Sashe 8
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da daddare Neehal ta na kwance a ɗakin Mama, sai juyi take akan gado saboda murd'awar da cikinta yake mata, hawaye ne kawai yake fita daga idanunta, wani amai ne ya taho mata ta tashi da gudu ta nufi toilet ta shiga kelayashi, ta na yin aman ta na jin fitar jinin a jikinta, Ta na sassauke Numfashin azaba ta gyara jikinta ta sanya pad, kuskure bakinta ta yi ta janyo ƙafarta da ta fara riƙe mata ta dawo ɗaki ta kwanta. Mama ta shigo ɗakin ta dube ta cikin tausayawa ta ce "Sannu Daughter ya jikin?" Neehal ta ɗaga mata kai kawai, Mama ta ce "Allah ya ƙara sauƙi" Sosai Mama take tausayin Neehal lokacin period ɗinta, saboda azaba take sha ba ta wasa ba, ciwon mara, baya, k'ugu duk take yi, ƙafafunta duka su riƙe, yau ko gurin aiki ba ta je ba, sai Haneefah ce ta je ta maye gurbinta. Time ɗin da Dad ya zo dubata bacci ya ɗauke ta. Washegari dai da ta tashi jikin nata da sauƙi sai dai ba ta warware tas ba. Da safe ta na cin Irish da soyayyen kwai ɗin da Mama ta kawo mata ta tilasta mata ta sha Ameen ya shigo ɗakin, jin kamashin turarensa ya sa ta d'ago kanta da sauri ta na kallonsa, gabanta ne ta ji ya fad'i ba ta san dalili ba, satar kallonsa ta shiga yi ta ga ya canza sosai ba kamar kwanaki ba, ramar da ya yi duk babu ita sai ma wani fresh da haske daya ƙara, lumshe idonta ta yi a hankali ta ce "Ina kwana?" Kamar bai ji ba sai kuma can ya ce "Lafiya, ya jikin?" Ba ta yi mamakin sanin ba ta da lafiya da ya yi ba, domin kowa na gidan ya san time ɗin period ɗinta saboda azabar da take sha a lokacin yin period ɗin nata. Cikin raunin murya ta ce "Da sauƙi" Juyawa ya yi ya fita ganin Mama batanan, a falon ƙasa su ka haɗu da Mama ta dawo daga part din Dad, Mama ta na dubanshi ta ce "Welcome, har ka zo kenan?" Ya ce "Ehh, ina kwana?" Mama ta ce "Lafiya ƙalau, ya aiki" Ya ce "Alhamdulillah, ya naku?" Mama ta ce "Lafiya ƙalau" Zai nufi part d'in Dad Mama ta ce "Idan ka dawo ina son ganinka" Ya ce "Toh." Misalin ƙarfe goma na safe Aunty Sadiya da Aunty A'isha da yarinyar gurinta Maryam su ka zo gidan, domin yin snacks na karɓar kayan lefe, Neehal dai ta na shan Magani ta kwanta bacci ya ɗauketa dan jiya ba ta samu wani baccin kirki ba, saboda ciwo. Yauma ba ta samu damar zuwa gurin aiki ba, Hajiya da yamma ta ƙaraso gidan da tulin kayanta dan sai bayan biki za ta tafi, wadda za ta yi wa Neehal gyaran jiki Mama ta kira ta, ta ce ta bari sai Monday tun da Neehal ɗin ba ta jin daɗi. Bayan sallar isha'i bayan su Mama sun gama aiki ta samu Ameen a ɗakinsa, Ameen ya tattara duka hankalinshi akan Mama jin ta ce za su yi Magana. Mama tana dubanshi ta ce "Gobe za ka koma Lagos ko jibi?" Ya ce "Gobe da safe" da mamaki Mama ta ce "Da safe kuma?" Ya ce "Ehh" Ta ce gobe fa za'akawo lefen Neehal kuma sai da yamma, kuma maza ne za su kawo" Ya ce "Am sorry Mum, amma ba zan samu damar tsayawa ba, dan akwai wani important thing da zan yi" Mama ta ce "Sunday ce fa, saboda gudun haka fa ya sa aka sa weekend, kar wani uzurin ya tsaida wani" ya yi shiru bai ce komai ba, Mama ta mik'e ta ce "Dole ne koma uzurin mene da kai ka jira a karb'i kayan da kai, ka ji na faɗa maka" Ta na faɗin haka ta fice daga ɗakin, Ameen ya bita da kallo.
Washegari Sunday Ranar kawo kayan lefe, tun safe su Mama su kai packaging kayan snacks d'in da soyayyen naman kaza gami da lemuka, yamma kawai suke jira masu kawo kayan su zo. Neehal yau ta lallaɓa ta shirya ta tafi gurin aiki, duk da Mama ta so hanata amma ta ce mata ta ji sauƙi za ta iya zuwa. Mama na kitchen Ameen ya shigo ya same ta da shirinsa na tafiya. Mama ta masa wani kallo bayan ta amsa sallamar da ya yi, Ya ce "Ina kwana Mum" Mama ta ce "Lafiya k'alau" Ya ce "Am sorry Mum zan wuce Lagos yanzu, nima ba son raina ba ne uzurin da zan yi a can mai ƙarfi ne" Mama ta ce "Uhm, uzurin har na fi umarnina kenan a gurinka?" Ya ce "A'a Mum, kar ki ce haka Please" Mama ta yi shiru kawai ta na kallonsa, Ya ce "Am sorry" Mama ta ce "Na yi sorry ɗin ka je Allah ya kiyaye, amma ka sani ko kananan ko ba kanan ba za'a fasa komai ba, idan ma ka ga dama karka halacci taron bikin" ya yi murmushi kawai ya ƙaraso kusa da ita ya yi hugging d'inta tare da faɗin "Thank you Mum, Allah ya sa su zo lafiya su tafi lafiya bye" Mama ba ta ce komai ba, ya sake ta ya fice. Mama ta bishi da kallo, abinda ya sa ta barshi ya tafi tasan uzurin da yake faɗa ba ƙarami ba ne, dan Ameen ba ya taɓa mata musu a kan duk wani abun da za ta sa shi ya yi, komai wuyarsa kuwa.
Ƙarfe 12 na rana Mama su na zaune a falo ita da Hajiya da uncle Mahmud da ya zo shima dan karÉ“ar lefen É—in, wayar ta shiga ringing, É—auka ta yi ta duba ta ga Ammin Anwar ce ke kiranta, murmushi ta yi ta d'aga wayar ta kara a kunnenta tare da yin sallama, ba tare da Ammi ta amsa sallamar da Mama ta mata ba, cikin tsananin ruÉ—u da matsanancin tashin hankali ta ce..........âœï¸
[7/21, 9:00 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
_By_
_Zeey Kumurya_
0ï¸âƒ£6ï¸âƒ£
Doctor an..an...an ka..kashe An...Anwarrrr!' ta fad'i maganar a rarrabe saboda tsananin tashin hankali. Suman zaune Mama ta yi zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu, Ammi ba ta jira amsar Mama ba ta katse wayar. Ita kuwa Mama wayar ma sakin ta ta yi ta fad'i ƙasa. Ganin yanda Mama ta k'ame kamar gunki ga kuma wayarta da ta saka ta faɗi ya sa Hajiya a ruɗe ta ce "Ke lafiyar ki kuwa, kika zuba mana na mujiya ga waya kin saki ta fad'i ƙasa?" Uncle Mahmud da ya fuskanci da akwai wata matsalar ya taso ya dawo kusa da Mama, ganin yanda ta sandare sai ya ɗan girgiza ta, wani nannauyen numfashi ta ja ta sauke, saitin zuciyarta ta dafe da hannunta jin yanda ta ke bugawa tamkar za ta yi tsalle ta fito daga k'irjinta, sai a sannan wani uban gumi ya fara tsatstsafo mata ta ko wanne k'ofofin gashi na jikinta, duk da sanyin Ac'n dake falon. Kallo ɗaya za ka yiwa Mama a wannan lokacin ka hango zallar tashin hankali da ɗimuwar da take ciki, gabad'aya ta rasa a duniyar da take jinin jikinta ya tsaya, ƙwaƙwalwarta ta cak da aiki. Ganin yanayin Mama Uncle Mahmud ya ƙara tabbatar da ba k'alau ba, a ɗan ruɗe ya ce "Doctor lafiya kuwa, me ke faruwa ne?" Mama ba ta bashi amsa ba, numfarfashi kawai take saukewa. A ruɗe Hajiya ta ce "Na shiga uku Ni Zainaba, Fatima ki faɗa mana me ya faru mana, yanayin da ki ka koma Lokaci ɗaya ya tada mana hankali" Mama ta runtse idanunta ta ce "Anwar ya rasu!" A gigice Hajiya ta mik'e tsaye ba tare da ta shirya wa hakan ba, ta ce "Innalillahi_wa'inna'ilaihirraji'un, wanne Anwar d'in?, kar dai ki ce mun na Neehal" Uncle Mahmud innalillahi kawai ya shiga maimaitawa a fili domin mutuwar ta bige shi ba kaɗan ba, Hajiya ta saka kuka ta na salati ta ce "Allah ya ji ƙanka Anwar yaron kirki, mai biyayya, Allah ya sa aljannah ta zamo makoma a gareka, Ni Zainabu yaya Neehal za ta ji mutuwar nan?" Daidai nan Dad ya shigo falon a firgice, ganin yanayin su ya tabbatar masa da su ma sun ji mutuwar.
Mama ta shafe wasu mintuna a zaune a gurin, abu biyu ne yake ƙara dugunzuma mata hankali a kan mutuwar Anwar, na farko cewa da Ammi ta yi an kashe shi, na biyu kuma halin da Neehal za ta shiga idan wannan mummunan labarin ya riske ta. Hajiya kuwa ban da kuka babu abin da take, Dad ma kallo ɗaya mutum zai masa ya gane ya na cikin tsananin tashin hankalin mutuwar Anwar ɗin, musamman idan ya tuna halin da daughter d'insa za ta shiga idan ta ji mutuwar, Uncle Mahmud ne ma mai dauriyar cikin su, amma babu ƙarya wannan ahali mutuwar Anwar ya dake su ba kaɗan ba. Da k'yar Mama ta yi ƙarfin halin kiran Aunty Sadiya da Aunty A'isha ta sanar musu, su ma sun shiga tashin hankali da jin mutuwar Anwar d'in ba kaɗan ba, Ameen kuwa ta yi ta neman Number'nsa amma ba ta shiga, kuma duka layikansa ta yi ta gwadawa amma sun ƙi tafiya, dole sai haƙura ta yi ta ajiye wayar ta fara tunanin hanyar da za ta sanar da Neehal.