Sashe 110
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin dawowarsa Mama ta sakko ta zauna akan kujera sannan cikin kulawa ta ce. "Neehal ta faɗa maka za mu yi magana ko Doctor?" Cikin fad'uwar gaban da bai san ko ta mecece ba ya ce "Eh Mama." Mama ta danne tausayinsa dake cikin ranta ta fara yi masa bayani, cikin tausasan kalamai ta yanda zai fuskanta. Da farko ji yay kansa ya masa wani irin juyawa, yawun bakinsa ya kafe kaf, dak'yar ya iya had'iye wani abu mai ɗaci da ciwo daya tsaya masa a mak'oshi ya ce. "Babu komai Mama, na fahimce ki, Allah kuma yasa hakan shi ya fi Alkhairi a gare mu gaba-ɗaya." Ya yi maganar cikin tsananin dauriyar zafin da zuciyarsa take masa. Bai kuma fuskantar abun da Mama take kuma faɗa masa ba, ya dai ji kamar haquri take ba shi da kuma ƴar nasiha. Ya gyaɗa mata kai kawai, ita kuma ta tashi ta nufi upstairs tana faɗin bari ta turo masa Neehal ɗin su yi Sallama. A karon farko bayan barin Mama falon ya d'ago kansa tare da lumshe idonsa yana fatan ya kasance mafarki yake ba gaske ba ne abin da Mama ta sanar masa. Ya yi hasashen wai hakan na nufin ya rabu da Princess ɗinsa kenan har abada, nan da wani ɗan lokaci za'ai mata aure da wani ba shi ba. "Innalillahi,wa'inna'ilaihirraji'un!" ya shiga maimaita a fili cikin sanyin murya mai cike da damuwa, har ya ji ya fara ɗan samun salama a cikin ransa. Neehal wadda da ƙyar Mama ta yaƙo ta, ta fito saboda ta ce bata san da idon da zata kalle shi ba, ta ƙaraso falon idanunta na shatatar hawaye, da ƙyar take iya ganin gabanta. Ya ƙura mata ido cikin sarewa da karayar zuci, karon farko a rayuwarta ta faɗa jikinsa tare da fashewa da kuka. Ya runtse ido ya buɗe saboda yanda kukan nata yake taɓa masa zuciya. Ya tsotsi lips ɗinsa da suka bushe lokaci ɗaya saboda damuwa cikin marainiyar murya ya ce. "Please Princess Stop crying, ko so kike nima in yi kukan?" Ta girgiza masa kai. Ya d'ago kanta da hannunsa ɗaya, ɗayan kuma ya shiga share mata hawaye da shi. Ta bar jikinsa tana sakin ajiyar zuciya. Cikin muryar kuka ta ce, "I'm so sorry Uncle, I..." Ya katse ta da faɗin. "Me kikai mun Princess da zaki bani haquri? Na fuskanci bayanin Mama kuma na gamsu. Ba mu muke da ikon tsarawa kanmu rayuwa ba, Allah ne yake tsara mana. Ni musulmi ne, kuma dole na yarda da ƙaddara mai kyau da mara kyau, tabbas rasa ki a cikin rayuwata ba ƙaramin rashi ba ne, amma kuma babu yanda zamu yi da ikon Allah. Karki damu akan wannan Please Princess, Na san kina so na sosai, kuma hakan ma abin alfahari ne a gare ni ." Ta kalli fuskarsa yay mata murmushin da ya fi kuka ciwo tare da kamo hannunta ya ce. "Princess! Sau da yawa abun da zuk'atansu suke so ba shine Alkhairi a gare mu ba, sai mu ga wanda ba ma so ɗin ya fi zama Alkhairi a gare mu. Duk da na san kina son guy ɗin da zaki aura ba wai auren dole za'ai miki ba. Amma ko kaɗan ban ji a raina kin yaudare ni ba ko something like this, abun da kikai shine dai-dai, kuma shine adalci. Tunda shi guy ɗin ya riga ni zuwa gurin ki da maganar aure, abun da baza ka so ai maka ba kaima karka so kaiwa wani, dan haka ki daina damun kanki indai ni Ahmad ne na haqura, dama rayuwa cike take da farinciki da baƙinciki, idan ka yi haquri kuma zaka ga ribarsa a gaba, kuma komai zai wuce kamar bai faru ba." Ya yi shiru yana sauke numfashi, dan shi kansa ya san ba ƙaramin dauriya yake ba wajen ɓoye mata damuwarsa. Ta ƙura masa ido cikin mamakin kalamansa zuciyarta cike da tsantsar tausayinsa, ta san daurewa kawai yake dan ya ga ta damu kar ta tashi hankalinta. A hankali ta ce "Thank you so much Uncle, da kulawar ka da duk wani abu da ka mun a rayuwata." Ya yi irin murmushin d'azu ya ce. "Nima na gode da k'aunar da kika nuna mun Princes, Na gode, Na gode sosai, da k'aunar kike wa ƴaƴana. Allah ya yiwa rayuwarki albarka, ya baku zaman lafiya ke da mijinki idan kun yi aure, ya kuma baku zuri'a d'ayyiba." Ta ce "Amin Uncle tare da kai." Ya ja karan hancinta ya ce, "Zan wuce sai mun zo biki." Dan ba ƙaramin dauriya yake ba, so yake kawai ya kadaice ya rarrashi zuciyarsa. Ta lumshe ido hawaye ya zirnano daga cikin idanun nata. Kamar zai yi kuka ya ce. "Oh My God Princess, dan Allah ki bar kukan nan, baki san yadda nake jin zafi a cikin raina ba idan kina yi. Ta share hawayen bayan ta zare hannunta daga cikin nasa ta ce. "Na daina Insha Allah Uncle." Ya ce "ki mun alƙawari ko na tafi baza ki yi kuka ba." Ta ja hanci a hankali ta ce. "Ba zan yi ba Uncle Insha Allah." Ya shafi kuncinta ya ce, "Good lady, yanzu fa kin girma Princess, ko kina so twins ɗinki su gan ki kina kuka?" Ta girgiza masa kai. Ya ƙara kamo hannunta ɗaya ya ce. "Tashi mu je ki raka ni." Ta kalle shi sannan ta tashi ganin shi ma ya miƙe. Ya taune lip ɗinsa jin kamar zai faɗi tare da dafa hannun kujera yana ambaton sunan Allah. Ta ƙura masa ido kawai cikin damuwa. Ya d'ago yana murmushi ya ce, "Wannan kallon fa?" Ta ƙara waro masa manyan kyawawan idanunta haɗe da juya masa su sannan ta lumshe su a hankali. Salon nata ya shige sa ba kaɗan ba, bai san sanda ya dafa kafaɗunta ba ya yi kissed saman idanun, a hankali kuma ba tare da ta taɓa zato ba ta ji saukar lips ɗinsa akan nata. Ta sauke wani gwauron numfashi lokacin da ta ji yana kissing ɗinta, kafin a hankali ya janye fuskarsa daga tata. Cikin raunin murya ya ce, "Good bye Princess, I love You.!" Sannan kamar wanda aka tsikara ya juya da sauri ya fice daga falon. Sai buɗe idanunta ta yi ta ga babu shi sai k'amshinsa da ya bar mata a jikinta da falon. Ta ja ƙafafuwanta da sukay mata nauyi ta ƙarasa kujerar dake kusa da ita, ta faɗa kanta ta fashe da kuka, a ranta tana faɗin. 'This means daga yanzu mun rabu da Uncle, rabuwa ta har abada.' Ta ci gaba da kukan ta a gurin, ta ma manta da alƙawarin da ta ɗaukar masa na baza ta kuma yin kuka ba, akan rabuwar ta da shi.
Da ƙyar Ahmad ya iya jan ƙafarsa ya je parking space, yana zuwa ya buɗe Motar da ya zo da ita ya shiga ya zauna ya ɗora kansa akan sitiyarin Motar, yana jin zuciyarsa tamkar zata soye saboda zafin da take masa. Ganin abun yake tamkar almara, domin bai taɓa tunanin zai ƙara rasa Neehal a karo na biyu ba. Amma ya yarda da ƙaddara, ya kuma yarda wani ba ya taɓa auran matar wani. Zai dage da addu'a akan Allah ya cire masa sonta ko da ba duka ba daga cikin ransa, ya kuma ba shi mace ta gari wadda zata kula da shi da marayun ƴaƴansa. Sai dai ya rasa me yasa wani b'arin na zuciyarsa yake tabbatar masa da bai rasa Neehal ba, yake nuna masa kamar zai mallake ta a gaba. Ya sauke numfashi tare da addu'ar idan rabonsa ce ita, Allah ya ba shi, zai je ya dage da addu'a. Sunan Allah yay ta maimaita a ransa, har ya ɗan samu nutsuwa. Cikin dauriya ya kunna Motar ya fice daga gidan bayan an buɗe masa gate ya nufi gidan Mamy. Yanda Mamy ta ganshi ya shigo a sanyaye kamar mai cuta ta san da matsala, a ɗan rikece ta tambaye shi me nene? Kamar zai ɓoye mata sai kuma ya sanar mata. Itama Mamy ta ji ba daɗi a ranta sosai, domin ta yi wa Ahmad sha'awar Neehal, dan ta yaba da hankalinta da nutsuwarta. Amma sai ta kwantar masa da hankali, ta ce ya je ya dage da addu'a Allah ya zaɓa masa abin da ya fi Alkhairi.
Har bayan Magriba Neehal bata daina kuka ba, Mama ta yi rarrashin ta yi nasihar ta yi faɗan amma ta ƙi barin kukan, har ta gaji ta ƙyale ta. Tana jin wayarta nata vibrate ana ta kiran ta amma ta ƙi bi ta kanta. Ga kanta dake ciwo saboda kukan da take. Bayan Magriban ne Ameen ya zo gidan, lokacin tana ɗakinta a kwance akan gado. Bayan sun gaisa da Mama ya tambaye ta Neehal ɗin, ta sanar masa tana ɗaki tana kuka, ko abinci bata ci ba tun safe. Bai tambaye ta dalilin kukan ba ya tashi ya shiga ɗakin. Ya zauna a gefen gadon ya kira sunanta, ta tashi zaune da ƙyar tana goge hawayen fuskarta, idanunta sun yi jajur. Cikin sanyin murya mai nuni da rarrashi yay mata Ƴar nasiha, akan kuka ba maganin damuwa ba ne, komai yake damun ka, ka kaiwa Allah kukan ka, shi zai maka magani. Sai gashi ta yi shiru, ya ce ta je ta wanke fuskarta ta zo ta ci abinci. Ba ta musa ba, ta tashi ta yi abin da ya ce. Mama ta cika da mamakin ganin cikin mintuna ƙalilan ta saki ranta, Alhalin ita tun yamma take fama da ita. Sai da ta ci abincin ta sha maganin ciwon kai sannan Ameen ya bar gidan.