← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 118

Sashe 98

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan kwana biyu ranar Juma'a da safe ta samu Mama a ɗakinta ta ce mata. "Mama Ya Sadik ya matsa wai sai na je gidansu na gaishe da Maamah." Mama ta ce "To ki shirya anjima ki je mana." Ta ce "Ni dai Mama kunya nake ji, kuma ba zan iya zuwa ni kaɗai ba." Mama ta ce "Maganin rashin zumuncin ki kenan, da kina zuwa ki kaiwa Freind's ɗinki ziyara da yanzu sai ki kira wata ta raka ki ku je." Ta ce "Bari in kira zee ta B.U.K." Mama ta ce "Tunda baki da kunya ba, yarinyar nan haka tay ta zuwa gidan nan amma saboda ba kya zuwar mata itama ta gaji ta daina zuwa, yanzu kuma sai ki kira ta ki ce ta zo ta raka ki ko? Tunda zaman ki take." Ta marairaice fuska ta ce "Allah sarki, Haneefah tah, ga ranarta ta zo." Mama ta ce "Bari na kira Hajiya Rabi, idan Salma tana free yau sai ta zo anjima ku je." Neehal ta yi murmushin jin daɗi ta ce "Yawwa Mamana." Mama ta ɗauko Wayarta ta kira Hajiya Rabi wadda ta kasance ƙawarta ce, Salma kuma ƴarta ce baza ta fi mate ɗin Neehal ba. Bayan sun gaisa Mama ta roƙe ta alfarmar zuwan Salman idan babu abun da take. Hajiya Rabi ta ce, zata zo insha Allah bayan an sauko daga masallaci. Mama tay mata godiya su kay sallama. Ta dubi Neehal ta ce "Sai ki kira shi ki sanar masa ya zo da yamma ya kai ku." Ta ce "Toh Mama, amma duk da haka ina jin kunya in na je me zance?" Mama ta ce "To ai ba zama zaku yi ba, gaishe su kawai zaki ku dawo." Ta ce "Tom, bari na je na kira shi." A safiyar Ahmad ya kira wayarta, ta d'aga ta saka a speaker sannan ta bawa su Afrah. Tun ranar Larabar nan da ya tafi ba su kuma magana ba, idan ya kira sai dai ta bawa ƴaƴansa, shima kuma ba ya cewa su bata wayar, ko zancen ta ba ya musu, sai dai su in sun masa maganarta yana biye musu. Ta yi shiru tana sauraren voice ɗinsa a cikin wayar, yana magana da ƴaƴansa cikin nishad'i. Sai ta ji ba daɗi sosai a ranta, na ƙin kulatan da yake kwana biyu, ta turo baki kamar yana ganin ta, jin yana cewa su Afrah ranar Sunday zai zo ya ɗauke su. Afrah ta kalle ta, ta ce "Aunty Daddy ya ce zai zo ya ɗauke mu ranar Sunday." Ba ta ce komai ba, sai lumshe idonta da ta yi. Ahmad ya ɗan lumshe idonsa cikin tsananin kewarta, ambatar sunan ta da Afrah ta yi kawai yasa ya ji ba zai iya jurewa ba sai ya ji muryarta a yanzu. A hankali ya ce "Ina Aunty?" Amrah ta ce "Gata nan, a kwance." Ya ce "Ku bata wayar." Suka matso jikinta suna kiran sunan ta, "Aunty, Daddy ya ce ki karb'i wayar." Tana jin su tay musu shiru, ta kuma ƙi buɗe idonta. Amrah ta ce masa. "Daddy ta yi bacci." Ya san ba baccin take ba, kawai wayar ce baza ta karɓa ba. Sai yay wa yaran sallama ya katse wayar ya tura mata text. Sai bayan sun gama surutunsu sun fita falo sannan ta tashi ta ɗauki wayar, a lokacin ta ga text da Numbern sa. Cikin sauri ta shiga karanta abun da ya turo. _Princess, ya jikin naki, I hope kin samu lafiya sosai. I MISSED YOU ALOT._ Ta ji wani murmushi ya subce mata, ko ba komai ya nuna care a kanta, duk da bata san me yasa 2 days ya daina kula ta ba, ita kuma tsananin kunyarsa ce tasa in ya kira take kasa pick. Tay masa reply da, _Ina lafiya Uncle, dafatan kai ma haka?_ Ta rungume wayar a ƙirjinta zuciyarta na azalzalarta akan ta kira shi, ta ji muryarsa. Duk da ta ji yanzu da suna waya da su Afrah, amma ta yi missed ɗin yanda yake mata magana da ita a cikin kunnenta cikin salo mai narkar da zuciya, tana ta tunanin nasa bata san bacci ya ɗauke ta ba. Sai ƙarfe ɗaya saura Mama ta tashe ta. "Ki tashi, ki shirya ki shirya su Amrah, ko kin manta zaku fita ne?" Ta tashi zaune cikin muryar bacci ta ce "Ban ma san sanda baccin ya ɗauke ni ba." Mama ta ce "Sai ki tashi yanzu, kafin Salma ta ƙaraso, gidan A'isha zaku fara zuwa sai ya je ya ɗauke ku a can." Tana sakkowa daga kan gadon ta ce "Toh."

Kafin ƙarfe biyu Neehal ta gama shiryawa cikin wani cotton material mai kyau, milk colour an masa ado da coffee colour, ɗinkin Baby gown ta yi das a jikinta. Ta yi simple d'auri da d'ankwalin material ɗin, sannan ta yafa mayafi coffee colour. Ta yi kyau sosai, hannunta ya ci zobuna da abun hannu, sai tashin sassayan k'amshinta take. Ta zira plate shoe coffee colour a farar ƙafarta, sannan ta ɗauki ƙaramar handbag itama coffee colour ta zira wayoyinta a ciki. Ta kalli kanta a mirror tana tambayar kanta 'Shigar jikinta ta dace data zuwa gidan surukai? Tun kafin tay wanka take ta tunanin kayan da zata saka a jikinta, da a niyyar ta Hijabi zata zumbula ta tafi, amma kuma data zo saka kayan sai ta fasa ta ɗauko na jikinta wanda bata taɓa saka su ba ta sa. Ta sauke numfashi tana jin zuciyarta wani iri akan zuwa gidansu Sadik ba tare data san dalili ba, ba yau ne first time ɗinta zuwa gidan surukai ba, ta je gidan su Anwar da Jameel, amma wannan sai ta ji kamar ta ce ta fasa zuwan. A hankali ta juya ta fice jikinta a sanyaye, a falon ƙasa ta tarar da Mama da Twins data shirya su tun d'azu, ta kora su gurin Mama dan ta samu damar shiryawa a tsanake. Afrah ce ta fara ganin ta, cikin kaud'inta ta ce "Aunty You look so beautiful." Neehal ta yi murmushi, Amrah ta juyo itama ta ce "Kin yi kyau Aunty." Tay mata murmushi ta ce "Thank you yaran kirki." Ta ƙarasa ta zauna a kusa da Mama dake kallon ta, ta ce. "Mama shiga ta bata yi komai ba?" Mama ta ce "Babu abun da ta yi, Daughter sai ma kyau da tay miki." Ta yi murmushi kawai, Mama ta ce "Na ga jikinki duk a sanyaye, ki saki jikinki Daughter babu abun da zai faru sai Alkhairi, Insha Allahu, wannan shine last zuwan ki another in-laws Family." Ta ce "Allah yasa." Ba jimawa da zamanta Salma ta iso gidan, cikin shiga ta mutunci. Black beauty da ita. Ta gaishe da Mama sannan suka gaisa da Neehal, Neehal ta kawo mata drinks ta sha kaɗan bisa takurawar Mama. Kafin ƙarfe uku sun isa gidan Aunty A'isha, Salma da yake she is so friendly tay ta tsokanar Neehal da suna tafiya, dan Mama ta mata bayanin inda za su je, Neehal kam sai dai tay mata murmushi kawai.

Sai bayan la'asar Sadik ya zo ya ɗauke su dan kai su gidansu, har da Maryam ɗin Aunty A'isha suka tafi. Ta so barin su Afrah a gidan Aunty A'isha, amma suka saka ihun sai sun bita, Aunty A'isha ta ce ta je da su kawai. Duk uban warning da ta ja musu akan kar su yi surutun su in je gidan, amma tun a Mota suka fara yiwa Sadik zuba, shi kuma yana biye musu cikin fara'a. Parking ɗin Sadik a compound ɗin gidan su, ya yi dai_dai da fad'uwar gaban Neehal. Ta lumshe ido a ranta tana fatan wannan gidan ya zama na ƙarshe a zuwa gaisuwar surukai a rayuwarta.

Salma ce ta fara fita daga cikin Motar su Afrah suka bi bayan ta cikin zumud'in sun zo unguwa sai kuma Maryam. Sadik ya dubi Neehal ya ce "What happened Wifey?" Ta ce "Nothing, me ka gani?" Ya girgiza kai tare da faɗin. "Babu komai." Ya buɗe Motar ya fita sannan ya zagaya ya buɗe mata. Ta ɗan ɓata rai tana masa kallon bata so hakan ba. Ya yi murmushi ya ce "To naga sai jan aji kike, Maamah kuma na san zuciyarta ta cika taf da d'okin ganin ki." Ta fito tana faɗin, "ni ma haka." Ya ce "Sure?" Ta ce "Sosai ma, waye ba zai so ganin Mamansa ba?" Ya yi murmushi, suka jera suka nufi cikin gidan, Salma na bin bayan su tare da tsokanar su tana faɗin. "Gaban dai Mama za'a je, a rage rashin ta ido." Neehal ta harare ta. Sadik ya ce "A'a gwara dai ta gani da idonta irin son da sirikar ta takewa ɗanta, ko Baby?" Neehal ta ɓata fuska ta ce "Kar ka sa in kasa shiga, ni ka yi gaba ma." Ya yi murmushi tare da yin gaban kamar yadda ta ce.
Chapter 98 · 0% Book details