Sashe 108
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Haneefah data Æ™ura mata ido tana sauraren ta, ta numfasa ta ce "Yanzu Neehal ke a karan kanki kin kasa zaÉ“ar wanda zuciyarki ta fi so, ta yaya wani zai iya zaÉ“ar miki? Ke baki san wa kika fi so a cikin su ba?" Cikin damuwa Neehal ta ce "Wallahi ban sani ba Besty, na kasa tantancewa, idan ina tare da wannan sai in mata da waccan." Haneefah ta ce "To duk ba son su suke ba." Neehal ta dube ta cikin mamaki tare da faÉ—in "Kamar ya?" Haneefah ta ce "Kamar yadda kika ji na faÉ—a, ai shi wanda zuciya take so baya b'uya, Neehal da ace kina son Sadik ko Ahmad idan kina tare da É—ayan su ba zaki taÉ“a mantawa da wanda kikewa son gaskiya a ba a cikin su. Daga Sadik har Ahmad tausayin su kawai kike ji, ko kuma wani a cikin su yana miki wani abu da yake burge ki, and kuma kina duba halacci ko kyautatawar da sukay miki a rayuwarki, amma so dai da k'auna na soyayya ba kya yiwa Sadik da Ahmad. Ni nafi tunanin akwai wanda zuciyarki take so, wanda ke kanki baki sani ba." Neehal ta É“ata fuska ta ce "Ni babu wani wanda nake so daban kuma, to wani saurayin ne dani bayan su da zan so shi?" Haneefah ta ce "Wanda ba kya taÉ“a mantawa da shi a cikin ranki, ko da kuwa kina tare da Sadik da Ahmad. Indai akwai wanda kike jin haka a kan shi to shi kike so." Neehal ta tab'e baki ta ce "Babu shi gaskiya, kema kin sani." Haneefah ta ce "Lokaci ne zai faÉ—a mana haka, amma now back to our business, wa kike ganin hankalinki ya fi kwanciya da shi a tsakanin su?" Neehal ta ce "Wannan ita ce tambayar da Mama tay mun, kuma na kasa tantancewa, shi yasa na zo mu haÉ—u mu tantance." Haneefah ta ce "Indai a yanda kika bani labari ne gaskiya zan fi so ki auri Sadik, saboda yanda yake da rauni akan soyayyar ki, kece mace ta farko da Sadik ya fara so a rayuwarsa, idan kika rabu da shi saboda Ahmad kin zalunce shi, saboda sai da ya gama sakankancewa ya samu mata sannan kuma ki canza zance. Time É—in da Ahmad ya dawo cikin rayuwarki already kuna tare da Sadik, dan haka yanzu idan kika bar shi kin yaudare shi, kuma hak'k'in shi ba zai barki ba. Sannan kuma ki duba yanda danginsa ba kowa ke son ku tare ba, idan kika rabu da shi kika watsa masa Æ™asa a ido za ai masa dariya, ace shi yana ta wahala a kanki ashe ma ke ba k'aunar sa kike ba, kuma Sadik ya riga Ahmad fara sonki." Neehal ta yi sauri ta ce "Uncle Ahmad ya riga, na faÉ—a miki fa tun ina yarinya farkon haÉ—uwar mu yake so na." Haneefah ta ce "Ai wancan lokacin daban, kuma ya wuce. Zancen yanzu ake da girmanki, amma ni dai shawara nake baki, dan ni Baban twins É—in nan ma bai wani mun ba, ya miki tsufa, gwara ki auri saurayi É—an shawalwali wanda zaku fi jin daÉ—in rayuwar auranku. Kuma na lura kalaman Ahmad da iya tsara mace ne suke rud'ar ki a kansa, dan na san ki da son soyayya, da son a nuna miki k'auna." Neehal ta ce "Ni duk ba wannan nake dubawa ba, ina duba taimakon da yay mun a baya, ni kuma yanzu yana buÆ™atar nawa sai in Æ™i taimaka masa? Kuma ga yaransa da muka shak'u da su, bana son rabuwa da su" Haneefah ta ce "Idan dan Allah yay miki ba zai yi wannan tunanin ba dan baki zaÉ“e shi ba, su Afrah kuma dan kin yi aure ai ba yana nufin kin rabu da su ba kenan, zaki cigaba da zumuncin ki da su, tunda Allah ne ya haÉ—a ku." Neehal ta yi shiru na tsawon mintuna biyu, sannan kamar zata yi kuka ta ce. "Haneefah! Uncle Ahmad yana so na Sosai, kuma duk abun da kika faÉ—a akan Sadik gaskiya ne, ya cancanci zama miji a gare ni, amma ban san da idon da zan kalli Uncle Ahmad na faÉ—a masa wannan maganar ba, Allah na yi dana sanin haÉ—a two dating at one time." Haneefah ta ce "Haka nan Sadik É—in shima idan kika zaÉ“i Ahmad zaki ji nauyin sanar masa kin zaÉ“i wanin shi a matsayin miji. Neehal! matar mutum kabarinsa, tun kafin ki zo duniya Allah ya riga ya rubuta wanda zaki aura, ki yarda da wannan, ki kuma dage da addu'a da neman zaÉ“in Allah, tunda kin san dai baza ki auri maza biyu ba ko?" Neehal ta ce "Haka ne Æ™awata, daren jiya ma kusan kwana na yi ina kaiwa Allah kukana tare da neman zaÉ“in sa." Haneefah ta ce "Yawwa, kisa a ranki kawai wanda kika zab'a shine mafi Alkhairi a gare ki, kuma shi Allah ya rubuta zai zamto mijinki." Neehal ta ji wani É—an sanyi a ranta, lallai ta yarda shawara tana daÉ—i. A hankali kamar wadda aka tilasta mata ta ce "Na zaÉ“i Ya Sadik, Allah yasa haka shi yafi Alkhairi." Haneefah ta ce "Amin ya Allah, shi kuma Ahmad Allah ya bashi tasa matar mai Alkhairin." Kamar zata yi kuka ta ce "Amin, amma ban san yanda zai É—auki wannan al'amarin ba, ina jin kamar ban kyauta masa ba." Haneefah ta ce, "Musulmi ne fa shi, kuma ya san qaddara mai kyau da mara kyau, Insha Allahu zai fahimce ki. Amma fa ba forcing É—inki nake akan Sadik ba fa, kawai ina baki shawara ne kamar yadda kika nema daga gurina, idan kin ji zuciyarki ta fi k'aunar Ahmad karki cuci kanki, ki zaÉ“i wanda kike so ki aura, dan aure ba abun wasa ba ne." Neehal ta ce "Hmm, Allah yasa ya fahimta É—in. No, ni da Ya Sadik da Uncle Ahmad duk É—aya ne a gurina, duk wanda na zab'a dai-dai ne, saboda duk sun cancanta." Ta yi shiru tare da É“ata fuska, sannan cikin damuwa ta ce. "Ni duk ba wannan ba ma, ina tsoron abun da ya faru a baya ya kuma faruwa." Sai ta fara hawaye sannan ta cigaba da magana. "Ina tsoron a kuma kashe mun wanda zan aura yanzu ma." Haneefah ta É“ata fuska ta ce "Oh my God, Neehal har yanzu baki daina wannan banzan tunanin ba, kin manta Allah ne me rayawa da kashewa." Neehal ta girgiza kai kawai ba ta ce komai ba, hawaye na cigaba da shatata a fuskarta. Haneefah ta matso ta rungume ta, cikin lallami ta ce. "Insha Allahu, Besty babu abun da zai faru sai Alkhairi, Allah yana sane da ke, ki miÆ™a masa k'ok'on bararki, shi kuma da yardarsa na san zai kawo miki É—auki. Kuma duk wanda yake kisan nan matuÆ™ar dan ke ake yi bisa zalunci da son zuciya Ubangiji zai saka miki cikin gaggawa, dan Allah yana karÉ“ar addu'ar wanda aka zalunta. Kuma rayuwar mumuni bata tafiya sai da jarrabawa, ke kuma wannan ita ce taki jarabawar, amma in kika yi haquri sai ki ga komai ya wuce tamkar bai taÉ“a faruwa ba, be a good Muslim please Dear." Haka dai Haneefah tay ta nusar da Neehal da nasihohi da kalamai masu daÉ—i gami da Æ™ara mata k'warin gwiwa akan Sadik, daga baya kuma ta koma tsokanarta da matar Barrister, an kusa shiga daga ciki. Har ta ji zuciyarta ta mata sanyi, kaso mafi yawa na damuwar da take ciki ya tafi. Shi yasa take son Haneefah, because mutum ce har da Æ™ari, kuma ta san baza ta taÉ“a bata shawarar da zata cutar da ita ba. Amma wani b'arin na zuciyarta sai tambayar ta yake akan anya ta yiwa Ahmad adalci kuwa? Sai bayan Magriba sannan ta bar gidan, shi ma sai da Mama ta kira ta a waya, dan sosai ta ji daÉ—in kasancewa da Besty'n tata.........âœï¸
[8/7, 9:21 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*5ï¸âƒ£8ï¸âƒ£*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*
[8/7, 9:21 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*5ï¸âƒ£8ï¸âƒ£*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*