← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 118

Sashe 97

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

A part ɗin Mama kuwa, ba jimawa da fitar Neehal Mama ta miƙe ta shiga ɗakinta, a lokacin ne kuma kiran Ahmad ya shigo wayar Neehal dake hannun su Afrah. Suka dinga shafa wayar har Allah ya ba su sa'a su kay picking ba tare da sun sani ba. Amrah ta ƙara danna wayar a ƙoƙarin ta na ganin sun koma game ɗin da suke, ashe gurin speaker ta danna. Jin muryar Mahaifinsu yana sallama suka ruɗe da murna. "Daddy! Daddy! Daddy!" Kowacce na son ya yi magana da ita. Ya ce "Oh, sweethearts zaku kashewa Daddy kunne fa." Afrah ta ce "Daddy Aunty ta ce ka tafi ka bar mu." Ya ce "Ai zan dawo in ɗauke ku soon, ko baku san zama a gurin Aunty." Suka ce "Muna so." Ya ce "Yawwa yaran kirki, ina Aunty? Ko bacci take?" Amrah ta ce "Ta fita gurin Uncle Sadik." A kwance yake amma bai san sanda ya tashi zaune ba. A fili ya ce "What? who is he?" Ya yi maganar a gigice. Afrah ta ce "Daddy yana zuwa gida gurin Aunty, yana da kirki yana ba mu chocolates." Amrah ta karɓe zancen da faɗin "Shi ya kai mu gidan Aunty Haneefah da ana bikinta." Ahmad ya had'iye wani abu da ya tsaya masa a mak'oshi, da ƙyar ya iya cewa "Unguwa suka je?" Afrah ta ce "No, Mama ta ce suna waje a zaune." Ya cize lip ɗinsa da ƙarfi, tare da faɗin "Damm it." Yaran suka ce "Hello Daddy." Ya sauke numfashi ya ce "Bye Dear, I will her call later." Ya kashe wayar ya cillar akan gado. Kansa ya dafe da hannunsa yana zancen zuci. Me yasa tun farko bai yi tunanin Neehal tana da wani saurayin ba? a age ɗinta dama dole a ce tana da samari ba ma saurayi ɗaya ba. Hankalin Ahmad fa in ya yi dubu ya tashi, ya maimaita sunan Sadik a cikin ransa ba a dadi, kamar mai neman wani abu a cikin sunan. Ji yake kamar ya yi tsintsuwa ya gan shi a Kano, ya ga wane Sadik ɗin nan da his future wife take kulawa. "Kenan tana son shi?" Ya faɗi haka a fili cikin tsananin damuwa. 'Tana son shi mana tunda har take kula shi.' Zuciyarsa ta ba shi amsa da haka. "Ya Allah!" Ya furta haka a fili wani irin kishi na nuk'urk'usar zuciyarsa.

Sai wajen 9 Sadik ya tafi, bayan ya gama wanke mata zuciyarta tass, ya kuma roƙe ta kar ta sanar da Mama abun da ya tambaye ta, bare itama hankalinta ya tashi. Tay masa alƙawarin ba zata faɗa mata ba. A bakin part ɗin Mama tana ƙoƙarin danna door beil, ta ji k'amshin Ameen ya cika mata hanci, ta juya bayanta da sauri suka yi 4 eyes da shi.........✍️
[7/21, 9:32 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*

_By_
_Zeey Kumurya_

*5️⃣4️⃣*

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*

Gaba-ɗaya sai ta duburburce ta rasa ina zata saka ranta saboda tsoro da kunya. Ya ƙaraso ba tare da ya ce komai ba ya buɗe ƙofar da key ɗin part ɗin dake gurinsa ya shige. Ta turo baki tare da bin bayansa, a ranta tana faɗin. 'Ya bar gidan ma amma har yanzu yana tare da key ɗin part ɗinsu.' Ya tsaya bayan ya shiga falon yana kallon ta, ta sunkuyar da kanta ta ce "Ina yini?" Ya ce "Lafiya, Ya jikin?" Ta ce "Da sauƙi." Ya ce "Allah ya ƙara sauƙi." Bai jira amsar ta ba ya nufi upstairs. Ta d'ago kanta tare da sauke ajiyar zuciya ta bi bayan shi zuwa saman. Babu kowa a falon hakan yasa ta nufi bedroom ɗinta, a nan ta tarar da su Afrah kwance akan gado suna bacci. Ta ajiye mayafin jininta tare da kwanciya ta lumshe idonta ta faɗa duniyar tunani. Ameen kuwa ɗakin Mama ya shiga, bayan sun gaisa ta ce "Neehal ta ce mun ka zo da safe ina gurin aiki." Ya ce "Eh." Ta ce "Ya jikin Hafsan?" Ya ce "Ta ji sauqi." Mama ta ce "Allah ya ƙara sauƙi." Ya miƙe ya ce "Ameen, bari na je gurin Dad." Mama ta ce "Okay." Bayan fitar sa Mama ta ɗauki wayar Neehal data karɓa a hannun su Afrah ta nufi ɗakinta, dan dubawa ko ta dawo." Turo ƙofar ɗakin da Mama ta yi yasa ta buɗe ido, Mama ta ce "Har kin dawo kin kwanta kenan?" Ta ce "Ban jima da dawowa ba." Mama tana mata kallon tsaf ta ce "Are you Okay?" Ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Kaina ke mun ciwo." Mama ta ce "Allah ya sauqaqe sai ki tashi ki ci abinci ki sha magani." Ta ce "Toh." Tare da karɓar wayarta da Mama ke miƙo mata." Mama ta ce "Sai kiran ki ake, waye yake miki wannan kiran ne haka?" Tana latsa wayar ta ce "Uncle Ahmad ne, yaransa yake son magana da su may be." Mama ta ce "Sai ki kira shi ki sanar masa sun yi bacci." Ta gyaɗa mata kai, amma bata jin zata iya kiran nasa. Mama ta juya ta fita bayan ta ƙara jajjada mata ta fa tashi ta ci abinci ta sha magani. Ta fi awa bayan fitar Mama tana sak'awa da kuncewa sannan ta miƙe ta fito ta sauka ƙasa. Abinci ta ɗebo ta ci, sannan ta dawo ta sha magani. Har time ɗin bata kira Ahmad ba, shi ma bai ƙara kiran ta ba. Ta shiga toilet tay wanka ta fito ta shirya cikin kayan bacci masu taushi ta kwanta, text kawai ta yiwa Sadik ta yi addu'a ta tofa wa su Afrah sannan ta shafa a jikinta, ba jimawa bacci ya ɗauke ta.
Chapter 97 · 0% Book details