Sashe 28
Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Neehal kuwa tana gama fitowa daga Motar ta dubi Ameen ta ce "Thank you." Ameen dake kallonta kamar zai cinye ta ya ce "Jira ni anan, kar ki je ko'ina." Bai jira amsarta ba ya nufi gurin Hafsat ya barta da baki a sake. Fadeelah ta sakar masa murmushi bayan ya ƙarasa inda suke tana faɗin, "Haba Ango ya zaka mana haka, gaskiya mun yi fushi." Ameen yana duban Hafsat wadda ta haɗe rai tare da ɗauke kai ya ce "Afuwan." Fadeelah ta yi murmushi kawai tare da matsawa ta koma gurin sauran ƙawayensu. Ameen ya kama hannun Hafsat ya ce "Ba magana." Hafsat ta d'ago ta kalle shi ba ta ce komai ba sai ƙura masa ido da ta yi ganin irin kyawun da ya mata, a hankali ta ce "Ka yi kyau sosai." Ya kashe mata ido tare da faɗin "Ke ma haka amaryata." Hafsat ta saki murmushi cikin tsananin farin ciki, gaba-d'aya ɓacin ranta ta neme shi ta rasa kasancewar Ameen a kusa da ita, dan sosai take farin ciki da Allah ya cika mata burinta na mallakar shi a matsayin miji. Neehal dake kallonsu ta tab'e baki tare da maida dubanta a kan wayarta, lalubo Numbern Sadik ta yi ta danna dialling. A lokacin ne kuma mutane suka fara zuwa inda Ameen da Hafsat suke suna ɗaukar su a hoto, Neehal dai bata motsa daga inda take ba takaicin Ameen ya kusa kashe ta na tsayar da ita da ya yi, gashi ta kira layin Sadik har sau biyu bai ɗauka ba, kiran Haneefah ta yi ringing uku ta d'aga, hayaniyar gurin yasa Neehal bata jinta sosai hakan yasa ta katse wayar. Sai daHaneefah ta fito daga cikin hall ɗin zuwa harabar gurin sannan ta kira Neehal, Neehal ta d'aga da sauri ta kara wayar a kunnenta. Haneefah ta ce "Wai ina kika tsaya ne Neehal? Tun d'azu nake ta baza ido ko zan ga kin shigo amma shiru, kuma na kikkira ki baki ɗauka ba." Neehal ta sauke numfashi ta ce "I'm sorry sai yanzu na ƙaraso ne." "Kina ina?" Haneefah ta tambaye ta cikin zak'uwa, Neehal ta ce "Ina harabar gurin tare da Yaya." Haneefah ta ɗan kalli gabanta inda take hango mutane ta ce "Gurin da nake hango mutane?" Neehal ta ce "Eh." Haneefah ta ƙaraso gurin tana duba Neehal, Neehal ta hango ta ta je kusa da ita tare da dafata tana faɗin "Ga ni nan fa." Haneefah ta juyo amma ta gaza cewa komai sai bin Neehal da ido kawai take ganin kayan dake jikinta da kuma irin kyawun da ta yi. Neehal ta ce "Ya dai, wannan kallon fa?" Haneefah ta ce "Na mamaki ne sai kuma kyawun da kika yi kamar ke ce amaryar, amma yana ga kin saka wasu kayan ba irin namu ba." Neehal ta shagwab'e fuska ta ce "Rigimar Yaya mana." Ta kwashe duk yadda suka yi da shi ta faɗa wa Haneefah a tak'aice. Haneefah ta yi murmushi ta ce "Kuma wallahi kin yi kyau sosai, makeup ɗin naki ma ya fi namu kyau." Neehal ta ce "Kuma takun ta yi kyau, ina su Ameera fa?" Haneefah ta ce "Suna ciki suna cashewa, nikam tunda na zo ko rawar ban yi ba, hankalina yana kan ki, musamman da kayan ki suke wurina, har fa Mama sai da na kira na faɗa mata, shima Yayan na kira shi bai ɗauka ba." Neehal ta ce "Shi yasa na ga missed call ɗin Mama." Haneefah ta ja hannun Neehal tana faɗin "Zo mu shiga ciki, kafin su amarya su shigo." Neehal ta kalli inda su Ameen suke ta ga anyi arranging ƙawayen Amarya da Abokanan Ango, domin shiga wurin. Ameen duk abun da ake hankalinsa na gun Neehal da ya tsaida ta, domin so yake su shiga gurin tare, amma suna zuwa inda ya barta ya neme ta ya rasa. A cikin hall kowa ya zazzauna filin rawa ma babu kowa, sai Mc dake ta karaɗin isowar ango da Amarya. Neehal kuwa gurin cousins ɗinta suka nufa, tana zuwa kowa ya fara yaba kyawun da ta yi, hotuna suka shiga ɗauka kowa yana so ya yi da ita. A nutse ƙawayen Amarya suka fara shigowa suna ɗan rausayawa abun gwanin sha'awa, nan fa mutane suka mik'ewa suna video a wayoyinsu, ga masu Camara ma nata fama ko ta ina, shigowar Ango da Amarya aka sauya sauti zuwa wak'ar masoya, a hankali suke tafiya har suka ƙarasa mazauninsu. Nan fa wurin ya fara cika da jama'a kowa yana so ya ɗauke su a hoto, da ƙyar Mc ya samu mutane suka ragu. Amarya da ango sun yi kyau sosai, abu ɗaya ne ya musu cikas rashin dacewar kalar kayansu, dan ita Hafsat gown ɗin jikinta purple colour ce. Hafsat har ta gaji da ciwon bakin da ƙawayenta suke mata akan me yasa ba su saka kaya kala ɗaya ba ita da Ameen? Itama ba ta ji daɗin hakan ba ko kaɗan, kuma ta tambayi Ameen ɗin tun kafin yau amma bai faɗa mata kalar kayan da zai saka ba. Neehal tana zaune dan su ba su tashi ba saboda cikowar mutane, ji ta yi kamar wayarta tana vibrate tana dubawa ta ga Ameen ne ke kiranta. Da mamaki ta ce "Yaya kuma, yana high table amma yana kira na, to me zan masa?" Haneefah dake gefen ta ta kama hannunta ta ce "Taso mu je, sai a mana hotuna ma da su." Neehal ba dan ta so ba ta mike tana faman riƙe riga suka je. Ta zauna a gefen Ameen Haneefah kuma ta zauna a gefen Hafsat aka ɗauke su a hoto, Neehal ta dubi Ameen ta ce "Yaya na ga ka kira ni." Ameen ya harare ta ya ce "Me na ce miki?" Neehal ta ɗan turo baki gaba ta ce "To ai na ga shigowa za ku yi shiyasa kawai na taho." Duk maganganun da suke masu ɗaukar hoto nata musu ba tare da sun sani ba, domin sai suka zama tamkar suke Ango da Amaryar. Neehal ta tashi ta zagaya bayan kujerar da suke ta ɗan sunkuya tsakanin Hafsat da Ameen ta ce "Aunty ina yini." Hafsat ta saci kallon Ameen ta ga ita yake kallo hakan yasa ta ɗan saki fuska ta ce "Lafiya k'alau." Neehal ta ce "Ya taro." ta ce "Alhamdulillah." Kusa da ita Neehal ta je ta zauna ta ɗan rungumo ta aka musu hoto, Hafsat kuwa ji ta yi tamkar Neehal wuta ta sa mata a jikinta da ta taɓa ta.
An cigaba da gudanar da shagalin biki yanda ya kamata, Amarya da Ango sun fito tsakiyar fili anata zuba musu lik'i. Neehal ma ta yi liƙi da kuɗin da Ameen ya sa wani abokinsa ya bata bandir ɗin 200. tana gurin bikin ne amma hankalinta gaba-d'aya yana gurin Sadik, sai kiran shi take amma ba ya picking. Mama ma ta zo gurin ita da tawagarta ta yi kyau sosai cikin wani haddadden lace kalar orange and black, Maman Hafsat ma ta zo. Neehal da taje yiwa Mama lik'i Maman tai ta kallonta cike da mamakin kayan da ta gani a jikinta, amma bata mata magana ba, kuma ko shakka ba ta yi tasan duk shirin Ameen ne wannan.
An cigaba da gudanar da shagalin biki yanda ya kamata, Amarya da Ango sun fito tsakiyar fili anata zuba musu lik'i. Neehal ma ta yi liƙi da kuɗin da Ameen ya sa wani abokinsa ya bata bandir ɗin 200. tana gurin bikin ne amma hankalinta gaba-d'aya yana gurin Sadik, sai kiran shi take amma ba ya picking. Mama ma ta zo gurin ita da tawagarta ta yi kyau sosai cikin wani haddadden lace kalar orange and black, Maman Hafsat ma ta zo. Neehal da taje yiwa Mama lik'i Maman tai ta kallonta cike da mamakin kayan da ta gani a jikinta, amma bata mata magana ba, kuma ko shakka ba ta yi tasan duk shirin Ameen ne wannan.