← Book details Neehal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 118

Sashe 33

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tare suka fito daga ɗakin, Neehal ta fice shi kuma ya zauna yana haɗe rai dan kar su cigaba da tsokanarsa, aikwa kamar ma ya ce su yi suka fara, daga baya kuma suka koma zancen Neehal kowa yana faɗin yana kamu. Shi dai ko kanzil bai ce musu ba. Neehal tana koma Haneefah ta miƙa mata su Afrah da suke ƙoƙarin saka kuka ganin shiru_shiru ba su gan ta ba, ta kama hannunsu suka shiga ɗakinta, ta adana turarukan. Bayan Magriba aka tafi ɗaukar Amarya, su Neehal kam ba a je da su ba, Mama ta ce sa je daga baya. Bayan isha'i mutane suka fara watsewa, gidan ya rage daga su Aunty Sadiya sai na nesa waɗanda za su tafi gobe da safe, Hameedah ma da Mamanta suna nan. Sai yau Mamansu Anwar ta zo ita da k'annenshi, ba ta jin dad'i ne shi yasa tunda aka fara bikin ba ta zo ba. Neehal dai tana kwance a ɗakin Mama tana ta matsar kwalla, Twins na manne a jikinta suna cin Cheese, tunda ta idar da Sallah ta haye gadon tay kwanciyarta. Hajiya ce ta shigo ɗakin tana ƴan mitocinta da ba ta rabo da su, kallon Neehal ta yi ta ce "Ke kuma lafiya kike kwance?" Neehal tay mata shiru, ta tab'e baki ta ce "Wai waɗannan Yaran ina uwarsu ne?" Daidai nan Mama ta shigo ɗakin, Hajiya ta ce "Yawwa, Ta Abuja (Da yake haka take ce mata idan fulatancin ya motso mata) yanzu nake tambayar wannan uwar langwan ta mun shiru, waɗannan Yaran waye ne haka, take ta wahala da su?" Kafin Mama ta ce wani abu Neehal ta juyo da sauri idanunta da guntun hawaye ta ce "Ƴaƴan ƙawata ne, ba ta da lafiya ba ta samu zuwa ba shine ta aiko aka kawo mun su." Mama ta kalle ta kawai, Hajiya ta ce "Ayyo, ga su kuwa kyawawa kamar Ƴaƴan Turai." Mama dake kallon Neehal ta ce "Kukan me kike?" Kafin ta yi magana Afrah ta yi karaf ta ce "Ba ta da lafiya." Da yake haka Neehal ɗin ta ce musu da suka dame ta da tambaya ganin tana kuka. Mama ta ce "Allah ya sauwaqe." Ta juya ta fice. Hajiya ta ce "Sannu gajiyar biki ce." Ciki_ciki Neehal ta ce "Yawwa." Hajiya ta fara yiwa su Afrah surutu da tambayoyi kamar wasu manya, su dai shiru kawai suka yi suna kallonta tare da ƙara lafewa a jikin Neehal, sai da ta gaji ta tashi ta fita.

Da daddare wajen 12 Mama suna zaune ita matar Yayan Daddy da Hajiya dake ta gyangyad'i, ance ta koma ɗaki ta ƙi. Neehal ce ta fito daga ɗakin Mama wadda bacci ya ɗauke ta bayan ta gama shan kukanta, yanzu ma Amrah ce ta tashe ta, idanunta kuwa har sun kumbura. Mama ta bita da kallo kafin ta ce "Wai lafiyarki kuwa Neehal, me aka miki kike kuka?" Ta yi shiru ba ta ce komai ba, Mama ta ce "Ba na son halin kin nan fa, ana miki magana kina ji ki yi shiru." Neehal ta ce "Ba komai kawai dai.." sai kuma ta yi shiru, Mama ta ce "Kawai dai me?" Neehal ta ce "I started missing Yaya." Mama ta tab'e baki ta ce "Shine kuma zaki zauna kina kuka, kamar wanda ya mutu, ko ce miki aka yi ya tafi kenan?" Neehal ta ce "To ai ba zai dinga zuwa kodayaushe ba." Mama ta ce "So you can follow him ai, tunda tare aka haife ku." Matar Yayan Dad wadda ake kira da Umma ta ce "Ai da gaskiyarta dole ta yi kewar ɗan'uwanta." Hajiya data wartsake tun fitowar Neehal ta ja tsaki ta ce "Wai dama akan Aminu kike asarar hawayenki saboda baki san ciwon kanki ba, Ameen ɗin da ba wani k'aunarki yake ba, ai daɗi ma ya kamata ki ji yanzu zaki wataya babu mai ƙara takura miki a gidan nan, kafin kema Allah ya kawo miki miji ki tafi." Neehal ta turo baki gaba ta nufi kitchen dan haɗawa Amrah tea.

Washegari tun safe sauran baƙi suka tafi, su Aunty Sadiya ma suna gama gyaran gidan kafin Azhar suka wuce nasu gidajen, Hajiya ma ta bi Ammin Amirah sun wuce Gombe. Gida ya rage daga Mama da Neehal sai su Dije masu aiki da Twins, sai Hameedah da Mom ɗinta da Umma wanda suma da Yamma za su wuce Abuja. Driver Mama ta aika ya kaiwa su Ameen breakfast, da rana ma haka. Neehal kam wuni ta yi a ɗaki ita da Twins ɗinta. Sai can yamma Haneefah ta zo gidan. Da daddare bayan kowa ya tafi Mama ta je part ɗin Dad su yi magana akan su Afrah, Mama tana duban shi ta ce. "Daddy yanzu sai mu san abun yi akan yaran nan, dan yanzu na san duk inda hankalin iyayensu yake a tashe yake ba kaɗan ba." Daddy ya ce "Hakane, tunda gobe Monday idan Neehal zata aiki sai mu tafi tare mu bada a yi cikiyar iyayensu, na san Insha Allahu za'a samu iyayen nasu ko a'ina suke a  ƙasar nan, tunda babu inda ba'a kallon ASTV, daga nan sai mu biya wasu gidan Radios ɗin duk mu bada cikiya. Mama ta ce "Allah ya kai mu goben lafiya. Dad ya ce "Ameen, kira mun Neehal ɗin ma tunda aka fara biki haɗuwar mu ta yi wuya." Mama ta ce "Kuma a part ɗin nan take kwana, dan dai ana sha'anin biki ne." Mama ta kira Neehal a waya ta ce ta zo part ɗin Daddy. Ba jimawa ta ƙaraso tare da Twins. Mama ta ce mata "Kai Neehal kina cika wa yaran nan kayan zaƙi, duk sanda zan gansu da sweet ko chocolate a hannunsa." Neehal ta yi Murmushi tare da zama a kusa da Daddy. Ta gaida Daddy suma su Afrah suka gaishe shi, ya amsa musu cike da fara'a. Sun ɗan taɓa hira da Daddy har su Afrah suka fara bacci. Mama ta dubi Neehal ta ce "Gobe za mu je mu yi report akan yaran nan, daga nan mu biya mu ba da cikiyar iyayensu." Gaban Neehal ya faɗi, dan bata k'aunar abun da zai rabata da yaran ko na second ɗaya, ta yi shiru ba ta ce komai ba. Mama data kula da yanayinta na canzawar da fuskarta ta yi ta ce "Sai ki shirya da wuri, dan ke zaki yi bayanin yanda kika tsince su." Neehal da idanunta suka ciko da k'walla ta ce "Mama gobe ya yi wuri a bari a ƙara wasu kwanaki sai a...." Kallon da Mama ta watsa mata yasa ta had'iye maganarta. Mama ta ce "Kina cikin hankalinki kuwa? Yanzu kin san irin tashin hankalin da iyayensu suke ciki na rashinsu har na kwana biyu ba su san inda suke ba." Neehal ta ce "To ni Mama ban san rabuwa da su." Mama ta ce "Uhm, ke da kika same su sama ta ka kenan, kuma dududu kwana biyu kawai kuka yi tare, amma ba kyasan rabuwa da su, balle kuma mahaifiyarsu da ta haife su ta raine su na shekaru." Neehal ta ce "Ai ba su da Uwa, ta rasu." Mama ta ce "Who told you?" Neehal ta ce "Su ne, suka ce mun Daddy'nsu yace their Mom ta tafi ba za ta dawo ba for ever." Mama ta ce "Allah ya ji k'anta, amma ai suna da Uba da dangi ko?" Neehal ta yi shiru ba ce komai ba sai hawaye take. Daddy dake kallon su Ya ce "Daughter me yasa bakya son su tafi?" Neehal ta ce "Dad I love them and kuma bana son na rabu da su, na ji ina son su sosai, kuma ga su marayu ina tausayin Maraya sosai because....." Mama ta katse ta da faɗin "Shut up, Stupid, komai za ki ce yara dai sai an maida su gurin iyayensu, duk yanda kike son su ba ki kai iyayensu ba." Tana gama faɗar haka ta mik'e ta shige bedroom ɗin Daddy. Dad ya rarrashi Neehal ta bar kukan da take sannan ya rakata part ɗin Mama da Afrah a hannunsa, ita kuma ta ɗau Amrah. Ko wanka ba ta yi ba ta kwanta rungume da yaran gam a jikinta kamar wanda za'a k'wace mata su..........✍️
[7/21, 9:01 AM] Zee data: *âš¡ NEEHAL âš¡*

_By_
_Zeey Kumurya_

*2️⃣2️⃣*

A ɓangaren Ango da Amarya kuwa komai ya tafi yadda ya kamata a daren da aka kaita, sai dai Ameen ya sha rawar kai a gurin Hafsat, daga baya kuma ta koma raki da shagwab'a. Sai dai abu na farko da Ameen ya fuskanta dangane da Hafsat tana da ƙarancin ilimin Addini da shi kanshi addinin ma, dan Sallah ma da asuba har ya je masallaci ya dawo ba ta yi ba tana kwance, da ƙyar ya tashe ta ta yi, duk ya san bata jin dad'i amma ai ba cutar da zata hanata Sallah take ba. Haka ɓangaren gyaran gida ma babu abun da ta taɓa da sunan gyara, duk da jikin nata ya warware, sai da ƴan'uwanta suka zo da yamma ne ma suka gyara mata gidan. Da daddare Mama ta aiko musu da dinner, bayan sun gama ci ta tashi ta bar kayan a wurin, Ameen ya bita da kallo cikin mamaki zuciyarsa cike da takaicinta, amma ya danne bai nuna ba ya kwashe kayan ya kai kitchen, wurin da suka ci abincin kuwa ko arzik'in tattarewa bai samu ba haka ya kwana.
Chapter 33 · 0% Book details