa da kai ne." Yay murmushi ya buɗe wata jaka ya ɗauko mata turaruka kala uku ya bata, Neehal ta karb'a da murnarta ta ce "Thank you so much."
Chapter 32 · 0% Book details