← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 118

Sashe 103

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya miƙe ya fita, ta tashi ta cire hijabin jikinta ta ninke, sannan ta ɗauko mayafin abayar dake jikinta ta yane kanta da shi, ta fesawa jikinta turare kaɗan sannan ta ɗauki wayoyinta ta bi bayan shi. A falo ta zauna jiran shi, ba jimawa ya fito daga ɗakinsa inda Hafsat take a yanzu. Da ido yay mata alamar ta tashi su tafi, ba tare ta ce komai ba ta miƙe ta bi shi a baya. A falo ta tarar da su Harira suna kallo, su kai musu a dawo lafiya. Restaurant suka je ya siyo musu abinci, daga nan kuma ya biya ya siyo mata ice-cream da choculate da ya san tana matuƙar son su. A hanyar dawowa ta shagwab'e fuska ta ce "Yaya ka kai ni in ga Mama, sai mu dawo." Ba tare da ya dube ta ba ya ce "Ba ta ce zasu zo ba?" Ta ce "Ai na san da ƙyar za su zo, dama haka ta ce sai ta samu time." Bai kuma magana ba bai kuma kaita gidan ba, gidansa suka koma. Bayan an yi Sallar isha'i ta ci abinci sai ta sauko ƙasa gurin su Harira dan su yi hira. Saude ta ce "Mai kyau, d'azu na gan ki a talabijin." Neehal ta yi murmushi ta ce "Ni kuma? ba ni ba ce gaskiya, sai dai mai kama da ni." Saude ta ce "Alkur'an ke ce, da na je kaiwa Hajiya kifin data ce in sake d'umama mata ne na ga mai_gidan yana kallo, kuma har ɗan tsayawa na yi na ga kayan da kika fita da su ne a jikin wadda na gani." Neehal ta yi ƴar  dariya saboda yanda Sauden ta yi maganar ta ce "Ƴan biyu ce ni ai, to ɗayar kika gani ba ni ba." Saude ta ce "Tab' amma kuna kama sosai, har fa yanda kike yi da idonki haka take yi." Neehal ta ce "Ya nake da idon?" Harira ta gyara zama ta ce "Ni zan gwada miki." Sai ta wani lumshe ido ta buɗe tare da keɓe baki ita a dole iyayi take tana gwada yanda Neehal take magana. Neehal ta yi dariya sosai wadda ta ƙara fito da kyawun fuskarta, kumatunta suka lotsa kamar an cire naman gurin. Saude ta taɓa dai_dai gurin cikin santi ta ce "Ke kam ki godewa Allah, ya baki kyau, wannan abun yana ban sha'awa, tun ɗazu in kina magana shi kawai nake kallo." Neehal ta ce "Allah ya baki miji mai irinsa, sai ki yi ta kallon sa." Saude ta washe baki ta ce "Allah ya amsa bakin ki mai kyau." Suna cikin hirar su mai daɗi dake sanya Neehal nishad'i Ameen ya shigo falon, sai ta ga su Harira cikin sauri sun tashi sun shige ɗakin da suke bayan sun masa sannu da zuwa. Neehal ta bi su da kallo, sannan ta mayar da idonta kan Ameen dake kallon ta hannunsa riƙe da leda, ta ɗan ɓata fuska ta ce "Sannu da zuwa." Ya ce "Yawwa." Tare da shiga kitchen ya ajiye ledar hannunsa, ya dawo falon ya ce wa Neehal. "Miemerh Please ki shiga kitchen ki soyawa Hafsah kajin can." Neehal ta ɓata fuska amma bata ce komai ba ta tashi ta shiga kitchen ɗin dan babu musu a tsakanin ta da shi. Ya bi bayan ta zuwa kitchen ɗin, ta juyo ta kalle shi, ya nuna mata inda kajin suke. Ta ɗauko tana turo baki gaba ta juye su a abu, a yayyanke suke a wanke tass. Ta ƙara ɗauraye su, ta ɗauko tukunyar da zata cinye su ta ɗauraye ta juye su a ciki, sannan ta saka musu magi da spices da ɗan yaji ta kunna gas ta ɗora. Duk abun da take yana tsaye yana kallon ta, ya jingina da ƙofar kitchen ɗin. Bayan sun mata yanda take so ta sauke ta tsame su ta zuba a cikin colander, sannan ta tsiyayo mai a jarka ta zuba a kasko ta ɗora akan gas ɗin. Ta ƙara juyowa ta ga har lokacin yana kitchen ɗin, ta turo baki ta cigaba da abun da take. Har ta fara soyawa bai fita ba, ita kuma duk ta takura kamar ta ce masa ya fita. Sai da ya gaji dan kansa ya fita. Tana soya na ƙarshe ya dawo kitchen ɗin, naman ya yi irin ƙarar nan da yake yi a cikin mai, har man ya ɗan fallatso mata a hannu. Ta ɗan ja baya tare da yarfe hannun, ya matso kusa da ita da sauri ya kama hannun yana dubawa. Ta shagwab'e fuska kamar zata yi kuka. Murya ƙasa_ƙasa ya ce "Sorry dear, don't cry." Ta kalli fuskarsa tana turo baki gaba tare da gyaɗa masa kai, Idanunsa suna kan hannunta hakan yasa ta ƙurawa fuskarsa ido kamar mai neman wani muhimmin abu a fuskar, sai da ya d'ago sannan ta yi saurin lumshe idonta tare da sakin ajiyar zuciya a hankali. Ta matsa daga kusa da shi tare da zare hannunta daga nasa. Ya ce "Zaki iya ƙarasa suyar kuwa?" Ta d'aga masa kai alamar eh. Ya juya zai fita cikin siririyar murya ta ce "Yayah.!" Ya juyo ya kalle ta ba tare da ya amsa ba. Ta yi shiru dan ta kasa faɗar abun da yake ranta, ba yabo ba fallasa ya ce "What happened?" Ta ce "Nothing." Yay mata wani kallo sannan ya juya ya fice. Ta sauke numfashi tana jin zuciyarta na mata wari irin lugude, wani b'arin na zuciyar kuma mamakin Ameen take, yanda yake mata magana babu faɗa bare haɗe rai, ko dan ta zo gidansa ne? Jiki a sanyaye ta kwashe sauran naman da ya fara k'onewa. Sai da ta kimtsa kitchen ɗin sannan ta fice. Tana komawa ɗaki ta tarar da missed call ɗin Mama da Ahmad. Mama ta fara kira, tana ɗauka ta ce mata. "Shine ba ku zo ba Mama?" Mama ta ce "A gajiye Dad ya dawo ne shi yasa, sai gobe Insha Allah, ina kika shiga nay ta kiran ki?" Ta ce "Ina ƙasa, wayar kuma tana sama a ɗaki." Mama ta ce "Ya jikin Hafsan?" Ta ce "Da sauƙi." Mama ta ce "Babu matsalar komai dai?" Ta ce "Nothing Mama, ina Dad?" Mama ta ce "Ya kwanta bacci, saboda gajiyar dake damun sa, shi yasa ni kiran ki ɗazu ai, kuma baki d'aga ba, yanzu kuma ya yi bacci." Neehal ta ce "Ki gaishe shi idan ya tashi, har na fara kewarku Mama." Ta ƙarashe maganar cikin shagwab'a. Mama ta ce "Rigimarki da yawa take Daughter, yau ma fa kin gan mu." Ta ɓata fuska ta ce "Ni dai dan Allah ku zo gobe in gan ku." Mama ta ce "Allah ya kai mu goben lafiya, daga haka suka yi sallama ta katse wayar. Ahmad ta kira, kamar mai jiran kiran ringing ɗaya ya katse ya kira ta. "Princesss.!" Ya kira ta cikin shauƙi, bayan ta ɗaga ta ce "Uhm, Uncle ina yini?" Ya ce "Ga shi nan, babu daɗi tunda yau throughout ban ji muryarki ba." Ta ce "To yanzu ka ji ai, sai ka ji daɗin." Ya yi murmushi mai sauti ya ce "Ni da jin daɗi Baby ai sai ranar da aka kawo mun ke gidana a matsayin mata, na san zan yi farincikin da ban taɓa yin irinsa ba a rayuwata Princess, na san a ranar i war haka masu kawo mun ke sun tafi, sai mu kaɗai a gidanmu, muna making love." Ta rufe fuska kamar yana gabanta cikin jin kunya, ya ce "Princess ban san irin son da nake miki ba, kuma na san duk bayanin shi da zan miki baza ki gane ba, amma da zarar kin zama tawa, I know you will understand it more." Ta sauke numfashi ba ta ce komai ba, Ahmad da Sadik suna ɗaure ta da jijiyoyin jikinta, ga abun da yake ƙara bata haushi idan tana tare da kowannen su Heart ɗinta shi kaɗai take tuna mata, ta rasa gane wa take so da k'auna a cikin su, zuciyarta ta kasa tantance mata wanda ya kamata ta zab'a a matsayin abokin rayuwarta. 'Na barwa Allah zaɓi, Allah ka zaɓan mafi Alkhairi.' Ta faɗi haka a cikin ranta. Ahmad ya cigaba da yi mata hira mai daɗi cikin iya tsara kalamai masu kwantar da zuciya. Har bacci ya fara cin ƙarfin ta, saboda gajiyar dake tattare da ita. Jin hakan yasa yay mata sai da safe ya katse wayar, tashi ta yi dak'yar tana lumlumshe idanuwa ta rage kayan jikinta sannan ta kashe hasken ɗakin, ta kunna fitilar gado. Har ta kwanta ta ƙara tashi ta kunna light ɗin ɗakin sannan ta shiga toilet ta yi fitsarin da ya matse ta, bayan ta fito ta kulle ƙofar ɗakin tare da kashe light, sannan ta hau kan gadon ta ware bargon dake ninke a gefen gadon daga gurin bango ta lullub'e jikinta. Da ƙyar ta iya yin addu'ar kwanciya bacci, saboda baccin dake cin ta.

Cikin dare ta yi juyi, haka Allah ya halicce ta indai zata yi juyi a bacci sai ta ɗan farka, kamar an ce ta buɗe ido sai ta ga kamar an turo ƙofar ɗakin an shigo, ta ware idanunta dan tabbatarwa gabanta na dokawa a million. kamar a mafarki ta ga ana nufo gadon ta ɗan hasken bedside lamp. Ta ƙara waro idonta ganin dagaske fa ita ake tunkarowa har anzo bakin gadon, ta yunƙura ta tashi zaune cikin rawar jiki tare da ware baki da nufin ta ƙwala ƙara, amma sai ta ji ana fesa mata wani abu a fuska kamar shantos, ta fara jujjuya kai a ƙoƙarin ta na nemo iskar Ubangiji ta shak'a ba wannan abun mai wari da ake fesa mata ba. Cikin sakanni ƙalilan hankalinta ya gushe daga jikinta, daga nan bata ƙara sanin inda kanta yake ba.........✍️
[8/7, 9:21 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*

_By_
_Zeey Kumurya_

*5️⃣6️⃣*

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*
Chapter 103 · 0% Book details