← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 118

Sashe 61

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka rayuwa tay ta tafiya, Neehal ta daina d'aga kiran Sadik kwata_kwata, shi kuma ba ya gajiya kullum sai ya kira ta ba a daɗi gami da yi mata daɗaɗan text, na kalaman soyayya addu'a da fatan Alkhairi. Duk text ɗin da ya turo sai ta karanta amma fa bata reply, kuma ba ta yi block ɗinsa ba, saboda babu block ɗin mutane a tsarin rayuwarta, in dai ba abun da bai dace ba mutum yake turo mata ba. Mama ta je Gombe ta yi kwana uku ta dawo, gidan Aunty A'isha su Neehal suka koma kafin Mama ta dawo, su Zulai da Dije kuma garinsu suka je. Da tana gidan Aunty A'isha sai ga Sadik ya zo, Allah ya so tana ɗaki ba falo ba. Ashe ya saba zuwa gidan yana gaishe da Aunty A'ishan ita ba ma ta sani ba. Da Aunty A'isha ta ce a kira ta, sai ta ƙi fitowa ta ce ace bacci take yi. Duk wannan abun da Neehal take dauriya kawai take yi a ƙoƙarinta na ganin ta cire Sadik daga cikin rayuwarta, sai dai zuciyarta ta ce sam bata san wannan batun ba, dan da tunanin sa take kwana take tashi. A kwanakin nan da ta yi babu Sadik ta tabbatar wa da kanta tana son Sadik, so ba na wasa ba ma kuwa, Amma ta yi alƙawari ko son nasa zai kashe ta ba zata taɓa bari su yi soyayya ba. Ameen kuwa tun ranar da ya zo ɗin nan bata ƙara sa shi a idanta ba, tunda ya koma aiki sai weekend yake gari, weekend ɗinma idan ya zo gidan ita tana gurin aiki, bare ma ta ji Mama ta ce sau ɗaya ya ƙara zuwa tun ranar. Sai dai ita Hafsah ta zo sau biyu ta wuni, bata nuna wa Neehal komai ba saboda ganin idon Mama, ita ma Neehal ɗin haka, sai dai ba sa shigewa juna sosai. Dan Munafurci Hafsah harda cewa Mama wai Neehal bata zuwa gidanta, kamar so take ta je ɗin, Mama ta ce bata da lokaci ne shi yasa ga aiki ga school. Kamar yadda Mama ta kai su Afrah Islamiyya haka ta kai su makarantar boko, wadda haɗe take da islamiyya itama, Monday to wednesday sai 5:00pm ake tashin su, Thursday and Friday kuma 12:00 pm.

Yau Talata wanda ya kama azumi saura kwana shida ga mai rabon gani. Da yamma bayan Neehal ta dawo daga school tana ɗaki tana gugar Uniform ɗin su Afrah Haneefah ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da Sallama. Neehal ta d'ago tana dubanta ta amsa mata sallamar, "Amarya ke ce a gari yau? inji maƙi baƙo." Haneefah ta ce "Ni ce nan, na zo mu yi wata magana ne, da zan bari sai gobe sai kuma kawai na ce bari in zo tunda babu abun da nake yi yanzun." Neehal ta ce"Gwara da kika zo ai, Ya Mommy?" Haneefah ta ce "Tana nan k'alau." Suka ɗan taɓa hira kafin Neehal ta ƙarasa gugar sannan ta koma bakin gado kusa da Haneefah ta ce "Wacce maganar zamu yi Besty?" Haneefah ta ce "Akan Sadik ne." Neehal ta ɓata fuska ta ce "Me ya faru?" Haneefah ta ce "Yanayin da kika koma yanzu shi ya tabbatar mun da kin san koma menene." Neehal ta ce "Ban san komai ba ni." Haneefah ta ce "Anyway dai, Jiya Sadik ya zo gida ya same ni and he told me duk yanda kuka yi, wanda kin fini sani ba sai na ƙara maimaita miki ba, amma Neehal na tambaye ki mana." Neehal ta ce "Ina jin ki." Haneefah ta ce "Me yasa kika yi ignoring ɗinsa? Ko kin manta Sadik ɗin ne?" Neehal ta ɗan tab'e baki ta ce "Saboda bana buƙatar shi a cikin rayuwata." Haneefah ta yi ɗan murmushi ta ce "Bakin ki dai ya furta haka, amma fuskarki da yanayinki sun tona asirin zuciyarki. Neehal kina son Sadik! Kuma kema kin sani." Neehal ta yi shiru saboda ba ta san me zata ce ba, sai ma k'walla data cika mata ido. Haneefah ta cigaba da magana "Ina lura dake a kwanakin nan walwalarki ta ragu sosai, kuma na san duk akan haka ne. Amma Sadik yana da wani aibu ne da ba za ki iya soyayya da shi ba? Ko kuma yana da wani halin ne mara kyau da kika fuskanta wanda mu ba mu sani ba?" Neehal ta girgiza kai cikin karaya ta ce "Ko ɗaya." Haneefah ta ce "To me yasa ba za ki yi accepting ɗinsa a cikin rayuwarki ba? Wallahi Neehal baki ga yanda Sadik ya koma ba, gaba-ɗaya ba ya cikin nutsuwarsa, kuma duk saboda ke ne." Haneefah ta sassauta murya ta ce "Please Neehal dan Allah ki amincewa Sadik ku yi soyayya, ki tausaya masa ke ma kuma ki bawa zuciyarki abun da take so, kar ki cutar da ku dukanku." Neehal tana hawaye ta ce "I can't, ba zan iya ba Haneefah, na san ina son Sadik amma ba za mu yi soyayya ba, bana son na kuma yiwa iyayen kowa asarar ɗansu. Haneefah na rufe babin soyayya a rayuwata, ba zan ƙara soyayya da kowa ba!" Cike da tausayawa Haneefah ta ce "Kar ki yi haka Neehal, na sha faɗa miki ki daina faɗar irin wannan maganar, ke a karan kanki kina faɗar haka idan wani ya ji ya samu abun ɗorarwa fa?" Neehal ta ce "An yi na farko an yi na biyu, idan aka yi na uku Haneefah dole hankalin mutane zai dawo kan al'amarin, ko na faɗa ko ban faɗa ba, dole za a fara faɗar maganganu a kai na, ko so kike duk inda na yi a dinga nuna yi ana gata can, duk wanda zata aura sai ya mutu, sai....." Haneefah ta rufe mata baki ta ce "Insha Allahu haka ba zata faru ba, in Allah ya yarda za a yi auranku da Sadik lafiya babu abun da zai faru. Ke dai ki miƙawa Allah al'amuranki, sannan ki dage da addu'a. Su ya Ammar ma kwanansu ne ya ƙare a duniya, amma ba wai dan ke aka kashe su ba." Neehal zata yi magana Haneefah ta katse ta da faɗin "Dan Allah Neehal kar ki ɗauko abun da baki da tabbas akai ki saka a ranki Please!" Neehal ta sauke numfashi ba ta ce komai ba, sai kallon ƙawartata kawai take tana hawayen tausayin kanta. Haneefah ta baibaye Neehal da kalamai masu kwantar da hankali gami da wa'azin da ya ratsa mata zuciyata. Ta nuna mata babu wani mahaluƙi da ya isa ya maka abun da Allah bai maka ba. Neehal ta ji zuciyarta ta yi mata sanyi, kuma ta ji zata karb'i Sadik a matsayin masoyi a karo na uku a rayuwarta. Sai dai wani ɓangaren na zuciyarta cike yake fal da tsoro da fargabar rashin sanin abun da zai biyu baya a soyayyar tasu. Za su yi Aure da Sadik ɗin ne kamar yadda Haneefah ta faɗa ko kuma shima za'a kashe mata shi ne?..........✍️
[7/21, 9:04 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*

_By_
_Zeey Kumurya_

*3️⃣7️⃣*

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*

Sai da Haneefah ta tabbatar da bayananta sun shiga Neehal kuma sun ratsa ta sosai sannan ta miƙe dan tafiya gida  tana faɗin "Mu je in yiwa Mama Sallama na ga magriba ta taho." Neehal ta shagwaɓe fuska ta ce "Ki bari ki yi sallah mana." Haneefah ta ce "Tafiya zan yi, zan je in yi girkin dare." Neehal ta ce "Please dear!" Haneefah ta ce "Ikon Allah, to ki adana shagwab'arki idan yaya Sadik ya zo sai ki yi masa, amma bani zaki wa ba." Ta ƙarashe zancen da dariyar tsokana. Neehal ta ɓata fuska ta ce "Na ji ɗin zan masa." Suka fita daga ɗakin Haneefah tana ta tsokanarta. A ɗakin Mama suka tarar da twins suna cire uniform. Haneefah ta ce "Ashe kun dawo yanzu nake shirin tambayar su." Mama ta ce "Yanzu nan aka ɗauko su." Twins suka gaishe da Haneefah ta amsa, Afrah ta cewa Neehal "Aunty zamu biki." Neehal ta harare ta ta ce "Sarakan son yawo, to ba fita zan yi ba." Amrah ta kalli Haneefah ta ce "To Aunty ke zamu biki." Haneefah ta yi murmushi ta ce "Shikenan, ku saka kaya sai mu tafi." Suka shiga tsallen murna, Mama ta ce "Babu inda za su Assignment za su yi." Lokaci ɗaya Suka ɓaɓɓata fuska kamar za su yi kuka. Neehal ta ce "Don't cry My babies, gobe zan kai ku unguwa." Sai suka saki ransu suka ci-gaba da sabgarsu. Haneefah ta dubi Mama ta ce "Mama zan wuce, sai da safe." Mama ta ce "Allah ya kai mu, ki gai da gida da Mominki, Insha Allah kafin tafiyarmu Saudiyya zan zo gidan naku." Neehal ta marairaice ta ce "Wai Mama baza ki tafi da ni ba?" Mama ta ce "In na tafi dake Neehal mu bar yaran nan a ina? Kuma ga makarantarki ma, ki bari Lokacin Hajji idan Allah ya kai mu sai ki je indai kun yi hutun school." Haneefah ta ce "ki ƙyale ta Mama, rigima ce kawai ke damunta, yaushe ne tafiyar taku?" Mama ta ce "Biyar ga azumi Insha Allah." Haneefah ta ce "Allah ya kai mu, sannan ta yiwa Mama Sallama suka fice ita da Neehal wadda zata ɗan taka mata. Bayan Sallar Magriba Neehal ta yiwa Sadik text kamar yadda suka yi da Haneefah zata masa.
Chapter 61 · 0% Book details