← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 118

Sashe 80

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A cikin week ɗin nan Neehal ta je gidan Aunty Sadiya kamar yadda Mama ta umarce ta, ta kai mata ziyara. Aunty Sadiya ta yi amfani da wannan damar ta ƙara yiwa Neehal tambayoyi a game da binkicen da take na kisan su Anwar, kuma Alhamdulillahi ta ƙara samun wasu evidence ɗin. Ranar Friday kamar yadda Sadik ya ce suka dawo lafiya daga Ibadan. Delicious sosai Neehal ta haɗawa masa na tarb'ar sa, ta bayar aka kai masa har gida, tunda bai samu zuwa gurinta ba saboda sai yamma lik'is suka dawo. Sai washegari Saturday ya zo suka sha hirar su. A kwanakin nan da suka  wuce kullum Neehal sai sun yi waya da Ahmad every Morning and Night. Ranar Sunday tun ƙarfe goma sha ɗaya na safe ta shirya dan zuwa gidan Uncle Umar bisa tilastawar Mama. Tana aikin turo baki gaba ta shiga ɗakin Mama dan yi mata sallama. Mama ta dube ta, ta ce "To Haka zaki je musu hannu Rabbana." Ta ƙara ɓata fuska ta ce "Toh Mama me zan kai musu, ni fa dak'yar ma idan zan gane gidan." Mama ta ce "In kin je kar ki gane ɗin, ki ɓata, da duk da muke zuwa wani ne yake raka mu ai." Neehal ta ce "Toh Mama ai yanzu na daɗe ban je ba." Mama ta ce "Ko me zaki yi fa sai kin je, gwara ma ki bar wani kame_kame. Ki duba cikin drower ɗin  can zaki ga kuɗi ki ɗauki 10k, sai ki biya ta Mall kafin ki tafi ki yiwa yaransu tsaraba." Ta ƙarasa ta ɗauki kuɗin tana faɗin "An gode." Mama ta ce "Kin haɗa kayan wankin da na ce ki haɗa?" Ta gyaɗa mata kai alamar eh. Mama ta ce "Har su bedsheet da labulayen?" Ta ce "Eh duk na haɗa." Mama ta ce "Shikenan ki wuce ki tafi, Allah ya kiyaye, ki gaishe su." Ta amsa tare da ficewa daga ɗakin. Two days bata ga Motar  da take bin bayanta ba, ta yiwa Allah godiya tare da addu'ar Allah ya yi mata iyaka da koma su waye. Sai da ta biya ta siya musu kayan su chocolate duk da ta san yanzu su Iman sun girma, ta haɗa musu da turaruka da sabulan wanka, dan rasa me zata yi musu tsarabar da shi ta yi. Sha biyu da ƴan mutuna ta ƙarasa ƙofar gidan, ita kanta ta yi mamaki data iya gane layin, ko da yake layin ba shi da wahalar ganewa tunda miƙa ɗaya za kai daga titi har gidan. Da shagon wani mai aune_aune take gane gidan Uncle Umar da yake pacing ɗin gidan . Tabbas inda ta tsaya nan ne gidan, amma abun da ya bata mamaki ganin yanda gidan ya ƙara girma da kyau, filin kusa da gidan aka haɗe da gidan aka gine. A ranta ta ce "Ko sun tashi daga gidan ne? Ta day yi k'undunbala ta fito daga cikin Motarta hannunta ɗauke da ledar data musu shopping ta ƙarasa ta fara knocking ƙofar gidan. Muryar da ba za ta taɓa mantawa da ita ba a rayuwarta ta ji ta ce "Waye?" Ta sauke numfashi ta ce "Ni ce." Aunty Fauziyya ta ce "Turo ki shigo." Kanta a ƙasa ta tura ƙofar ta shiga tare da yin Sallama. Aunty Fauziyya da wata bak'uwar murya a gurinta suka amsa mata. Ta d'ago karaf suka haɗa ido da Aunty Fauziyya. Cikin mamaki Aunty Fauziyya ta ce "Neehal!" Ta ƙirƙiro murmushi ta ce "Na'am Aunty." Tare da bin ta da kallo ganin yanda ta zabge ta rame ta yi wani uban baƙi. Ɗayar matar da Neehal bata san ta ba cikin fara'a ta ce "Sannu da zuwa, ki ƙaraso mana." Neehal ta ƙarasa ta inda suke sannan ta ɗan tsugunna ta gaishe su. Ɗayar ce kawai ta amsa, Aunty Fauziyya kuwa mamaki ne ya sandarar da ita. Matar wadda ke sanye cikin atamfa doguwar riga tayi shar abunta ta ci d'aurinta ta kamo hannun Neehal ta yi hanyar sabon ginin da Neehal taga an yi a gidan tana mata lale marhabin. Sai a lokacin Aunty Fauziyya ta yi magana ta ce "To ai ba gurinki ta zo ba, tunda ba ma sanin ki ta yi ba, zaki wani janye ta daki." Matar ta juyo ta yiwa Aunty Fauziyya wani kallo sannan ta juya hannunta still riƙe dana Neehal suka shiga ƙofar part ɗin nata bayan ta buɗe. Ta nunawa Neehal guri a falon ta ce "Bismillah ki zauna bari in kawo miki ruwa." Neehal ta ɗan murmusa sannan ta zauna zuciyarta cike da tarin tambayoyi, ko shakka bata yi Uncle Umar ne ya ƙara aure, dan kwanaki suna waya da Uncle Usman ya fara mata zancen kuma sai wayar ta katse, data bi bayan shi kuma wayar ta ƙi shiga. Ita kuma bata wani riƙe zancen a ranta ba saboda a ganinta ba sabgarta ba ce. To an ma auren da Uncle Umar ya ƙara shine ya mayar da Aunty Fauziyya haka ta lalace ta zama kamar wata tsohuwa, ko kuma cuta ta yi... Dawowar matar falon ya katsewa Neehal tunaninta. Matar ta ajiye mata ruwa da juice a gabanta, sannan ta ƙara shiga kitchen ta dawo hannunta ɗauke da abinci. Neehal ta ce "Na gode." Matar ta ce "Babu komai, dan ma bamu san da zuwanki ba kawai ganinki mu kai, ai da an tanadar miki ko ɗan wani abu ne." Neehal ta ce "Babu komai, hakan ma Na gode sosai." Matar ta ce "Neehal ko Yar gidan Yayar Umar?" Bata jira amsar Neehal ba ta cigaba da faɗin "Ai na ji labarin ki a bakin Binta mak'ociyarmu da kuma shi kansa mai gidan namu." Neehal ta yi shiru cikin mamakin jin Uncle Umar ne har yake na zancen ta, ashe yana sane da ita kenan. Neehal ta ce "Ina su Iman fa ko basa nan?" Matar ta ce "Suna islamiyya, amma sun kusa dawowa, ɗaya tana yi zaki gan su sun dawo." Ta jinjina kai ta ce "Uncle fa? Sai dare yake dawowa shi ko?" Matar ta ce "Zaki iya ganinsa ya dawo anjima da yamma." Neehal ta yi shiru dan ba ma ta so su haɗu da shi. Haka matar ta yi ta jan Neehal da hira cikin fara'a da karamci, ta takurawa Neehal ta ci abinci tana mata tsiyar kamar ba gidansu ba ta ƙi sakin jikinta. Bayan ta ci abincin kaɗan ta yi Sallah sannan ta bawa Matar ledar data shigo da ita. Matar ta karɓa ta mata godiya ta debi abubuwan cikin ledar kaɗan ta bawa Neehal ta ce ta kaiwa Aunty Fauziyya sauran. Neehal ta fito ta tarar har lokacin Aunty Fauziyya tana tsakar gidan a zaune akan kujera yar tsugunne. Kallo ɗaya zaka mata ka fuskanci tana cikin damuwa. Aunty Fauziyya Ta shigar da Neehal ɗakinta cikin fara'ar data bawa Neehal mamaki. Bayan sun ƙara gaisawa ta ce "Neehal kin ƙara girma da kyau Masha Allah." Neehal ta yi murmushi kawai. Aunty Fauziyya ta cigaba da bin ta da kallo cike da sha'awa, a ranta tana faɗin kamar ba'a Nigeria take rayuwa ba saboda kyawun fatarta da hasken ta, ga k'amshin ta mai daɗi daya cika mata hanci irin na ƴan gayu. Ta sauke ajiyar zuciya ta fara bawa Neehal labarin abubuwan da Uncle Umar yake mata yanzu dan ya ƙara aure. Wai wulaqancin yau daban na gobe daban suke mata shi da matar tasa, har da k'wallar ta. Neehal ta ce "Ta yi haquri kawai." Dan bata san me zata ce mata ba, bayan haqurin. Daga ƙarshe kuma ta fashe da kuka wai Neehal ta yafe mata ko alhakin ta ne yake bibiyar  ta. Ta ce ita ta yafe mata, dama can bata riƙe ta ba. Sai kuma ta bata labarin ɓacin da Iman ta yi, wai yarinyar bata ji har bin maza take. Haka dai tay ta yiwa Neehal zance kamar wadda aka tambaya. Ita kuma duk sai ta ji tausayinta ya kamata har da zubar mata da hawaye. Suna cikin hirar su Iman suka dawo daga islamiyya, kallo ɗaya Neehal ta mata ta tabbatar da abun da mahaifiyarta ta faɗa. Yarinyar ta ci uban bleaching har da b'ular hanci, sai taunar cingum take ƙas_ƙas. Neehal tay ta mamakin ta a cikin ranta, yarinyar da bata fi 16 years ba amma ita ta yi wannan budewar idon haka. Ta ji ba daɗi sosai akan halin yarinyar, ko ba komai jininta ce bata so ta yi wannan lalacewar haka ba. Addu'ar shiriya ta mata a gurin Ubangiji, domin ita ce kawai mafita.
Chapter 80 · 0% Book details