← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 118

Sashe 37

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

_By_
_Zeey Kumurya_

*2️⃣4️⃣*

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*

Direct gida Ameen ya nufa da ita, domin ya san duk taimakon da za a bata a asibiti Mama za ta bata. Mama tana zaune a falo tana azkar ɗin yamma ta ga Ameen ya shigo mata da ƴa a hannu, a ruɗe a tashi tana dubansa ta ce "Al'ameen me ya same ta?" Sai da ya kwantar da Neehal a kan kujera sannan ya ce "Mama ciwon cikinta ne ya tashi." Mama ta ƙarasa inda take tana mata sannu, Neehal dai hawaye kawai take. Mama ta ce Ameen ya kai mata ita sama bari ta haɗa allura ta yi mata, insha Allah ciwon zai lafa mata yanzu.

Bayan 10 minutes Neehal har ta samu bacci saboda allurar da Mama ta yi mata, Mama dake zaune a gefenta ta sauke ajiyar zuciya cikin tausawa Neehal ɗin, gyara mata kwanciya ta yi daga ruf da cikin da ta yi sannan ta fice. Ameen yana falo tare da Twins har time bai tafi ba. ya dubi Mama ya ce "Ya jikin nata?" Mama ta ce "Alhamdulillah ta samu ya lafa mata har bacci ya ɗauke ta, dama haka ciwon nata yake kamar aljanu, lokaci ɗaya zai zo amma tana shan magani ko aka mata allura zata ji sauƙin shi 70%." Jinjina kansa ya yi kawai, a ransa yana mamakin wannan ciwon nata da baya jin magani, dan idan bai manta ba kusan 10 years kenan Neehal take fama da shi. Sun ɗan taɓa hira da Mama akan rashin bayyanar wanda ya san su twins har yau, sannan yay wa Mama Sallama ya tafi. Ko da ya koma gida Hafsah bata nuna masa komai na ɓacin rai ba, sai ma tambayarsa jikin Neehal da ta yi. Washegari da Neehal ta tashi lafiya k'alau ta tashi, sai dai ɗaurewar ciki kawai wanda duk lokacin period ɗinta haka yake mata, sai ta gama take jin ta normal.

*ABUJA*

Tun ranar da aka ba da cikiyar su Afrah misalin ƙarfe goma 12 na rana, budurwar nan ce zaune a falon gidansu tana kallon ASTV, 12 na yi aka fara labaran rana. Hankalinta ba ya kan TV'n dan bata damu da kallon labarai ba, kamar an ce ta d'ago idanunta suka sauka a kan hotunan twins ana cikiyar iyayensu. Wata muguwar zabura ta yi gabanta na tsananta bugu, ba ta san sanda ta cillar da wayar hannunta ba a matuƙar razane cikin ƙaraji  ta ce "What?" Mahaifiyarta ce ta fito daga bedroom tana dubanta da kyau ta ce " *Safeenah*! Ke da waye na ji kamar kina ƙara?" Tattaro nutsuwarta ta yi ta lalubi remote ta kashe TV dan kar mahaifiyartata ta ga cikiyar su Afrah da ake, ta sunkuya ƙasa ta ɗauki wayarta sannan ta dubi Mahaifiyartata ta ce "Ba komai Momma." Daga haka ta miƙe ta shige ɗakinta gumi na karyo mata ta ko ina a jikinta. Tab'e baki Momma ta yi ta wuce kitchen. Wani narkeken ashar Safeenah ta danna ta fara zarya a ɗakin a fili take faɗin "Lallai Gaye ya ha'ince ni, amma wallahi sai ya yi dana sanin cin amanata da ya yi." Ganin surutu ba mafita ba ne a gareta yasa ta ɗauki wayarta data cillar akan gado ta lalubo Numbern Aminiyarta kuma abokiyar shawararta. Bugu ɗaya ta ɗauka cikin tsananin tashin hankali Safeenah ta fara mata magana. "Na shiga uku Saudart, Gaye ya cuce ni ya ha'ince ni ashe Yaran nan be kashe su ba yar da su ya yi." "Ke wa ya faɗa miki haka?" Saudat ta tambaye cikin tarar numfashi. Safeenah na kuka ta ce, "Gashi nan na gani ana cikiyarsu a gidan TV an tsince su a Kano, yanzu ya zan yi ƙawata dan Allah ki ba ni shawara, ina tsoron kar asirina ya tonu." Ta ƙarashe zancen tamkar Numfashinta zai bar jikinta saboda tashin hankali. Saudat ta ce "Kin ga ƙawata ki kwantar da hankalinki, in dai ina raye ba zan bari hawayenki ya zuba ba, ki bani nan da zuwa yamma zaki sha mamaki, Gaye kuma zamu haɗu da shi zai san mu ya ha'inta." Safeenah zata yi magana ta ji wayar ta katse, zama ta yi a ƙasa dab'as tare da dafe kanta cikin rashin sanin abun yi. Ta san Saudat shu'umar kanta ce, yarinya ce mai buɗaɗɗan ido, ga shegen bin bokayen tsiya, a makarantar ABU Zaria suka haɗu da Safeenah har suka zama abokan juna. Ita Saudat ƴar cikin garin Zaria ce, ita ta bawa Safeenah shawarar tasa a sace su Afrah a kashe su, ita kuma ta haɗa ta da su Gaye sukai mata aikin. Yinin ranar cikin fargaba da tsoro Safeenah ta wuni, har wata yar ƙaramar rama ta yi, kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin firgici. Kamar yadda Saudat ta mata alƙawari da yamma ta kirata ta shaida mata ta je gurin wani boka ya mata aiki akan ko da mutum ya ga cikiyar su Afrah a rufe bakinsa ya kasa magana akai, kuma ta tabbatar mata aikin bokan tamkar yankan wuk'a yake. Wannan magana ta Saudat ita ta sanyaya wa Safeenah rai, domin kuwa ta tabbatar aikinsu ya ci tunda gashi har an fi sati amma babu wanda ya yi magana akan ya ga cikiyarsu Afrah da ake ta yi, kuma inda an gani za ta ji labari tunda gidansu ɗaya da Kakarsu Afrah ta wajen uwa, Safeenah ƙanwar mahaifiyar Su Afrah ce ubansu ɗaya. (Tsafi gaskiyar mai shi, Allah ka tsare mana imaninmu, Ameen ya Allah.) Su kam gidansu Mahaifin su Afrah ba su da nutsuwar wani kallon TV, kodayaushe suna zaryar asibiti hakan ya sa ba su ga cikiyar da ake ta yi ba. A ɓangaren su Kakarsu Afrah ta wajen uwa ma haka ne, tashin hankali bai barsu damar wani kallon TV ko sauraren Radio ita ƴaƴanta ba, hakan ya sa suma ba su ga cikiyar ko sun ji ta ba.

Ranar Laraba Neehal ta dawo daga school da yamma ta tarar da Aunty Sadiya wadda zuwanta kenan gidan daga wurin aiki ta biyo ta gidan. Neehal ta rungume ta tana faɗin "Auntyna oyoyo." Aunty Sadiya na murmushi ta ce "Oyoyo my Daughter, Ya school?" Neehal ta ce "Alhamdulillah, sai yau ma ni na koma." Aunty Sadiya ta ce "Allah ya taimaka, saura semester uku ku gama ko?" Neehal ta ce "Insha Allah." Mama ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da ruwa da glass cup, ta ajiye a gaban Aunty Sadiya, Aunty Sadiya ta ɗauki ruwan tana faɗin "Sannu Yaya, kamar wata baquwa sai kin kawo mun water." Mama ta ce "Ai na ga daga gurin aiki kike, kuma yanayinki ya nuna kin gaji." Aunty Sadiya ta ce "Hmmm bari kawai Yaya, yau tun 7 na fita office sai yanzu na samu kaina, case ɗin wannan Yarinyar da na ce miki an mata fyaɗe ne har yanzu ya ƙi ƙarewa, so suke su murd'e gaskiya ƙarshe ma idan ba ai wasa ba su kori shari'ar." Mama ta ce "Ai Allah ya fi su, kuma insha Allahu zai baku nasara." Aunty Sadiya ta ce "Allah ya amsa." Neehal ta dubi Mama tana turo baki gaba ta ce "Mama na dawo fa." Mama ta ce "Ai na ganki." Neehal ta ce "Ai ba ki yi welcoming ɗina ba." Mama ta ce "To bari in ɗauke ki in goya ki uwata." Neehal ba ta ce komai ba ta tashi ta wuce sama tana ɓata rai. Aunty Sadiya ta yi murmushi zuciyarta cike da tausayin Neehal. Neehal tana shiga ɗakinta ta tarar da twins sun ba je kayan kwalliyarta akan gado suna ta yaɓa wa fuskarsu. Suna ganin ta shigo suka fara kifkifta idanuwa, dan tasha yi musu faɗa akan in ta fita su daina yi mata b'arna a ɗaki. Cike da takaici take kallonsu, ganin yanda suka bata jikinsu da bedsheet da janbaki, ta ƙaraso cikin ɗakin tana faɗin "Sannun ku da aiki." Afrah ta nuna Amrah ta ce "Aunty ita ta ɗakko miki." Amrah tai sauri ta ce "Ba ni ba ce ita ce." Neehal ta ce "Ku sauka ni ku bari guri." Sauka suka yi daga kan gadon da sauri suna mutsitstsika janbaki a ƴan'yatsunsu. Tattare kayan da suka barbazar mata akan gadon ta yi, sannan ta cire zanin gadon ta kai toilet. sai da ta sake wani sannan ta kamo su Afrah ta cire musu kayan jikinsu ta musu wanka, sukwa sai murna suke an ƙara yi musu wanka, dan suna k'aunar wanka a rayuwarsu suga suna ta facal_facal da ruwa.
Chapter 37 · 0% Book details